{"id":8428,"date":"2026-11-18T06:31:01","date_gmt":"2026-11-18T06:31:01","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=8428"},"modified":"2026-11-18T06:31:01","modified_gmt":"2026-11-18T06:31:01","slug":"shugaban-najeriya-ya-nemi-sake-tsayawa-takara-domin-%c6%99arfafa-nasarorin-da-ya-samu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/18\/shugaban-najeriya-ya-nemi-sake-tsayawa-takara-domin-%c6%99arfafa-nasarorin-da-ya-samu\/","title":{"rendered":"Shugaban Najeriya Ya Nemi Sake Tsayawa Takara Domin \u0199arfafa Nasarorin Da Ya Samu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi goyon bayan &#8216;yan Najeriya domin sake zabensa a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Janairun 2027. Ya yi alkawarin karfafa nasarorin da gwamnatinsa ta samu tare da kammala ayyukan raya kasa da ke gudana a fadin kasar idan aka sake zabensa a karo na biyu.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban ya yi wannan kira ne a ranar Talata da ta gabata yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) a Birnin Kebbi jihar Kebbi. A wurin ya sake jaddada kudirinsa na karfafa zaman lafiya tsaro da ayyukan raya ababen more rayuwa musamman a yankin Arewa maso Yamma.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bai wa al&#8217;ummar jihar Kebbi tabbacin cewa zai ci gaba da yin aiki kafada-da-kafada da Gwamna Nasir Idris domin magance matsalolin ababen more rayuwa a jihar ciki har da biyan bukatun gina da gyaran hanyoyi da sauran ayyukan ci gaba.<\/p>\n<p>Yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam&#8217;iyyar a taron Shugaban ya bayyana cewa ziyararsa ta kuma ba shi damar nuna godiya ga mutanen jihar Kebbi bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin babban zaben 2023 wanda ya taimaka wajen samun nasarar jam&#8217;iyyar APC a zaben.<\/p>\n<p>Ya bayyana goyon bayan nasu a matsayin nuna amincewa da shugabancinsa inda ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da ke da nufin inganta walwala da yanayin rayuwar &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p>&#8220;Ban zo nan don yin dogon jawabi ba sai dai don in gode muku kan zaben da ya gabata. Kun zabe ni. Kun zabi Kauran Gwandu. Kun zabi sanatocinmu Adamu Aliero da Yahaya da sauran su.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Yanzu kuma na dawo ne don in ce muku na gode. Allah ya albarkace ku kuma ya amsa addu&#8217;o&#8217;inku. Kun sha rana tsawon yini. Abin da nake so in ce kawai shi ne na gode kwarai da gaske&#8221;<\/strong> <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>Shugaban ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ya kuduri aniyar cika abubuwan da suke tsammani daga gare shi tare da yin alkawarin ci gaba da daukar matakan karfafa tsaro raya ababen more rayuwa da kuma inganta samun damar samun ingantaccen ilimi da ayyukan kiwon lafiya.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Daga kasan zuciyata ina ba ku tabbacin jajircewata ga jihar ga yankin Arewa maso Yamma da kuma jam&#8217;iyyarmu.<\/strong><strong>&#8220;\u201cIn ba ku tabbacin cewa muna goyon bayan zaman lafiya kwanciyar hankali da ci gaban wannan \u0199asa. Mun ha\u0257a kai kuma muna da murya \u0257aya. Muna son ci gaba. Muna son bunkasa. Muna son ilimi. Muna son cibiyoyin kiwon lafiya wa\u0257anda za su zama abin alfahari ga al\u2019ummarmu kuma su kula da dukkanmu,\u201d<\/strong> <\/em>in ji Shugaba Tinubu.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya jaddada cewa manufofin ci gaban Najeriya sun dogara ne kan zaman lafiya mai dorewa girmama juna da kuma hadin kan kasa.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga shugabannin siyasa da magoya bayansu da su gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana yana mai nuni da cewa bambancin ra&#8217;ayin siyasa bai kamata ya zama barazana ga hadin kan kasa ba.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Na sake dawowa domin rokon ku da ku kiyaye zaman lafiya abota da kuma hadin kai,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya danganta nasarar da ya samu a zaben 2023 ga nufin Allah sannan ya sake yin kira ga jama&#8217;a da su ba shi goyon baya domin kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara yana mai jaddada cewa Allah ne ke ba da shugabanci kuma shugabanci ya kunshi nauyin yi wa al&#8217;umma hidima.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Allah ne kadai ke ba da iko ga wanda ya so. Na nemi hakan kuma Ya ba ni wannan girmamawa wannan dama da kuma wannan gata a karon farko.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;A wannan karon na zo a gaban ku ne domin neman goyon bayan ku na wa&#8217;adi na biyu domin in kammala abin da na fara&#8221;<\/strong><\/em> in ji Shugaban.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bai wa jihar Kebbi tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba da tallafi ga muhimman ayyukan ci gaba ciki har da shirin kafa tashar jiragen ruwa ta cikin kasa (inland port) hanyar Birnin Kebbi\u2013Argungu\u2013Kaniyaka da kuma sake gina sassan hanyar Kalgo\u2013Bunza\u2013Kamba da ambaliyar ruwa ta lalata. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da Gwamna Nasir Idris domin inganta harkokin sufuri ayyukan tattalin arziki da kuma yanayin rayuwar al&#8217;umma.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Dukkan bukatun da Gwamna ya gabatar suna a gabana a nan. Na saurara sosai. Muna aiki tare&#8221;<\/strong> <\/em>in ji shi yana mai bai wa taron tabbaci.<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma yi kira ga matasa masu kada kuri&#8217;a da su shiga harkokin zabe mai zuwa sosai su kuma mallaki katunan zaben su (PVC) yana mai tambayar ko a shirye suke su yi amfani da hakkinsu na zabe.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Matasan Kebbi mai girma Kebbi mai ci gaba shin kuna shirye don kada kuri&#8217;a? Kuna da katin zaben ku (PVC) Ku daga hannu idan kuna da katin zaben ku. Shin za ku fito ku kada kuri&#8217;a?&#8221;<\/strong><\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya gode wa magoya bayan bisa karbuwar da suka nuna ya yi addu&#8217;ar neman albarkar Allah sannan ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su fito da yawa domin kada kuri&#8217;a a zaben mai zuwa<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi goyon bayan &#8216;yan Najeriya domin sake zabensa a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Janairun 2027. Ya yi alkawarin karfafa nasarorin da gwamnatinsa ta samu tare da kammala ayyukan raya kasa da ke gudana a fadin kasar idan aka sake zabensa a karo &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":8431,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-8428","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8428","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8428"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8428\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8432,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8428\/revisions\/8432"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8431"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8428"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8428"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8428"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}