{"id":8002,"date":"2026-11-13T11:45:09","date_gmt":"2026-11-13T11:45:09","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=8002"},"modified":"2026-11-13T11:58:15","modified_gmt":"2026-11-13T11:58:15","slug":"hukumar-za%c9%93en-gambia-ta-tabbatar-da-yan-takara-biyar-domin-za%c9%93en-shugaban-%c6%99asa-na-disamba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/13\/hukumar-za%c9%93en-gambia-ta-tabbatar-da-yan-takara-biyar-domin-za%c9%93en-shugaban-%c6%99asa-na-disamba\/","title":{"rendered":"Hukumar Za\u0253en Gambia Ta Tabbatar Da &#8216;Yan Takara Biyar Domin Za\u0253en Shugaban \u0198asa Na Disamba"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Gambia ta tabbatar da \u2018yan takara biyar don zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 5 ga watan Disamba, ciki har da shugaba mai ci Adama Barrow wanda ke neman wa\u2019adi na uku a kan karagar mulki.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hukumar ta sanar da sunayen \u2018yan takarar a ranar Alhamis bayan tantance takardun tsayawa takara da masu neman mukamin suka gabatar gabanin zaben.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sauran \u2018yan takarar da aka amince da su sun hada da babban jagoran \u2018yan adawa na kasar Ousainou Darboe daga jam\u2019iyyar United Democratic Party da kuma shahararren dan siyasa matashi Talib Ahmed Bensouda daga jam\u2019iyyar UNITE Party.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Tawagar ECOWAS Za Ta Tantance Shirye-shiryen Zaben Gambia<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jerin sunayen ya kuma kunshi Isatou Touray mace ta farko a kasar da ta tsaya takarar shugaban kasa da kuma Modou Lamin Sima daga jam\u2019iyyar Alliance of Progressive Citizens.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Barrow, wanda ke jagorantar jam\u2019iyyar National People\u2019s Party ya hau karagar mulki a shekarar 2016 bayan ya kayar da tsohon shugaba Yahya Jammeh wanda hakan ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 22.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Duk da cewa da farko Barrow ya nuna cewa ba zai nemi wa\u2019adi na uku ba kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1997 bai sanya iyakar wa\u2019adin mulki ga shugaban kasa ba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kokarin sanya iyakar wa\u2019adin mulki ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki ya ci tura sau biyu bayan da \u2018yan majalisa suka yi watsi da sabbin kundin tsarin mulkin da aka gabatar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Darboe tsohon mataimakin shugaban kasa kuma gogaggen dan siyasar adawa yana kokarin zama shugaban kasa a karo na biyar bayan ya zo na biyu a zabukan da suka gabata.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A daya bangaren kuma, Bensouda tsohon magajin garin Kanifing ya samu goyon baya sosai daga matasa a \u2018yan watannin nan.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa ya fuskanci rashin tabbas bayan wani rahoton gwamnati ya zarge shi da rashin gaskiya wajen tafiyar da harkokin kudi a lokacin da yake rike da mukamin magajin gari. Sai dai hukumar zabe ta amince da takararsa a yanzu.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Zaben na ranar 5 ga watan Disamba zai kasance zaben shugaban kasa na uku tun bayan da kasar ta koma tsarin dimokuradiyya a shekarar 2016.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ana sa ran ayyukan yakin neman zabe za su fara a ranar Litinin mai zuwa kuma za su ci gaba na tsawon makonni biyu gabanin ranar zaben.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Gambia ta tabbatar da \u2018yan takara biyar don zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 5 ga watan Disamba, ciki har da shugaba mai ci Adama Barrow wanda ke neman wa\u2019adi na uku a kan karagar mulki. Hukumar ta sanar da sunayen \u2018yan takarar a ranar Alhamis &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":8005,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-8002","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8002","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8002"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8002\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8004,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8002\/revisions\/8004"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8005"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8002"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8002"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8002"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}