{"id":7985,"date":"2026-11-13T10:23:55","date_gmt":"2026-11-13T10:23:55","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7985"},"modified":"2026-11-13T10:23:55","modified_gmt":"2026-11-13T10:23:55","slug":"taron-apc-a-edo-mataimakin-shugaban-kasa-shettima-ya-gabatar-da-nasarorin-shugaba-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/13\/taron-apc-a-edo-mataimakin-shugaban-kasa-shettima-ya-gabatar-da-nasarorin-shugaba-tinubu\/","title":{"rendered":"Taron APC A Edo: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gabatar Da Nasarorin Shugaba Tinubu"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su auna shugabanci ta hanyar tasirin da za a iya aunawa yana mai jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu yana bukatar wa&#8217;adi na biyu domin ya cika dukkan manufofin gwamnatinsa na tattalin arziki da ababen more rayuwa.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Saboda haka ya bukaci su yi nazari kan gwamnatin Tinubu bisa tasirin da take da shi ga rayuwar &#8216;yan kasa da kuma ci gaba da gyare-gyaren ababen more rayuwa da tattalin arziki da ke bukatar karin lokaci don kammalawa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Mataimakin Shugaban Kasa wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake wakiltar Shugaba Tinubu a taron yakin neman zaben Shugaban Kasa na All Progressives Congress (APC) a birnin Benin Jihar Edo ya lura cewa duk da cewa an kammala wasu ayyuka wasu har yanzu suna ci gaba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce: &#8220;<em>Muna rokon a yi la&#8217;akari da shugabancinmu ta hanyar rayuwar da shawarwarinmu suka shafa da kuma aikin da muka kuduri aniyar kammalawa. Mun kai wannan matsayi da amincewarku kuma muna neman izininku na kammala aikin da muka fara<\/em>.&#8221;<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake bayyana cewa wasu alkawurra har yanzu suna nan a gaban gwamnatin Tinubu Mataimakin Shugaban Kasa ya ce Gwamna Monday Okpebholo ya sa APC ta yi alfahari kuma Shugaba Tinubu ya tsaya tare da shi yana goyon bayan kokarinsa na biyan bukatun mutanen Edo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya sake jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na cike gibin da ke tsakanin kayayyakin more rayuwa da Najeriya inda ya nuna muhimmancin rawar da jihar Edo ke takawa a fannin tattalin arziki da kuma alkawarin &#8216;yantar da &#8216;yan kasuwa na gida daga asarar kudi da ke faruwa sakamakon mummunan yanayin hanya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Ha\u0257a Ci gaban Kudaden Shiga na Ondo Da Gyaran Tattalin Arziki<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake tabbatar da cewa ci gaban kasa ba zai iya faruwa ba tare da la&#8217;akari da gaskiyar yankin ba Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya ce &#8220;<em>Lokacin da muka zo gare ku shekaru hudu da suka gabata mun tabbatar muku cewa ba za mu iya cike gibin kayayyakin more rayuwa na kasarmu ba tare da mun dauki jihar Edo tare ba.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Ba mu yi watsi da wannan al\u0199awarin ba. Mun \u0199uduri aniyar gina hanyoyi wa\u0257anda \u0257an kasuwa a Agbede ba zai \u0199ara rasa ku\u0257i ba saboda jinkiri. Shi ya sa muka fara aiki don ha\u0253aka hanyar ta Ekpoma Auchi da Okpella.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Wannan shine dalilin da ya sa ake yin gyare-gyare na gaggawa a kan hanyoyin daga Benin zuwa Asaba da Sapele. Kuna da cikakken &#8216;yancin ri\u0199e mu a kan alkawarinmu har sai kun iya tafiya wa\u0257annan hanyoyin cikin kwanciyar hankali.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-full wp-image-7988\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1304.jpeg\" alt=\"\" width=\"1024\" height=\"682\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1304.jpeg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1304-300x200.jpeg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1304-768x512.jpeg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Mataimakin Shugaban \u0198asa ya jawo hankali ga wani babban ci gaba ga \u0253angaren masana&#8217;antu na Jihar Edo yana tabbatar da cewa iskar gas yanzu tana gudana ta cikin bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3) da aka kammala.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana cewa an amsa kiraye-kirayen da aka da\u0257e ana yi na farfa\u0257o da cibiyoyin masana&#8217;antu na gida tare da mafita ta makamashi ta dindindin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Mutanen Jihar Edo nagari mun ji kiranku na farfa\u0257o da masana&#8217;antu a jiharku. Mun kuma san cewa masana&#8217;antu ba za su bun\u0199asa ba tare da ingantaccen makamashi ba. A yau muna alfahari da cewa iskar gas yanzu tana ratsa bututun mai na Obiafu-Obrikom-Oben da aka kammala&#8221;<\/em> in ji mataimakin shugaban \u0199asa Shettima.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Dangane da harkokin kiwon lafiya ya nuna cewa tsoma bakin gwamnatin Najeriya yana bayyana a cikin &#8220;<em>Tallafinta ga cibiyoyi kamar Asibitin Koyarwa na Jami&#8217;ar Benin wanda yanzu ke ba da maganin radiotherapy ga masu fama da cutar kansa da kuma tallafin dialysis ga marasa lafiya da suka cancanta.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Mun kuma ba da fifiko ga ingantawa a Asibitin Koyarwa na Musamman na Irrua da Cibiyar Kula da Cututtukan Haihuwa ta \u0198asa. Wannan \u0199ari ne ga tallafinmu ga cibiyoyin kiwon lafiya na jama&#8217;a 158 a fa\u0257in Edo ta hanyar Asusun Kula da Lafiya na Asali&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Mataimakin shugaban \u0199asa ya sake tabbatar da jajircewar gwamnatin Najeriya ga daidaiton ilimi yana mai bayyana cewa Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Najeriya (NELFUND) yana karya shingen ku\u0257i don \u0257aliban Jihar Edo da kuma fa\u0257in \u0199asar su iya ci gaba da burinsu na ilimi ba tare da katsewa ba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Dangane da aikin gona ya ce &#8220;<em>Mun ware takin zamani ga manomanku. Muna horar da manoma da &#8216;yan kasuwa kuma muna shigar da &#8216;ya&#8217;yanku maza da mata a shirye-shiryen sana&#8217;a ta hanyar Hukumar Aiki ta \u0198asa.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Yayin da yake nuni da cewa ci gaban da aka samu na daga cikin dalilan da suka sa Shugaban Kasa ya sake komawa wurin masu zabe cike da kwarin gwiwa Mataimakin Shugaban Kasa ya jaddada kudurin gwamnatin Najeriya na kwato kayan tarihi na Najeriya da aka sace a baya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana cewa gwamnatin tana tsaye kafada da kafada da al&#8217;umma da masarautun gargajiya wajen neman a dawo da tsoffin kayan tarihi na Benin (Benin Bronzes) da sauran kayan al&#8217;adu zuwa gida ba tare da wani sharadi ba.<\/span><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-full wp-image-7993\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1305-2.jpeg\" alt=\"\" width=\"1024\" height=\"682\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1305-2.jpeg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1305-2-300x200.jpeg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1305-2-768x512.jpeg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/p>\n<p>Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa ayyukan da gwamnatin tarayya ta kawo jihar sun fara haifar da canji mai ma&#8217;ana.<\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya yi alkawarin cewa al&#8217;ummar jihar Edo za su ba Shugaba Bola Tinubu kuri&#8217;u miliyan 2 domin sake zabensa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 mai zuwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tsohon Gwamnan jihar Edo Sanata Adams Oshiomhole ya shaida wa taron cewa ayyukan da jam&#8217;iyyar APC ta yi a matakin jiha da na tarayya sun ba shi kwarin gwiwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Da ba don ayyukan kirki da gwamnatin APC ta yi a matakin jiha da na tarayya ba da ban ji alfahari da jagorantar wannan yakin neman zabe a jihar Edo ba&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Haka kuma Gwamnan jihar Imo kuma Sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam&#8217;iyyar APC Hope Uzodinma ya bayyana yawan jama&#8217;ar da suka halarci taron a matsayin &#8220;<em>Shaida bayyananniya ta goyon baya.<\/em>&#8220;<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Yawan jama&#8217;ar da suka taru da kuma karamcin da aka nuna mana shaida ce ta kauna da goyon bayan da al&#8217;ummar jihar Edo ke nunawa Shugaba Bola Tinubu&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya yi kira ga &#8216;yan kasa da su je su karbi katunan zabensu na dindindin domin &#8220;<em>Babban alkawarin kuri&#8217;un da suka yi wa Shugaban Kasa ya zama gaskiya.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC Sanata Abdulaziz Yari ya shaida wa jama&#8217;a cewa kulawar da Shugaba Tinubu ke bai wa jihar Edo a bayyane take ta hanyar ayyukan da ake gudanarwa a jihar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Shugaba Bola Tinubu yana matukar kaunar jihar Edo shi ya sa wadannan ayyukan ci gaba suke zuwa jihar&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Yari ya yi kira ga &#8216;yan kasa da su &#8220;<em>Fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben Shugaba Bola Tinubu&#8221;<\/em> yana tunatar da su cewa tsarin jam&#8217;iyyar ya sanya &#8220;M<em>agance matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama&#8217;a a matsayin babban fifiko.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce yawan jama&#8217;ar da suka halarci taron ya yi magana da kansa. \u201c<em>Yawan jama\u2019ar da suka fito domin tarbar tawagar yakin neman zaben jam\u2019iyyar APC shaida ce da ke nuna cewa tuni mutane suka yanke shawarar zaben APC a dukkan mukaman da ake takarar su\u201d<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A matsayinsa na \u0257an yankin Kudu-Kudu (South-South) ya yi alkawarin bayar da gudummawarsa ta musamman inda ya ce zai \u201cT<em>abbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu bai fuskanci wani gagarumin kalubale daga abokin hamayya ba\u201d<\/em> a yankin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban jam\u2019iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya kammala jawabinsa da jaddada amincewar jam\u2019iyyar ga dan takararta. \u201c<em>Jam\u2019iyyar mu tana da dan takara mafi cancanta saboda haka ta cancanci a sake zabenta a zabe mai zuwa<\/em>\u201d in ji shi yayin da yake magana da al\u2019ummar jihar Edo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A wani bangaren kuma Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya ziyarci fadar Oba na Benin inda ya shaida wa basaraken cewa tawagar gwamnatin tarayya ta zo masarautar ne domin nuna matukar godiya kan irin jagorancin da yake bayarwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">\u201c<em>Mun zo nan ne domin mu nuna godiyarmu a gare ku Mai Martaba bisa irin gagarumin kokarin da kuke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma kare al\u2019adun gargajiya masu tarin yawa na kakanninku<\/em>\u201d in ji Mataimakin Shugaban Kasan.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake mayar da martani Oba na Benin Omo N\u2019Oba N\u2019Edo Uku Akpolokpol Oba Ewuare II ya nuna jin dadinsa game da kasancewar gwamnatin tarayya da kuma goyon bayan da take bai wa al\u2019ummar jihar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">\u201c<em>Masarautar Benin ta lura kuma tana matukar godiya kan irin shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi a jihar tamu\u201d<\/em> in ji Oba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Musamman ma ya yaba da manyan ayyukan raya ababen more rayuwa da ake gudanarwa a karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu inda ya bayyana su a matsayin ayyukan da suka \u201c<em>Shafi rayuwar al\u2019umma kai tsaye.\u201d<\/em><\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su auna shugabanci ta hanyar tasirin da za a iya aunawa yana mai jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu yana bukatar wa&#8217;adi na biyu domin ya cika dukkan manufofin gwamnatinsa na tattalin arziki da ababen more rayuwa. Saboda haka ya bukaci su yi nazari &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":7987,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-7985","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7985","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7985"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7985\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7994,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7985\/revisions\/7994"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7987"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7985"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7985"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7985"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}