{"id":7908,"date":"2026-11-12T11:03:38","date_gmt":"2026-11-12T11:03:38","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7908"},"modified":"2026-11-12T11:03:38","modified_gmt":"2026-11-12T11:03:38","slug":"shugaba-tinubu-ya-taya-dansa-murnar-samun-sarauta-ya-bukaci-ya-yi-wa-alumma-hidima","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/12\/shugaba-tinubu-ya-taya-dansa-murnar-samun-sarauta-ya-bukaci-ya-yi-wa-alumma-hidima\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Taya Dansa Murnar Samun Sarauta Ya Bukaci Ya Yi Wa Al\u2019umma Hidima"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Shugaba Bola Tinubu ya taya dansa Seyi Tinubu murnar nada shi sarautar &#8216;Dan Zaki Gwandu&#8217; a Jihar Kebbi inda ya bukace shi da ya gudanar da nauyin da ke tattare da sabon mukamin nasa na gargajiya cikin tawali&#8217;u jarumtaka da sadaukarwa wajen hidima.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban ya jaddada cewa wannan karramawa ta wuce batun samun daukaka ta kashin kai kawai ya bayyana ta a matsayin kira na dorewa kan dabi&#8217;un shugabanci inganta zaman lafiya da fahimtar juna da kuma bayar da gudummawa ga jin dadin al&#8217;umma.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon taya murna da aka fitar a ranar Laraba wanda kuma ya samu sanya hannun Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru Mista Bayo Onanuga biyo bayan nada dansa a wannan sarauta ta gargajiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamnan Kwara Murnar Samun Sarauta a Ilorin<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban ya nuna godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Gwandu da Majalisar Masarautar Gwandu bisa wannan karramawa wadda sarkin ya bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin masarautar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">&#8220;A matsayina na uba na ji dadin ganin an karrama dana ta hanyar wata cibiyar gargajiya mai tarihi mai cike da daukaka.<\/span><\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">&#8220;Sai dai kuma ina tunatar da shi cewa duk wata karramawa tana zuwa ne tare da nauyi. Sarautar &#8216;Dan Zaki Gwandu&#8217; tana kunshe da dabi&#8217;un jarumtaka shugabanci da kuma hidima.<\/span><span class=\"s1\">&#8221; Ina kira gare shi da ya yi rayuwa bisa ga wadannan dabi&#8217;u ya kasance mai tawali&#8217;u kuma ya ci gaba da sadaukar da kansa domin amfanin sauran mutane&#8221;<\/span><\/em><span class=\"s1\"> in ji Shugaban kasa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da dansa ya bayar wajen shigar da matasa harkoki ci gaban al&#8217;umma da karfafa su musamman ta hanyar rawar da ya taka a kungiyar &#8216;City Boy Movement&#8217; da sauran shirye-shiryen da ke tallafawa matasan Najeriya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bukaci Seyi Tinubu da ya dauki wannan lakabi a matsayin kira na kara kaimi wajen bunkasa matasa inganta zaman lafiya da kuma hidimtawa kasar Najeriya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban ya kara da cewa wannan karramawa tana nuna karfin dangantakar abota girmama juna da hadin kai da ke tsakanin al&#8217;ummomin Najeriya daban-daban.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya sake jaddada muhimmancin masarautun gargajiya a matsayin masu kula da tarihi al&#8217;adu da hadin kan kasa tare da mika godiya ga Sarkin Gwandu da al&#8217;ummar jihar Kebbi bisa karrama dansa da suka yi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaba Tinubu ya yi wa Seyi Tinubu fatan samun hikima tawali&#8217;u da karfin gwiwa yayin da yake karbar nauyin da ke tattare da sabon lakabin sarautar gargajiyar da aka ba shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne ya nada Seyi Tinubu a matsayin &#8216;Dan Zaki Gwandu&#8217; wato &#8216;Dan Zakin Gwandu&#8217;<span class=\"Apple-converted-space\">\u00a0 <\/span>a fadar tarihi ta Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya taya dansa Seyi Tinubu murnar nada shi sarautar &#8216;Dan Zaki Gwandu&#8217; a Jihar Kebbi inda ya bukace shi da ya gudanar da nauyin da ke tattare da sabon mukamin nasa na gargajiya cikin tawali&#8217;u jarumtaka da sadaukarwa wajen hidima. Shugaban ya jaddada cewa wannan karramawa ta wuce batun samun daukaka ta &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":7910,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39,48],"tags":[],"class_list":["post-7908","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","category-entertainment"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7908","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7908"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7908\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7912,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7908\/revisions\/7912"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7910"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7908"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7908"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7908"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}