{"id":7671,"date":"2026-11-08T13:10:36","date_gmt":"2026-11-08T13:10:36","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7671"},"modified":"2026-11-08T13:10:36","modified_gmt":"2026-11-08T13:10:36","slug":"shugaba-tinubu-ya-taya-tawagar-flamingos-murnar-samun-nasara-ta-tarihi-a-gasar-cin-kofin-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/08\/shugaba-tinubu-ya-taya-tawagar-flamingos-murnar-samun-nasara-ta-tarihi-a-gasar-cin-kofin-duniya\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Taya Tawagar Flamingos Murnar Samun Nasara Ta Tarihi A Gasar Cin Kofin Duniya"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar &#8216;Flamingos&#8217; ta Najeriya murnar nasarar tarihi da suka samu ta hanyar doke Japan da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na mata &#8216;yan kasa da shekaru 17 (FIFA U-17 Women\u2019s World Cup) a Rabat kasar Morocco. Wannan nasara ta sanya Najeriya zama kasa ta farko a Afirka da ta taba lashe wannan gasa.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana wannan nasara ta farko a matsayin abin alfahari ga kasa baki daya tare da cewa babban ci gaba ne ga kwallon kafa na mata a nahiyar Afirka.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya samu labarin nasarar ne yayin da ya dawo daga ziyarar yakin neman zabe a jihohin Akwa Ibom da Ribas.<\/p>\n<p>A cikin sakon taya murna da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya ce: <em>&#8220;Wani irin labari mai dadi ke nan da na dawo na tarar &#8216;Yan matanmu sun yi nasara a duniya kuma sun bai wa &#8216;yan Najeriya a ko&#8217;ina dalilin sake yin murna da kasarmu mai girma.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Ga tawagar &#8216;Flamingos&#8217; tamu jarumai ina taya ku murna. Kun nuna jarumtaka ladabi kudurin cimma manufa da kuma ruhin &#8216;yan Najeriya na rashin karaya ko kadan.<\/em><\/p>\n<p>KARANTA KUMA: &#8216;Flamingos&#8217; Sun Doke Japan Sun Lashe Kofin Duniya Na Mata &#8216;Yan Kasa Da Shekaru 17<\/p>\n<p>&#8220;<em>Na bi diddigin tafiyarku a duk tsawon wannan gasa kuma bayan nasarar da kuka samu a wasan kusa da na karshe kun yi alkawarin dawo wa gida da kofin. A yau kun cika wannan alkawari. Kun amince da kanku kun yi fafutuka domin juna kuma kun daga tutar kasarmu zuwa matsayi mafi girma a duniya.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Nasararku ta zama abin koyi ga miliyoyin &#8216;yan matan Najeriya da ke mafarkin cimma manyan nasarori. Kun nuna musu cewa ta hanyar aiki tukuru samun dama da kuma kudurin cimma manufa su ma za su iya kaiwa matsayi mafi girma na nasara.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;A yau Najeriya na taya ku murna. Kun rubuta sunayenku da zinare, kuma kasarku tana alfahari da ku kwarai da gaske.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya yaba musamman ga Awawu Bashiru da Oluebube Umejiaku wadanda kwallayen da suka zira suka tabbatar da wannan nasara ta tarihi sannan ya yaba wa daukacin tawagar bisa hadin kan da suka nuna a duk tsawon gasar.<\/p>\n<p>Ya kuma taya tawagar masu horarwa Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) da Hukumar Wasanni ta Kasa murnar gudummawar da suka bayar wajen samun nasarar kungiyar.<\/p>\n<p><em>Shugaban ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na zuba jari wajen bunkasa wasanni a matakin tushe da kuma fadada damammaki ga matasan Najeriya musamman &#8216;yan mata domin gano basirarsu bunkasa ta da kuma cimma cikakken karfin da Allah ya ba su. \u201cIn taya ku murna Flamingos. Na gode da kuka sanya Najeriya ta yi alfahari\u201d in ji Shugaban.<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar &#8216;Flamingos&#8217; ta Najeriya murnar nasarar tarihi da suka samu ta hanyar doke Japan da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na mata &#8216;yan kasa da shekaru 17 (FIFA U-17 Women\u2019s World Cup) a Rabat kasar Morocco. Wannan nasara ta sanya Najeriya zama kasa ta &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":7674,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[41],"tags":[],"class_list":["post-7671","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-sports-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7671","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7671"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7671\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7675,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7671\/revisions\/7675"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7674"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7671"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7671"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7671"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}