{"id":7582,"date":"2026-11-07T15:35:39","date_gmt":"2026-11-07T15:35:39","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7582"},"modified":"2026-11-07T15:35:39","modified_gmt":"2026-11-07T15:35:39","slug":"2027-gwamnan-jihar-ribas-ya-yi-al%c6%99awarin-bayar-da-%c6%99uriu-miliyan-uku-ga-shugaba-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/07\/2027-gwamnan-jihar-ribas-ya-yi-al%c6%99awarin-bayar-da-%c6%99uriu-miliyan-uku-ga-shugaba-tinubu\/","title":{"rendered":"2027: Gwamnan Jihar Ribas Ya Yi Al\u0199awarin Bayar Da \u0198uri&#8217;u Miliyan Uku Ga Shugaba Tinubu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara ya yi alkawarin samar da akalla kuri&#8217;u miliyan uku ga Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Janairun 2027 inda ya ba shi tabbacin cewa jihar za ta ba shi cikakken goyon baya.<\/strong><\/p>\n<p>Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne yayin taron yakin neman zaben Shugaba Tinubu a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakol inda ya ce Jihar Ribas za ta mayar da martani ta hanyar goyon bayan Shugaban kasar kamar yadda shi ma ya nuna wa jihar goyon baya.<\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana matakin da Shugaba Tinubu ya dauka a lokacin rikicin siyasa a Jihar Ribas a matsayin nuna jagoranci irin na uba yana mai cewa Shugaban kasar ya tsaya tare da gwamnatinsa a daidai lokacin da jihar ta tsinci kanta a wani mawuyacin hali na tsaka mai wuya.<\/p>\n<p><em>&#8220;A lokacin da Jihar Ribas ta kasance a tsaka mai wuya ka shigo ciki a matsayin uba kuma a matsayin kwararren shugaba mai hangen nesa a tsakiyar rudanin siyasa mai tsanani. Ba ka yi biris ba&#8221; cewar Gwamna Fubara.<\/em><\/p>\n<p>DUBA KUMA: Wike Da Fubara Sun Ha\u0257a Kai Don Goyon Bayan Shugaba Tinubu A Zaben 2027<\/p>\n<p>Ya nuna godiyarsa kan goyon bayan da Shugaba Tinubu ya bayar musamman rawar da ya taka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tare da ayyukan more rayuwa da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa ciki har da aikin gina babbar hanyar mota ta bakin teku da ta tashi daga Legas zuwa Kalaba.<\/p>\n<p>Gwamna Fubara ya kuma bayyana cewa Shugaban kasar ya nada &#8216;yan asalin Jihar Ribas sama da 40 a mukamai daban-daban a cikin gwamnatinsa.<\/p>\n<p><em>&#8220;Kamar yadda ka tsaya tare da mu mu ma za mu tsaya tare da kai. Kamar yadda ka goyi bayan Jihar Ribas Jihar Ribas za ta goyi bayan ka&#8221; in ji shi.<\/em><\/p>\n<p>Ya kuma bai wa Shugaba Tinubu tabbacin cewa tsarin yakin neman zaben jam&#8217;iyyar APC a jihar zai tattara masu kada kuri&#8217;a domin samar masa da kuri&#8217;u da ba za su gaza miliyan uku ba.<\/p>\n<p>Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike shi ma ya bai wa Shugaba Tinubu tabbacin goyon bayan jihar Ribas inda ya bayyana cewa al&#8217;ummar jihar sun riga sun amince su zabi Shugaban a zaben watan Janairun 2027.<\/p>\n<p>Yayin da yake jawabi a wurin taron yakin neman zaben Wike ya ce yawan jama&#8217;ar da suka halarci taron a filin wasa na Adokiye Amiesimaka ya nuna cewa jihar a shirye take ta goyi bayan Tinubu.<\/p>\n<p><em>&#8220;Jihar Ribas ta riga ta yanke shawara ta riga ta amince domin a ranar 16 ga watan Janairu za su zabe ka&#8221; in ji Wike yayin da yake magana da Shugaban.<\/em><\/p>\n<p>Ya kuma yi nuni da yadda Gwamnatin Tarayya ta nada &#8216;yan asalin jihar Ribas a mukamai daban-daban inda ya yi ikirarin cewa jihar ta samu mukaman siyasa sama da 47 tun bayan fara aikin gwamnatin mai ci.<\/p>\n<p>Wike ya kalubalanci &#8216;yan adawa da su bayyana irin ayyukan da suka yi a jihar a baya yana mai jaddada cewa yakin neman zaben jam&#8217;iyyar APC ba zai bari sukar siyasa ta dauke masa hankali daga manufarsa ba.<\/p>\n<p>Tsohon Gwamnan Jihar Delta Sanata Ifeanyi Okowa shi ma ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Tinubu yana mai cewa Shugaban yana shimfida harsashin gina tattalin arziki mai karfi da kuma samar da kyakkyawar makoma.<\/p>\n<p>Sanata Okowa wanda ya bayyana cewa ya goyi bayan wani takarar shugaban kasa daban a shekarar 2023 kafin ya koma jam&#8217;iyyar APC ya siffanta manufofin Tinubu a matsayin wadanda suka zama dole domin sake gina kasar.<\/p>\n<p><em>&#8220;Na ga haske kuma na fahimci cewa abin da Shugaban Kasa ke yi wa Najeriya shi ne abin da ya dace a yi&#8221; in ji shi.<\/em><\/p>\n<p>A cewarsa karuwar albarkatun da jihohi da kananan hukumomi ke samu ya taimaka musu wajen aiwatar da ayyuka da kuma sauke nauyin da ke kansu ciki har da biyan albashi da kudaden fansho.<\/p>\n<p>Ya kuma yaba da shirin gwamnatin na bayar da lamunin karatu ga dalibai inda ya ce hakan zai taimaka wa daliban Najeriya kammala karatun jami&#8217;a ba tare da fuskantar matsalolin kudi ba.<\/p>\n<p><em>&#8220;Dole ne mu yi hakuri. Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata kuma na yi imani cewa ana samun sabuwar Najeriya&#8221; in ji Sanata Okowa.<\/em><\/p>\n<p>Ya yi kira ga matasan Najeriya da su goyi bayan sake zaben Shugaba Tinubu yana mai cewa manufofin Shugaban Kasan an tsara su ne domin tabbatar da makomarsu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara ya yi alkawarin samar da akalla kuri&#8217;u miliyan uku ga Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Janairun 2027 inda ya ba shi tabbacin cewa jihar za ta ba shi cikakken goyon baya. Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne yayin taron yakin neman zaben Shugaba &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":7585,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-7582","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7582","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7582"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7582\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7587,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7582\/revisions\/7587"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7585"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7582"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7582"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7582"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}