{"id":7335,"date":"2026-11-04T06:25:57","date_gmt":"2026-11-04T06:25:57","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7335"},"modified":"2026-11-04T06:25:57","modified_gmt":"2026-11-04T06:25:57","slug":"unesco-ta-soki-rashin-hukunta-masu-aikata-laifuka-kan-yan-jarida","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/04\/unesco-ta-soki-rashin-hukunta-masu-aikata-laifuka-kan-yan-jarida\/","title":{"rendered":"UNESCO Ta Soki Rashin Hukunta Masu Aikata Laifuka Kan &#8216;Yan Jarida"},"content":{"rendered":"<p><strong>Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al&#8217;adu wato UNESCO ta bayyana cewa rashin hukunta wadanda ke kashe &#8216;yan jarida ya karu a duniya a karon farko cikin fiye da shekaru goma.<\/strong><\/p>\n<p>A cikin wani rahoto da aka fitar domin dacewa da Ranar Duniya ta Kawo Karshen Rashin Hukunta Masu Aikata Laifuka kan &#8216;Yan Jarida hukumar ta bayyana cewa tun daga shekarar 1993 an kashe &#8216;yan jarida sama da 1,700 a duniya baki daya.<\/p>\n<p>Ta kara da cewa tsakanin shekarar 2024 da 2025 &#8216;yan jarida da sauran ma&#8217;aikatan kafofin watsa labarai 189 sun rasa rayukansu\u2014adadin da ya haura na shekaru biyu da suka gabata da kashi 20 cikin dari.<\/p>\n<p>UNESCO ta ce a cikin kowane shari&#8217;o&#8217;i 10 a shari&#8217;o&#8217;i 9 ba a hukunta wadanda suka aikata kisan ba.<\/p>\n<p>Ta kara da cewa duk da cewa kisa shi ne mataki mafi tsanani na takaita aikin &#8216;yan jarida akwai kuma wasu barazanar da dama da suke fuskanta.<\/p>\n<p>Wadannan sun hada da sace mutane, azabtarwa, da sauran hare-hare na jiki har ma da cin zarafi\u2014musamman a duniyar yanar gizo.<\/p>\n<p>Yankin Gabas ta Tsakiya shi ne yankin da ya fi yawan &#8216;yan jarida da aka kashe inda aka kashe &#8216;yan jarida 97 a cikin shekaru biyun da suka gabata da yawa daga cikinsu suna da alaka da yakin da ake yi a Gaza.<\/p>\n<p>Sai dai nahiyar Afirka ma tana ci gaba da fuskantar kalubale masu tsanani.<\/p>\n<p>&#8216;Yan jarida a kasashe irin su Somaliya Uganda da yankin Sahel na fuskantar barazanar kisa tsoratarwa da cin zarafi ta yanar gizo.<\/p>\n<p>A bana kungiyar &#8216;Reporters Without Borders&#8217; (RSF) ta bayar da rahoton mutuwar &#8216;yan jarida biyu a nahiyar Afirka: daya a Uganda dayan kuma a Somaliya.<\/p>\n<p>UNESCO ta ce wannan yanayi yana haifar da tsoro ga kwararrun &#8216;yan jarida wanda hakan ke hana yaduwar bayanai ra&#8217;ayoyi da tunani cikin &#8216;yanci ga dukkan &#8216;yan kasa.<\/p>\n<p>Haka kuma ta yi gargadin cewa ana kara kai hare-hare kan &#8216;yan jarida a yankunan da ake fama da rikici ciki har da amfani da jiragen sama marasa matuka (drones).<\/p>\n<p>Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma lura cewa sanya rigar kariya ko kwalkwali mai dauke da alamar &#8216;yan jarida ba ya bayar da tabbacin tsaro ga &#8216;yan jarida a wuraren da ake yaki.<\/p>\n<p>Ta yi kira da a kara daukar matakan tabbatar da adalci da kuma kare &#8216;yan jarida tana mai jaddada cewa alamomin tantance &#8216;yan jarida ba su ba da garantin kare lafiyarsu ba.<\/p>\n<p>An zabi ranar 2 ga watan Nuwamba ne domin tunawa da kisan &#8216;yan jarida biyu na gidan rediyon Radio France International a kasar Mali a shekarar 2013<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al&#8217;adu wato UNESCO ta bayyana cewa rashin hukunta wadanda ke kashe &#8216;yan jarida ya karu a duniya a karon farko cikin fiye da shekaru goma. A cikin wani rahoto da aka fitar domin dacewa da Ranar Duniya ta Kawo Karshen Rashin Hukunta Masu Aikata Laifuka kan &#8216;Yan Jarida &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":7338,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-7335","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7335","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7335"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7335\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7340,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7335\/revisions\/7340"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7338"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7335"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7335"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7335"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}