{"id":7153,"date":"2026-10-31T15:25:57","date_gmt":"2026-10-31T15:25:57","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7153"},"modified":"2026-10-31T15:25:57","modified_gmt":"2026-10-31T15:25:57","slug":"gwamnan-kano-ya-rantsar-da-kwamishinoni-masu-ba-da-shawara-da-sauransu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/31\/gwamnan-kano-ya-rantsar-da-kwamishinoni-masu-ba-da-shawara-da-sauransu\/","title":{"rendered":"Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Kwamishinoni Masu Ba Da Shawara Da Sauransu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf ya rantsar da kwamishinoni shida da aka nada sababbi da masu ba da shawara guda uku da kuma sakatarorin dindindin guda 19 a matsayin wani mataki na karfafa gudanar da mulki inganta ayyukan gudanarwa da kuma kyautata samar da ayyuka ga al&#8217;umma a fadin jihar.<\/strong><\/p>\n<p>An gudanar da bikin rantsarwar ne bayan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da nadin kwamishinonin shida a ranar 26 ga watan Oktoba 2026 biyo bayan kammala tsarin tantancewa da majalisar ta gudanar.<\/p>\n<p>Kwamishinonin da aka rantsar sun hada da: Air Commodore Salisu Yusha\u2019u (mai ritaya) &#8211; wanda aka sanya a Ma\u2019aikatar Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman Ibrahim Namadi Dala &#8211; Ma\u2019aikatar Zuba Jari Farfesa Sani Lawan Manunfashi &#8211; Ma\u2019aikatar Ilimi Mai Zurfi Muktar Ishaq Yakasai &#8211; Ma\u2019aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa &#8211; Ma\u2019aikatar Kimiyya da Fasaha da kuma Idris Garba Mustapha &#8211; Ma\u2019aikatar Ayyuka na Musamman.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Sanata Barau Ya Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zabe Na Kano Ta Arewa<\/p>\n<p>A wani labarin kuma Gwamna Yusuf ya sanar da yin garambawul kadan a majalisar zartarwarsa inda ya sauya wa wasu kwamishinoni biyu ma\u2019aikatu.<\/p>\n<p>A karkashin wannan sabon tsari an tura Dr. Ibrahim Abdullahi Waiya wanda a baya yake rike da mukamin Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida zuwa Ma\u2019aikatar Matasa da Ci Gaban Wasanni yayin da aka tura Hamza Kachaco zuwa Ma\u2019aikatar Muhalli.<\/p>\n<p>Wannan sauyi ya bar Ma\u2019aikatar Labarai da Harkokin Cikin Gida da kuma Ma\u2019aikatar Ma\u2019adanai ba tare da shugabanni ba a halin yanzu har sai gwamnatin jihar ta yanke wani sabon hukunci a kansu.<\/p>\n<p>Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade da sauye-sauye ne domin karfafa cibiyoyin gwamnati inganta ayyukan gudanarwa da kuma sake tsara muhimman ma\u2019aikatu domin samar da ingantaccen hidima ga jama&#8217;a.<\/p>\n<p>Gwamna Yusuf ya yi kira ga kwamishinoni masu ba da shawara da sakatarorin dindindin da aka nada kwanan nan da su nuna sadaukarwa gaskiya da kuma rikon amana wajen gudanar da ayyukansu.<\/p>\n<p>Ya jaddada muhimmancin sanya moriyar jama&#8217;a a gaba fiye da bukatun kansu tare da yin aiki tare domin ci gaban Jihar Kano baki daya.<\/p>\n<p>Bugu da kari Gwamnan ya umarci wadanda aka nadan da su tafiyar da ayyukansu bisa tsarin ci gaban gwamnatinsa tare da tabbatar da cewa al&#8217;umma sun ci gajiyar manufofi da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Ya taya sabbin wadanda aka nada murna tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukan da aka dora musu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf ya rantsar da kwamishinoni shida da aka nada sababbi da masu ba da shawara guda uku da kuma sakatarorin dindindin guda 19 a matsayin wani mataki na karfafa gudanar da mulki inganta ayyukan gudanarwa da kuma kyautata samar da ayyuka ga al&#8217;umma a fadin jihar. An gudanar da bikin rantsarwar &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":7156,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-7153","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7153","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7153"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7153\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7157,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7153\/revisions\/7157"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7156"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7153"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7153"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7153"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}