{"id":7089,"date":"2026-10-30T13:30:12","date_gmt":"2026-10-30T13:30:12","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=7089"},"modified":"2026-10-30T13:30:12","modified_gmt":"2026-10-30T13:30:12","slug":"hadarin-jirgin-helikwafta-na-italiya-a-bosnia-ya-yi-sanadiyyar-mutuwar-mutane-hudu-tare-da-jikkata-wasu-11","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/30\/hadarin-jirgin-helikwafta-na-italiya-a-bosnia-ya-yi-sanadiyyar-mutuwar-mutane-hudu-tare-da-jikkata-wasu-11\/","title":{"rendered":"Hadarin Jirgin Helikwafta Na Italiya  A Bosnia Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Hudu Tare Da Jikkata Wasu 11"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Ma\u2019aikatar Tsaron Italiya ta sanar cewa, wani jirgin helikwafta na sojan Italiya wanda ke aiki a karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Turai a Bosnia da Herzegovina ya yi hatsari a ranar Alhamis. Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 11.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ma\u2019aikatar ta bayyana cewa biyu daga cikin wadanda suka mutu sojojin Italiya ne yayin da sauran biyun kuma mambobi ne na rundunar sa-kai ta kungiyar Red Cross ta Italiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ta kara da cewa dukkan mutane 11 da suka jikkata suna samun kulawar likitoci kuma babu wanda ke cikin halin da zai sanya rayuwarsa cikin hadari mai tsanani.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jimillar mutane 15 ne ke cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsarin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ministan Tsaron Italiya Guido Crosetto ya mika sakon ta&#8217;aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa inda ya bayyana lamarin a matsayin lokaci na tsananin bakin ciki.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce: &#8220;<em>A wannan lokaci na tsananin bakin ciki tunanina yana tare da iyalan wadanda muka rasa da farko. Ina mika musu ta&#8217;aziyyata ta kashin kai, da kuma ta&#8217;aziyyar dukkan ma&#8217;aikatar Tsaro.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Hatsarin Jirgin Masu Yawon Bude Ido a Peru Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 13 Kusa da Nazca Lines<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kamfanin dillancin labarai na Italiya ANSA ya rawaito cewa jirgin ya fadi ne a kauyen Gorice da ke gundumar Brcko.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hotunan da kafofin yada labarai na yankin suka wallafa sun nuna jirgin sojan wanda ake amfani da shi wajen jigilar kaya ko mutane a juye a kasa kuma ya farfashe gunduwa-gunduwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Crosetto ya ce: &#8220;<em>Babu kalmomin da za su iya rage radadin irin wannan babban rashi.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jirgin yana aiki ne a karkashin &#8216;Operation Althea&#8217;<span class=\"Apple-converted-space\">\u00a0 <\/span>wato tawagar Tarayyar Turai (EUFOR) da ke da alhakin sa ido kan aiwatar da Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Dayton wadda ta kawo karshen yakin Bosnia.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ma\u2019aikatar Tsaron Italiya ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin da kuma yanayin da ya faru a lokacin.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ma\u2019aikatar Tsaron Italiya ta sanar cewa, wani jirgin helikwafta na sojan Italiya wanda ke aiki a karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Turai a Bosnia da Herzegovina ya yi hatsari a ranar Alhamis. Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 11. Ma\u2019aikatar ta bayyana cewa biyu daga cikin wadanda &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":7091,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-7089","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7089","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7089"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7089\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7093,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7089\/revisions\/7093"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7091"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7089"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7089"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7089"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}