{"id":6962,"date":"2026-10-29T07:26:29","date_gmt":"2026-10-29T07:26:29","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6962"},"modified":"2026-10-29T07:26:29","modified_gmt":"2026-10-29T07:26:29","slug":"putin-ya-yi-alkawarin-goyon-bayan-ci-gaban-afirka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/29\/putin-ya-yi-alkawarin-goyon-bayan-ci-gaban-afirka\/","title":{"rendered":"Putin Ya Yi Alkawarin Goyon Bayan Ci Gaban Afirka"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi al\u0199awarin zurfafa ha\u0257in gwiwa da \u0199asashen Afirka a fannin kasuwanci noma kayayyakin more rayuwa da fasaha.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce Rasha a shirye take ta tallafa wa ci gaban nahiyar ta hanyar musayar kwarewa da kuma samar da kayayyaki a cikin gida.<\/span><\/p>\n<p>Putin ya yi al\u0199awarin ne a ranar Laraba a taron kolin Rasha da Afirka na uku da aka yi a Moscow.<\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sanarwar ta samu halartar shugabannin Afirka da wakilan gwamnati daga \u0199asashe 48 inda ake sa ran shugabannin Afirka 22 za su yi tattaunawa ta \u0253angarorin biyu kan batutuwa da suka ha\u0257a da kasuwanci tsaro makamai da kayayyakin hatsi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Putin ya ce &#8220;<em>Afirka na \u0199ara zama muhimmiyar &#8216;yar wasa a harkokin tattalin arziki da siyasa na duniya.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana cewa Rasha na goyon bayan \u0199arin wakilcin Afirka a cibiyoyin \u0199asa da \u0199asa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Rasha ya soki abin da ya bayyana a matsayin \u0199o\u0199arin \u0199asashen Yamma na amfani da albarkatun Afirka da kuma ci gaba da dogaro da \u0199asashe kan basussuka yana mai jayayya cewa shirye-shiryen ku\u0257i marasa kyau na iya rage ci gaba na dogon lokaci.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Putin ya ce Rasha a shirye take ta raba \u0199warewarta gami da fasahar dijital da kuma ha\u0253aka samar da kayayyaki na cikin gida maimakon mai da hankali kawai kan siyan kayan masarufi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Mnangagwa a Moscow don taron kolin Rasha da Afirka<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cewarsa irin wannan hadin gwiwa na iya samar da ayyukan yi kara kudaden shiga na haraji da kuma tallafawa ci gaban tattalin arziki a fadin kasashen Afirka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Ciniki Noma da Kayayyakin more rayuwa<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Rasha ya ce Moscow a shirye take ta ci gaba da ayyukan hadin gwiwa a fannin sufuri da kayayyakin more rayuwa na noma da kuma samar da hatsi da taki ga karin kasashen Afirka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya kuma nuna goyon baya ga kara tasirin Afirka a Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Taron wanda aka fara gudanarwa a shekarar 2019 wani bangare ne na kokarin Rasha na karfafa dangantakarta ta siyasa tattalin arziki da soja da kasashen Afirka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kafafen yada labarai na gwamnatin Rasha cibiyoyin al&#8217;adu da kamfanoni sun kuma nemi fadada kasancewarsu a nahiyar ciki har da hakar ma&#8217;adinai da samar da wutar lantarki.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Shugabannin Afirka Sun Nuna Ha\u0257in Kai<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Firaministan Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo ya bayyana hadin gwiwar kasarsa da Rasha a matsayin gaskiya kuma bisa ga muradun juna.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake magana da gidan talabijin na Rasha RT Ouedraogo ya ce hadin gwiwar ya girmama harsuna da al&#8217;adun Afirka yana kwatanta shi da dangantakar tarihi ta Burkina Faso da Faransa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Rasha ta fuskanci suka daga gwamnatocin kasashen Yamma dangane da ayyukan dakarunta masu kama da na soja a kasashen Afirka ciki har da zarge-zargen cewa suna goyon bayan gwamnatocin soji tare da ciyar da manufofin siyasa da dabarun Rasha gaba. Gwamnatin Rasha ta musanta wadannan zarge-zarge.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wannan taro kuma wani bangare ne na kokarin da Rasha ke yi na karfafa dangantaka da kasashen da ke yankin Kudancin duniya (Global South) a daidai lokacin da kasashen Yamma ke ci gaba da matsa mata lamba dangane da yakin da take yi a Ukraine.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi al\u0199awarin zurfafa ha\u0257in gwiwa da \u0199asashen Afirka a fannin kasuwanci noma kayayyakin more rayuwa da fasaha. Ya ce Rasha a shirye take ta tallafa wa ci gaban nahiyar ta hanyar musayar kwarewa da kuma samar da kayayyaki a cikin gida. Putin ya yi al\u0199awarin ne a ranar Laraba a &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":6965,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-6962","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6962","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6962"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6962\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6967,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6962\/revisions\/6967"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6965"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6962"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6962"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6962"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}