{"id":6880,"date":"2026-10-27T14:25:42","date_gmt":"2026-10-27T14:25:42","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6880"},"modified":"2026-10-27T14:25:42","modified_gmt":"2026-10-27T14:25:42","slug":"qatar-ta-bayar-da-bas-guda15-a-matsayin-kyauta-ga-senegal","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/27\/qatar-ta-bayar-da-bas-guda15-a-matsayin-kyauta-ga-senegal\/","title":{"rendered":"Qatar Ta Bayar Da Bas Guda15 A Matsayin Kyauta Ga Senegal"},"content":{"rendered":"<p><strong>Kasar Qatar ta bayar da kyautar motocin bas guda 15 ga kasar Senegal domin tallafawa fannin sufuri gabanin gasar Olympics ta matasa ta Dakar 2026 yayin da kasar ta Yammacin Afirka ke shirin karbar bakuncin gasar Olympics ta farko a nahiyar Afirka.<\/strong><\/p>\n<p>Motocin bas din wadanda aka kawo tare da kayan aikin tsaro wani bangare ne na shirin Qatar na taimaka wa kasashen da ke karbar bakuncin manyan gasannin wasanni na duniya ta hanyar raba gogewarta wajen shirya gasanni na matakin duniya.<\/p>\n<p>Qatar ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2022 da gasar cin kofin nahiyar Asiya (Asian Cup) da kuma gasar motoci ta Formula One Grand Prix. Haka kuma tana shirin karbar bakuncin gasar wasannin nahiyar Asiya (Asian Games) a shekarar 2030.<\/p>\n<p>Ibrahima Wade Babban Mai Gudanarwa na kwamitin shirya gasar Dakar 2026 ya bayyana cewa <em><strong>&#8220;wannan kyauta za ta karfafa karfin Senegal wajen shirya manyan gasanni na kasa da kasa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Ya ce kayan aikin za su inganta fannin sufuri da tsaro tare da taimakawa wajen bunkasa kwarewar &#8216;yan kasar wajen tafiyar da manyan gasannin wasanni.<\/p>\n<p>An tsara bude gasar Olympics ta matasa ta Dakar 2026 a ranar 31 ga watan Oktoba inda za ta hada matasan &#8216;yan wasa daga kasashe da yankuna sama da 200 domin gudanar da gasa na tsawon makonni biyu.<\/p>\n<p>Ana sa ran &#8216;yan wasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18 za su fafata a wasanni daban-daban guda 25 inda za a gudanar da gasannin a wurare daban-daban a birnin Dakar da kewaye.<\/p>\n<p>Wannan gasa tana zama wani muhimmin ci gaba a tarihi ga wasanni a Afirka kuma tana bai wa Senegal damar nuna kwarewarta wajen shirya abubuwa da al&#8217;adunta da kuma karimcin mutanenta ga duniya baki daya.<\/p>\n<p>Tallafin na Qatar ya kuma nuna muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa wajen bunkasa wasanni inda ake sa ran kyautar za ta taimaka wajen tsare-tsaren sufuri da tsaro a yayin gudanar da gasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>African News\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kasar Qatar ta bayar da kyautar motocin bas guda 15 ga kasar Senegal domin tallafawa fannin sufuri gabanin gasar Olympics ta matasa ta Dakar 2026 yayin da kasar ta Yammacin Afirka ke shirin karbar bakuncin gasar Olympics ta farko a nahiyar Afirka. Motocin bas din wadanda aka kawo tare da kayan aikin tsaro wani bangare &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":6883,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-6880","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6880","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6880"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6880\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6884,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6880\/revisions\/6884"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6883"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6880"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6880"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6880"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}