{"id":6746,"date":"2026-10-24T16:03:09","date_gmt":"2026-10-24T16:03:09","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6746"},"modified":"2026-10-24T16:03:09","modified_gmt":"2026-10-24T16:03:09","slug":"faransa-ta-tura-jamian-tsaro-gabanin-zanga-zanga","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/24\/faransa-ta-tura-jamian-tsaro-gabanin-zanga-zanga\/","title":{"rendered":"Faransa Ta Tura Jami&#8217;an Tsaro Gabanin Zanga-Zanga"},"content":{"rendered":"<p><strong>Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Laurent Nunez ya bukaci &#8216;yan sanda da su dauki mataki cikin gaggawa kan masu tayar da zaune tsaye da masu sace-sacen kaya yayin da aka tura jami&#8217;an tsaro a sassan birnin Paris gabanin zanga-zangar da ake fargabar za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali.<\/strong><\/p>\n<p>A yayin da yake jawabi ga &#8216;yan sanda a Paris Nunez ya gargadi jami&#8217;an cewa za su fuskanci yunkurin kai hari kan shaguna cibiyoyin gwamnati da kuma jami&#8217;an tsaro.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Dole ne mu kasance cikin shiri na musamman don daukar mataki nan take. Akwai kiran da aka yi daga kungiyoyin siyasa da kuma miyagu na aikata laifuka don haifar da rudani zai zama dogon yini<\/em>&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Motocin &#8216;yan sanda sun kewaye ginin Arc de Triomphe yayin da sojoji daga rundunar yaki da ta&#8217;addanci ke sintiri a kan titin Champs-Elysees domin kare muhimman wurare a Paris daga sake aukuwar tarzomar da ta girgiza Faransa a makon da ya gabata.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Faransa Ta Bayar Da Rahoton Kamuwar Mutum Na Farko Da Kwayar Cutar Shamonda<\/p>\n<p>Ayyukan barna da na sace-sacen kaya yayin zanga-zangar ranar 17 ga watan Oktoba sun haifar da damuwa game da ikon gwamnati na tabbatar da zaman lafiya da tsarin jama&#8217;a. Wannan ya sa Nunez ya tura jami&#8217;an &#8216;yan sanda 70,000 a fadin kasar domin zanga-zangar ranar Asabar adadin da ya zarce na baya da jami&#8217;a 10,000.<\/p>\n<p>Hau-hawan farashin kayayyakin rayuwa da kuma tabarbarewar ayyukan da gwamnati ke samarwa jama&#8217;a sun sa dalibai ma&#8217;aikata da kungiyoyin kwadago fitowa kan tituna a &#8216;yan makonnin nan.<\/p>\n<p>Reuters\/Sulaiman Ibrahim Muhammad<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Laurent Nunez ya bukaci &#8216;yan sanda da su dauki mataki cikin gaggawa kan masu tayar da zaune tsaye da masu sace-sacen kaya yayin da aka tura jami&#8217;an tsaro a sassan birnin Paris gabanin zanga-zangar da ake fargabar za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali. A yayin da yake jawabi &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":6749,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-6746","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6746","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6746"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6746\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6750,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6746\/revisions\/6750"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6749"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6746"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6746"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6746"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}