{"id":6582,"date":"2026-10-23T08:25:17","date_gmt":"2026-10-23T08:25:17","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6582"},"modified":"2026-10-23T08:25:17","modified_gmt":"2026-10-23T08:25:17","slug":"girgizar-%c6%99asa-mai-%c6%99arfi-ta-halaka-mutane-16-ta-jikkata-wasu-32-a-%c6%99asar-sin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/23\/girgizar-%c6%99asa-mai-%c6%99arfi-ta-halaka-mutane-16-ta-jikkata-wasu-32-a-%c6%99asar-sin\/","title":{"rendered":"Girgizar \u0199asa Mai \u0199arfi Ta Halaka Mutane 16 Ta Jikkata Wasu 32 A \u0199asar Sin"},"content":{"rendered":"<p><strong>Wata girgizar kasa mai karfin awo 7 ta afku a yankin Tibet dake kudu maso yammacin kasar Sin inda ta yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da jikkata wasu 32.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Rahotannin kafofin yada labarai na yankin sun bayyana cewa girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 10:33 na dare a lokacin yankin ranar Alhamis. Ya zuwa karfe 2:25 na asubahin ranar Juma&#8217;a mutane 11 ne ke dauke da munanan raunuka yayin da wasu 21 suka samu raunuka marasa tsanani.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Bayanai daga Cibiyar Kula da Girgizar Kasa ta kasar Sin (CENC) sun nuna cewa girgizar ta afku ne a wani yanki mai tsayi da ba a cika samun yawan jama&#8217;a ba a Nagqu arewacin Tibet a zurfin kilomita 10 a karkashin kasa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Matsakaicin tsayin wurin a cikin radius na kilomita biyar daga inda girgizar ta fi karfi ya kai kimanin mita 4,864 sama da matakin teku kuma wurin yana da nisan kimanin kilomita 400 daga Lhasa babban birnin yankin Tibet.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Mutane da dama sun mutu bayan girgizar kasa mai karfin awo 7.7 ta afku a Indonesia<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Rahotanni sun bayyana cewa, hukumomin yankin sun gano akalla mutane biyu da suka jikkata a wani kauye kusa da cibiyar girgizar yayin da wasu gidaje a kauyukan da ke makwabtaka da wurin suka samu tsage.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Bidiyoyin da kafofin yada labarai na yankin suka fitar sun nuna mazauna yankin suna barin gidajensu don neman mafaka a waje ko kuma a cikin motocin da ke ajiye biyo bayan girgizar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, girgizar kasar mai karfi ta tashe su daga barci inda ya kara da cewa ana iya jin karar tsagewar ginin gidan yayin da girgizar ke faruwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">CENC ta bayyana cewa an ji tasirin girgizar kasar sosai a yankunan da ke kewaye.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Rahotanni sun ce an tura tawagogin kwana-kwana da na ceto na yankin zuwa yankin da abin ya shafa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Bisa bayanan CENC an kuma samu wasu kananan girgizar kasa masu karfin awo tsakanin 3 da 4 a yankunan da ke kewaye bayan babbar girgizar kasar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wannan ita ce girgizar kasa mafi karfi da ta taba afkuwa a kasar Sin tun watan Janairun 2024.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A shekarar 2010 wata girgizar kasa mai karfin awo 7.1 ta afku a Yushu a lardin Qinghai da ke makwabtaka da yankin inda ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 2,698 yayin da wasu kusan 300 suka bace.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata girgizar kasa mai karfin awo 7 ta afku a yankin Tibet dake kudu maso yammacin kasar Sin inda ta yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da jikkata wasu 32. Rahotannin kafofin yada labarai na yankin sun bayyana cewa girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 10:33 na dare a lokacin yankin ranar Alhamis. &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":6584,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-6582","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6582","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6582"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6582\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6586,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6582\/revisions\/6586"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6584"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6582"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6582"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6582"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}