{"id":6478,"date":"2026-10-21T07:34:28","date_gmt":"2026-10-21T07:34:28","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6478"},"modified":"2026-10-21T07:34:28","modified_gmt":"2026-10-21T07:34:28","slug":"%c6%99ungiyar-aiki-na-shugaban-%c6%99asa-sun-gabatar-da-kudirin-dokar-yan-sanda-na-%c6%99asa-domin-dubawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/21\/%c6%99ungiyar-aiki-na-shugaban-%c6%99asa-sun-gabatar-da-kudirin-dokar-yan-sanda-na-%c6%99asa-domin-dubawa\/","title":{"rendered":"\u0198ungiyar Aiki Na Shugaban \u0198asa Sun Gabatar Da Kudirin Dokar &#8216;Yan Sanda Na \u0198asa Domin Dubawa"},"content":{"rendered":"<p><strong>Kwamitin Aiki na Shugaban Kasa kan Kudirin Dokar &#8216;Yan Sanda na Kasa ya kammala matakin tsara daftarin aikin da aka dora masa kuma ya mika daftarin Kudirin Dokar &#8216;Yan Sanda na Kasa na shekarar 2026\u2014tare da wasu kudirori 29 na gyare-gyaren dokoki masu alaka da shi\u2014ga Ma&#8217;aikatar Shari&#8217;a ta Tarayya domin a duba su ta fuskar tsarin doka tare da tantance ingancinsu.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban Kwamitin wanda kuma shi ne Babban Jami&#8217;in Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an mika wadannan daftarin dokoki ga Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari&#8217;a a ranar Litinin 19 ga watan Oktoba 2026 daidai da tsarin aikin da aka amince wa Kwamitin su bi.<\/p>\n<p>Gbajabiamila ya bayyana cewa Ma&#8217;aikatar Shari&#8217;ar za ta gudanar da cikakken bincike na doka kan daftarin dokokin domin tabbatar da cewa sun yi daidai da ka&#8217;idoji da tsare-tsaren da aka amince da su wajen tsara dokoki tare da duba ko akwai wani karo da dokokin da ke aiki a halin yanzu.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa ana sa ran Ma&#8217;aikatar Shari&#8217;ar za ta kammala aikin tantancewar sannan ta mayar da daftarin dokokin ga Kwamitin a ranar Juma&#8217;a 30 ga watan Oktoba 2026 ko kafin wannan ranar.<\/p>\n<p>A cewarsa bayan haka Kwamitin zai sake duba daftarin dokokin a karo na karshe kafin ya gabatar da su ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu matakin da zai zama kammala aikin da aka ba wa Kwamitin a hukumance.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6482\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/WhatsApp-Image-2026-10-20-at-18.52.34-1-300x187.jpeg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"187\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/WhatsApp-Image-2026-10-20-at-18.52.34-1-300x187.jpeg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/WhatsApp-Image-2026-10-20-at-18.52.34-1.jpeg 701w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Kudirin dokar &#8216;yan sanda na kasa da aka gabatar yana da nufin kafa tsarin doka da na kundin tsarin mulki domin samar da tsarin &#8216;yan sanda mai bangarori biyu a Najeriya wato rundunar &#8216;yan sandan tarayya da kuma rundunonin &#8216;yan sandan jihohi.<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara bayyana cewa shirya wannan kudirin dokar &#8216;yan sanda na kasa yana tafiya ne tare da aikin duba kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (Gyara na Shida) da majalisun dokokin jihohi ke gudanarwa a halin yanzu tsari ne da dole ne a kammala shi kafin a mika kudirin dokar &#8216;yan sandan ga Majalisar Dokokin Tarayya.<\/p>\n<p>Gbajabiamila ya sake jaddada kudurin tawagar aikin na ganin an bi tsari mai zurfi da gaskiya domin samar da cikakken tsarin doka wanda za a gabatar wa Shugaban Kasa sannan daga baya a mika shi ga Majalisar Dokokin Tarayya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kwamitin Aiki na Shugaban Kasa kan Kudirin Dokar &#8216;Yan Sanda na Kasa ya kammala matakin tsara daftarin aikin da aka dora masa kuma ya mika daftarin Kudirin Dokar &#8216;Yan Sanda na Kasa na shekarar 2026\u2014tare da wasu kudirori 29 na gyare-gyaren dokoki masu alaka da shi\u2014ga Ma&#8217;aikatar Shari&#8217;a ta Tarayya domin a duba su ta &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":6481,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-6478","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6478","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6478"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6478\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6483,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6478\/revisions\/6483"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6481"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6478"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6478"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6478"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}