{"id":6382,"date":"2026-10-19T07:46:34","date_gmt":"2026-10-19T07:46:34","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6382"},"modified":"2026-10-19T07:46:34","modified_gmt":"2026-10-19T07:46:34","slug":"kaduna-ta-karbi-byakuncin-gasar-wasanni-ta-sharia-ta-kasa-karo-na-32","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/19\/kaduna-ta-karbi-byakuncin-gasar-wasanni-ta-sharia-ta-kasa-karo-na-32\/","title":{"rendered":"Kaduna Ta Karbi Byakuncin Gasar Wasanni Ta Shari&#8217;a Ta Kasa Karo Na 32"},"content":{"rendered":"<p><strong>Jihar Kaduna ce ke karbar bakuncin gasar wasanni ta 32 ta bangaren shari&#8217;a (Judiciary Sports Competition). Gwamnatin jihar da Kungiyar Wasanni ta Kasa ta Bangaren Shari&#8217;a (NASAJ) sun jaddada muhimmancin wasanni wajen inganta walwala hadin kai da ci gaban kwararru a tsakanin jami&#8217;ai da ma&#8217;aikatan bangaren shari&#8217;a.<\/strong><\/p>\n<p>Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari&#8217;a James Atung Kanyip, ne ya bude gasar a ranar Asabar 17 ga Oktoba 2026 a filin Murtala Square da ke Jihar Kaduna a Arewacin Najeriya a madadin Gwamna Uba Sani.<\/p>\n<p>Kanyip ya bayyana cewa gasar tana ba wa ma&#8217;aikatan shari&#8217;a daga sassan kasar nan damar inganta lafiyar jikinsu karfafa alakar aiki da kuma inganta dabi&#8217;u irin su ladabi adalci aiki tare da girmama juna.<\/p>\n<p>Ya yi nuni da cewa ingancin aikin shari&#8217;a ba ya dogara ne kawai kan dokoki tsare-tsare da kayan aiki ba har ma ya dogara kan kwarewa gaskiya da walwalar mutanen da ke da alhakin gudanar da shari&#8217;a.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga mahalarta gasar da su fafata cikin adalci, su bi dokoki kuma su nuna halin &#8216;yan wasa na gari a duk tsawon lokacin gasar.<\/p>\n<p>Walwalar Jami&#8217;an Shari&#8217;a A cikin jawabinsa Babban Alkalin Jihar Kaduna Mai Shari&#8217;a Tukur Mu\u2019azu Aliyu\u2014wanda ya wakilci Babban Alkalin Najeriya Mai Shari&#8217;a Kudirat Kekere-Ekun\u2014ya bayyana cewa walwalar jami&#8217;ai da ma&#8217;aikatan bangaren shari&#8217;a na bukatar kulawa ta dindindin domin tabbatar da ingantaccen gudanar da shari&#8217;a.<\/p>\n<p>Ya bayyana wasanni da atisayen jiki a matsayin muhimman hanyoyi na kula da lafiya rage damuwa da kuma karfafa aiki tare ladabi da juriya.<\/p>\n<p>Mai Shari&#8217;a Aliyu ya kara da cewa gasar tana samar da dandamali ga ma&#8217;aikatan shari&#8217;a daga kotuna da cibiyoyi daban-daban don cudanya gina abota da karfafa jin cewa su duka &#8216;yan uwa ne a cikin iyali guda na bangaren shari&#8217;a.<\/p>\n<p>Tun da farko Shugaban Kungiyar Wasanni ta Kasa ta Bangaren Shari&#8217;a (NASAJ) Kwamrad Noah Sunday ya yaba wa Babban Alkalin Najeriya Gwamna Uba Sani da Babban Alkalin Jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka bayar wajen shirya gasar<\/p>\n<p>Ya bukaci mahalarta gasar da su rike ka&#8217;idojin ladabi gaskiya adalci da kwarewa yana mai jaddada cewa ana auna halin &#8216;yan wasa na gari ba wai kawai ta hanyar samun nasara ba har ma ta hanyar girmama wasu da kuma nuna ruhin shiga gasar. Gasar da ake yi kowace shekara tana tattaro jami&#8217;an shari&#8217;a da ma&#8217;aikata daga kotuna daban-daban da cibiyoyin shari&#8217;a a duk fadin kasar domin inganta lafiya zumunci da hadin gwiwa tsakanin hukumomi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jihar Kaduna ce ke karbar bakuncin gasar wasanni ta 32 ta bangaren shari&#8217;a (Judiciary Sports Competition). Gwamnatin jihar da Kungiyar Wasanni ta Kasa ta Bangaren Shari&#8217;a (NASAJ) sun jaddada muhimmancin wasanni wajen inganta walwala hadin kai da ci gaban kwararru a tsakanin jami&#8217;ai da ma&#8217;aikatan bangaren shari&#8217;a. Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari&#8217;a James Atung &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":6385,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[41],"tags":[],"class_list":["post-6382","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-sports-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6382","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6382"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6382\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6386,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6382\/revisions\/6386"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6385"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6382"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6382"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6382"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}