{"id":6191,"date":"2026-10-17T10:39:38","date_gmt":"2026-10-17T10:39:38","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6191"},"modified":"2026-10-17T10:39:38","modified_gmt":"2026-10-17T10:39:38","slug":"sarkin-moroko-mohammed-na-shida-ya-nada-mace-ta-farko-da-za-ta-jagoranci-gwamnatin-kasar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/17\/sarkin-moroko-mohammed-na-shida-ya-nada-mace-ta-farko-da-za-ta-jagoranci-gwamnatin-kasar\/","title":{"rendered":"Sarkin Moroko Mohammed Na Shida Ya Nada Mace Ta Farko Da Za Ta jagoranci Gwamnatin Kasar"},"content":{"rendered":"<p><strong>Sarkin Moroko Mohammed na shida ya nada mambobin sabuwar gwamnatin kasar a hukumance. A karon farko a tarihin kasar mace ce za ta jagoranci gwamnatin a matsayin Firayim Minista wato Fatima Ezzahra El Mansouri.<\/strong><\/p>\n<p>Jam&#8217;iyyarta mai ra&#8217;ayin tsakiya-dama wato &#8216;Authenticity and Modernity Party&#8217; (PAM) ita ce ta lashe zaben watan Satumba kuma ta kulla kawance da jam&#8217;iyyar &#8216;Istiqlal&#8217; mai ra&#8217;ayin dama tare da wasu kananan jam&#8217;iyyu biyu masu ra&#8217;ayin hagu.<\/p>\n<p>A dunkule suna da kujeru 210 cikin kujeru 395 da ke majalisar dokokin kasar.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Jam&#8217;iyyar PAM Ta Moroko Ta Kafa Gwamnatin Kawance Ta Jam&#8217;iyyu hudu<\/p>\n<p>An ci gaba da rike ministoci 13 daga cikin ministoci 31 na gwamnatin da ta gabata a cikin sabuwar majalisar zartarwar ciki har da Nasser Bourita a matsayin Ministan Harkokin Waje da Abdelouafi Laftit a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida.<\/p>\n<p>Fouzi Lekjaa wanda sabon shiga ne a jam&#8217;iyyar PAM\u00a0 kuma ya kasance ministan kasafin kudi a gwamnatin da ke barin gado sannan aka fi sani a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Moroko\u00a0 an daukaka shi zuwa matsayin Ministan Tattalin Arziki.<\/p>\n<p>Sabuwar gwamnatin ta kunshi mata bakwai har da Firayim Ministar wanda hakan ya yi daidai da yawan matan da ke cikin gwamnatin da ta gabata.<\/p>\n<p>Bayan ganawa da Sarkin El Mansouri ta bayyana cewa gwamnatin za ta aiwatar da &#8220;<em>tsare-tsare masu zurfi da buri wadanda za su iya biyan bukatun &#8216;yan kasa.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Zaben watan Satumba wanda ya samu karancin fitowar masu kada kuri&#8217;a mafi kankanta a cikin kusan shekaru 20 ya gudana ne a yayin da ake nuna damuwa game da tsadar rayuwa rashin aikin yi da rashin daidaito a tsakanin al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Sabuwar gwamnatin za ta fuskanci kalubalen magance wadannan matsaloli, yayin da take shirye-shiryen karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030 wadda za a gudanar tare da kasashen Spain da Portugal.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sarkin Moroko Mohammed na shida ya nada mambobin sabuwar gwamnatin kasar a hukumance. A karon farko a tarihin kasar mace ce za ta jagoranci gwamnatin a matsayin Firayim Minista wato Fatima Ezzahra El Mansouri. Jam&#8217;iyyarta mai ra&#8217;ayin tsakiya-dama wato &#8216;Authenticity and Modernity Party&#8217; (PAM) ita ce ta lashe zaben watan Satumba kuma ta kulla kawance &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":6194,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-6191","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6191","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6191"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6191\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6195,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6191\/revisions\/6195"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6194"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6191"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6191"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6191"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}