{"id":6123,"date":"2026-10-16T11:51:36","date_gmt":"2026-10-16T11:51:36","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6123"},"modified":"2026-10-16T11:51:36","modified_gmt":"2026-10-16T11:51:36","slug":"%c9%93arkewar-cutar-ebola-a-kongo-ta-ya%c9%97u-zuwa-shiyya-ta-takwas","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/16\/%c9%93arkewar-cutar-ebola-a-kongo-ta-ya%c9%97u-zuwa-shiyya-ta-takwas\/","title":{"rendered":"\u0181arkewar Cutar Ebola A Kongo Ta Ya\u0257u Zuwa Shiyya Ta Takwas"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC) ta bazu zuwa lardin North Ubangi kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda aka samu rahoton mutane biyu da suka kamu da cutar a cewar jami&#8217;an kiwon lafiya.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wannan sabon yanayi wanda hukumomin Kongo ba su sanar a hukumance ba tukuna ya sa yawan lardunan da cutar ta shafa ya kai takwas.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jami&#8217;an sun bayyana cewa an gano wadannan mutane a North Ubangi ne bayan samun rahotannin mutuwar mutane da ake zargin ta faru ne sakamakon cutar a yankin kiwon lafiya na Wapinda kusa da iyakar lardin Bas-Uele lamarin da ya sa hukumomin kiwon lafiya gudanar da gwaje-gwaje.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">An sanar da bullar cutar wacce nau&#8217;in kwayar cutar Ebola na &#8216;Bundibugyo&#8217; ke haifarwa a ranar 15 ga watan Mayu. A halin yanzu babu wani rigakafi ko takamaiman magani da aka amince da shi don yaki da wannan nau&#8217;in kwayar cutar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa ana sa ran fara gwajin rigakafi a kasar DRC kafin karshen watan Oktoba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Bisa ga alkaluman da aka fitar a ranar Laraba cutar ta shafi mutane sama da 9,000 kuma ta yi sanadin mutuwar mutane 4,441.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">An kuma samu rahoton kasancewar kwayar cutar a kasashen da ke makwabtaka da DRC ciki har da Uganda wacce ta sanar a watan Agusta cewa ta kubuta daga cutar Ebola.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A daya bangaren kuma kasar Kenya ta sanar a ranar Laraba cewa ta gano mutum na biyu da ke dauke da kwayar cutar. Mutumin dan uwa ne ga mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar wanda ya rasu a ranar 5 ga watan Oktoba.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC) ta bazu zuwa lardin North Ubangi kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda aka samu rahoton mutane biyu da suka kamu da cutar a cewar jami&#8217;an kiwon lafiya. Wannan sabon yanayi wanda hukumomin Kongo ba su sanar a hukumance ba tukuna ya sa yawan &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":6125,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42,45],"tags":[],"class_list":["post-6123","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","category-health"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6123","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6123"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6123\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6127,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6123\/revisions\/6127"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6125"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6123"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6123"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6123"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}