{"id":6083,"date":"2026-10-15T15:56:03","date_gmt":"2026-10-15T15:56:03","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6083"},"modified":"2026-10-15T15:58:11","modified_gmt":"2026-10-15T15:58:11","slug":"6083","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/15\/6083\/","title":{"rendered":"Jigon APC Ya Bayyana \u0199warin-gwiwar Nasarar Shugaba Tinubu A Karo Na Biyu"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Musa Illiyasu Kwankwaso wani mamba a Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana kwarin guiwa cewa Shugaba Ahmed Bola Tinubu zai lashe zaben wa&#8217;adi na biyu a shekarar 2027.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kwankwaso wanda kuma shi ne Daraktan Kudi a Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama\u2019are (Hadejia Jama\u2019are River Basin Development Authority)ya bayyana hakan ne a wurin taron Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC a ranar Laraba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce kasancewar da kuma shigar &#8216;yan siyasa daga jam&#8217;iyyu daban-daban a taron ya nuna yadda ake kara kar\u0253ar shugabancin Shugaba Tinubu, ba wai kawai a cikin jam&#8217;iyyar APC ba har ma a wajenta.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA:<a href=\"http:\/\/Kungiyar Gwamnonin APC (Progressives Governors\u2019 Forum) ta yi kira da a samu hadin kai a cikin jam'iyyar.\">http:\/\/Kungiyar Gwamnonin APC (Progressives Governors\u2019 Forum) ta yi kira da a samu hadin kai a cikin jam&#8217;iyyar.<\/a><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cewarsa &#8220;<em>wakilai da magoya bayan jam&#8217;iyyu irin su All Progressives Grand Alliance (APGA) da Labour Party da sauransu sun nuna goyon bayansu ga ci gaba da shugabancin Shugaban Kasa.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kwankwaso ya kuma yi nuni da wasu kalamai da aka danganta ga fitattun &#8216;yan siyasa \u00a0ciki har da Gwamnan Jihar Anambra Chukwuma Charles Soludo inda ya yi jayayyar cewa wadanda suka fahimci manufofin tattalin arziki da kuma yanayin da duniya ke ciki ne kawai za su iya fahimtar muhimmancin tsare-tsaren tattalin arzikin Shugaban Kasa yadda ya kamata.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana taron a matsayin wani sabon al&#8217;amari da ba a saba gani ba a tarihin siyasar Najeriya yana mai cewa Shugaba Tinubu ya hada &#8216;yan siyasar da a baya suke bangarori masu adawa da juna.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Ba a taba samun irin wannan a tarihin siyasar Najeriya ba inda mutum daya ya tara kusan dukkan jam&#8217;iyyun adawa ba wai &#8216;yan siyasar adawa kawai ba har ma da mutanen da ba su taba yarda su zauna wuri daya ba. Saboda Shugaba Tinubu sun amince su yi aiki tare don cimma manufa daya&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jigon na jam&#8217;iyyar APC ya jaddada cewa tattaunawar siyasa game da burin Tinubu na neman wa&#8217;adi na biyu ya kamata ya wuce batun zabe kawai ya kuma kunshi batun samar da wadata da ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci ga kasar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya amince cewa akwai kalubalen tattalin arziki da &#8216;yan Najeriya ke fuskanta amma ya jaddada cewa Shugaban Kasa ya kuduri aniyar aiwatar da manufofin gwamnatinsa da kuma cimma burin da ta sanya a gaba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;A gare ni kaddamar da wannan Majalisar Yakin <em>Neman Zabe tamkar wani taro ne na murnar sake zaben Shugaba Tinubu. Me kuma ya rage bayan da &#8216;yan Najeriya da muke son yin yakin neman zabe a gare su suka fito baki daya tare da nuna goyon baya ga mutum daya wato Tinubu?&#8221;<\/em> in ji Kwankwaso.<br \/>\n<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Dangane da Jihar Kano kuwa Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwar cewa tsarin hadin gwiwar siyasa da ya bayyana a matakin kasa zai kuma bayyana a cikin jihar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya yi nuni da yadda Shugaba Tinubu ya nuna karamci a bainar jama&#8217;a ga Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ciki har da ba shi hula a matsayin alama a matsayin wani abu da ya yi imani zai iya karfafa makomar siyasar Gwamnan.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kwankwaso ya bayyana kyakkyawan zato game da yiwuwar samun wa&#8217;adi na biyu ga Gwamna Yusuf da mataimakinsa Murtala Sule Garo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya kuma yi ikirarin cewa manyan &#8216;yan siyasa a jihar Kano suna aiki tare don cimma manufa guda wato goyon bayan sake zaben Shugaba Tinubu da Gwamna Yusuf.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga cikin wadanda ya ambata akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai Abubakar Kabir Abubakar Bichi Alhassan Ado Doguwa Abdulmumini Jibrin Kofa Sanata Kawu Sumaila tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam&#8217;iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya Ibrahim Shekarau da Alhassan Rirum.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cewar Kwankwaso &#8220;<em>hadin gwiwar da ke tsakanin wadannan manyan &#8216;yan siyasa yana nuna kudurin bai daya na ganin an cimma burin samun wa&#8217;adi na biyu ga Tinubu da kuma gwamnatin da Gwamna Yusuf ke jagoranta a Kano<\/em>.&#8221;<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya kammala da bayyana kwarin gwiwar cewa jam&#8217;iyyar APC za ta samu gagarumin goyon baya a fadin Arewacin Najeriya domin Shugaba Tinubu inda ya yi alkawarin cewa ana ci gaba da daukar matakai don tabbatar da cewa yankin ya bayar da kuri&#8217;unsa baki daya ga Shugaban.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Musa Illiyasu Kwankwaso wani mamba a Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana kwarin guiwa cewa Shugaba Ahmed Bola Tinubu zai lashe zaben wa&#8217;adi na biyu a shekarar 2027. Kwankwaso wanda kuma shi ne Daraktan Kudi a Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama\u2019are (Hadejia Jama\u2019are River Basin Development Authority)ya &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":6085,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-6083","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6083","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6083"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6083\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6087,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6083\/revisions\/6087"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6085"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6083"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6083"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6083"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}