{"id":6020,"date":"2026-10-14T06:48:37","date_gmt":"2026-10-14T06:48:37","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=6020"},"modified":"2026-10-14T06:48:37","modified_gmt":"2026-10-14T06:48:37","slug":"apc-da-kungiyar-arewa-sun-yi-kawance-don-kara-yawan-kuriu-a-zaben-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/14\/apc-da-kungiyar-arewa-sun-yi-kawance-don-kara-yawan-kuriu-a-zaben-2027\/","title":{"rendered":"APC Da Kungiyar Arewa Sun Yi Kawance Don Kara Yawan Kuri&#8217;u A Zaben 2027"},"content":{"rendered":"<p><strong>Jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi alkawarin yin aiki tare da kungiyar &#8216;Arewa for Asiwaju&#8217; (A4A) domin tattara karin masu kada kuri&#8217;a a fadin yankin Arewacin Najeriya gabanin babban zaben shekarar 2027.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban jam&#8217;iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin kungiyar A4A karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau suka kai masa ziyara a sakatariyar jam&#8217;iyyar ta kasa da ke Abuja.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: APC ta nada Gwamnan Kwara a matsayin Mataimakin Shugaba<\/p>\n<p>Farfesa Yilwatda ya bayyana cewa jam&#8217;iyyar za ta hada tsarin kungiyar cikin shirye-shiryen zabe domin karfafa yakin neman zabe da kuma inganta sakamakonta a zabukan shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa gwamnoni da majalisun dokokin jihohi.<\/p>\n<p>Ya yaba wa kungiyar bisa hada gwanayen shugabannin siyasa da matasa daga bangarori daban-daban inda ya bayyana tsarin kungiyar a matsayin mai hada kowa da kuma wakiltar yankin Arewacin Najeriya yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Shugaban na APC ya ce kungiyar za ta iya taimakawa wajen kawar da tunanin cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa ta hanyar bayyana ayyuka da shirye-shiryen da ake aiwatarwa a yankin.<\/p>\n<p>Ya ambaci manyan ayyukan hanyoyi bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) da kuma damar samun rancen kudin karatu ga dalibai a matsayin misalan ayyukan da zai amfani al&#8217;ummar Arewa.<\/p>\n<p>A cewarsa\u00a0 ayyukan hanyoyi da ake ginawa ko kuma ake shirin fara ginawa a Arewacin Najeriya sun kai tsawon kilomita sama da 3,000.<\/p>\n<p>Yilwatda ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki na yankin Arewa da su yi amfani da manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin inganta ilimi da fadada damar samun ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki da kuma tallafawa ci gaban yankin.<\/p>\n<p>Ya ce jam&#8217;iyyar za ta yi aiki tare da A4A domin tattara goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da &#8216;yan takarar APC a zaben 2027.<\/p>\n<p>Tun da farko Sanata Shekarau ya bayyana cewa an kafa kungiyar A4A ne domin tattara masu kada kuri&#8217;a a jihohi 19 na Arewa da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa kungiyar ta yi nazarin sakamakon zabukan da suka gabata domin gano wuraren da aka samu rauni karancin fitowar masu kada kuri&#8217;a, da kuma rashin sha&#8217;awar mutane wajen zabe inda ya kara da cewa za ta yi aiki don magance wadannan kalubale.<\/p>\n<p>Sanata Shekarau ya ce wannan shiri zai taimaka wajen karfafa kokarin APC Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa da gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa maimakon yin aiki daban daga tsarin jam&#8217;iyyar da ake da shi.<br \/>\nYa kara da cewa kungiyar ta nada masu kula da harkokinta a jihohi da sauran matakai domin karfafa hadin kan jama&#8217;a a matakin tushe da kuma wayar da kan jama&#8217;a game da nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a yankin Arewa.<\/p>\n<p>Tsohon gwamnan ya kuma gayyaci Farfesa Yilwatda zuwa bikin kaddamar da sakatariyar kungiyar da aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 17 ga Oktoba 2026 inda ya kara da cewa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya amince da gayyatar.<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Plateau ne Simon Lalong ya bayyana kungiyar ta A4A a matsayin dandamali da gogaggun shugabannin siyasa ke amfani da shi wajen tallafawa kokarin jam&#8217;iyyar APC a fagen zabe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi alkawarin yin aiki tare da kungiyar &#8216;Arewa for Asiwaju&#8217; (A4A) domin tattara karin masu kada kuri&#8217;a a fadin yankin Arewacin Najeriya gabanin babban zaben shekarar 2027. Shugaban jam&#8217;iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin kungiyar A4A karkashin jagorancin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":6023,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-6020","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6020"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6025,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020\/revisions\/6025"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6023"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6020"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6020"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6020"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}