{"id":5964,"date":"2026-10-13T14:32:25","date_gmt":"2026-10-13T14:32:25","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5964"},"modified":"2026-10-13T14:32:25","modified_gmt":"2026-10-13T14:32:25","slug":"2027-vp-shettima-woos-yan-arewa-don-sake-zaben-shugaba-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/13\/2027-vp-shettima-woos-yan-arewa-don-sake-zaben-shugaba-tinubu\/","title":{"rendered":"2027: VP Shettima Woos Yan Arewa Don Sake Zaben Shugaba Tinubu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya yi kira ga mutanen Arewa da su goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027 inda ya ba su tabbacin cewa babu abin da ya kamata su ji tsoro game da wa&#8217;adin mulki na biyu na Shugaban.<\/strong><\/p>\n<p>Ya bukaci shugabanni da al&#8217;ummar Arewa da su hada kai wajen goyon bayan shirin sake zaben Shugaba Tinubu yana mai bayyana wa&#8217;adin mulki na biyu a matsayin damar inganta ci gaba da kwanciyar hankali a yankin<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5968\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0143-1-768x512-1-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0143-1-768x512-1-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0143-1-768x512-1.jpg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya yi wannan kira ne a ranar Litinin da ta gabata yayin da ya karbi tawagar kungiyar &#8216;Arewa for Tinubu&#8217; (A4A) \u2013 wata kungiyar masu nazari da dabaru ta yankin Arewa da ke aiki domin ganin an sake zaben Shugaba Tinubu \u2013 wadanda suka kai masa ziyarar ban girma.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: 2027: Wike na hada kan masu ruwa da tsaki na Babban Birnin Tarayya (FCT) domin sake zaben Shugaba Tinubu<\/p>\n<p>Ya yi kira ga shugabanni a fadin yankin da su hada kai wuri guda tare da yin aiki domin ci gaban yankin da kuma jin dadin al&#8217;ummarsa wadanda ke cikin manyan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta sa a gaba.<img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5969\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0146-1-300x210.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"210\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0146-1-300x210.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0146-1-1024x718.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0146-1-768x538.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0146-1.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Mataimakin Shugaban Kasa ya ce, <strong><em>&#8220;Babu wani dalili da zai sa yankin Arewa ya ji tsoron sake zaben Shugaba Tinubu kasancewar yankin ya ci moriyar abubuwa da dama ta fuskar nada mutane a mukamai da kuma aiwatar da manyan ayyuka da shirye-shirye masu matukar tasiri.&#8221;<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Ya ce:<em><strong> &#8220;Mu hada kai a matsayinmu na al&#8217;umma domin bunkasa yankinmu da kuma ci gaban mutanenmu ta hanyar sake zaben wannan gwamnati. Muna cin moriya, kuma za mu ci gaba da samun karin fa&#8217;ida daga wannan gwamnati ta hanyoyi da dama<\/strong><\/em><em>&#8220;Bankin<strong> Noma (Bank of Agriculture) ya raba kudi har Naira biliyan 450 ga kananan manoma 700,000 a fadin Najeriya, kuma kusan kashi 70 cikin dari na wadanda suka ci moriyar tallafin &#8216;yan yankin Arewa ne.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Wannan gwamnati na aiki tukuru domin kammala manyan ayyuka masu muhimmanci da kuma kawo sauyi a sassa daban-daban na kasar nan. Ina ba ku tabbacin cewa Shugaban Kasa yana kaunar yankin Arewa, kuma zai ci gaba da yin aiki domin ci gaban yankin.<\/strong><\/em><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5972\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0151-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0151-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0151-1024x683.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0151-768x512.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0151.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Godiya<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasa ya nuna godiyarsa ga kungiyar bisa goyon bayan da suke bai wa Shugaba Bola Tinubu ba kakkautawa tare da yin kira gare su da su kara kaimi wajen hada karfi da karfe a matakan unguwanni al&#8217;ummomi da kananan hukumomi na yankin Arewa domin ganin an sake zaben Shugaban Kasar.<\/p>\n<p>Tun da farko Darakta Janar na kungiyar &#8216;Area for Asiwaju&#8217; kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru ya bayyana cewa kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai sun sanya yankin Arewa alfahari ta hanyar sake zaben Shugaba Tinubu.<img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5985\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0152-1-2-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0152-1-2-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0152-1-2-1024x683.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0152-1-2-768x512.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0152-1-2.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Gwamna Badaru ya bayyana cewa kungiyar na shirin ganawa da shugabannin addini\u2014ciki har da malaman Musulunci da na Kirista\u2014da kuma wasu fitattun &#8216;yan Najeriya domin yi musu bayani kan muhimmancin goyon bayan takarar Tinubu da Shettima a zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Mun yi nisa sosai wajen tattaunawa da manyan mutane. Mun riga mun gana da su sau da dama, kuma Kwamitin Amintattu (BoT) zai sake ganawa da su domin karfafa nasarorin da muka samu da kuma bayyana musu dalilin da ya sa ake bukatar goyon bayan wannan takara.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Haka kuma muna ba wa Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa (PCC) goyon baya kan duk wani aiki da suka bukaci mu yi\u2014musamman ayyuka na matakin kasa\u2014saboda su suna da babban nauyi a kansu kuma ba ma son mu manta da babban tsarin da ake da shi. Muna son mu mayar da hankali sosai kan hulda da mutane a matakin tushe wato a kananan hukumomi da mazabu,&#8221;<\/strong><\/em> in ji shi.<img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5981\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0148-696x464-2-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0148-696x464-2-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0148-696x464-2.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Haka kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar (BoT) kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa kungiyar masu nazari da tsare-tsare da ta yi aiki domin nasarar zaben Shugaba Tinubu a babban zaben 2023 za ta sake samun irin wannan nasarar a shekarar 2027.<\/p>\n<p>Shekarau ya ce,<em><strong> &#8220;kungiyar na ci gaba da ganawa da gwamnonin jihohin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin musayar ra&#8217;ayoyi da kuma hada kai kan hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da sake zaben Shugaban kasa.&#8221;<\/strong><\/em><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5982\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0155-1-696x464-2-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0155-1-696x464-2-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0155-1-696x464-2.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><br \/>\nYa bayyana cewa kungiyar ta kammala shirye-shiryen samar da cikakken sakatariya domin gudanar da ayyukan daidaitawa inda za a samar da ofisoshi ga daraktoci da masu kula da harkokin kungiyar a jihohi; wadannan za su rika nazari da kwatanta rahotanni tare da bayar da umarni ga mambobin kungiyar.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar Gudanarwa (BoT) ya gayyaci Mataimakin Shugaban Kasa a hukumance domin ya kaddamar da rukunin ofisoshin A4A a ranar Asabar 17 ga Oktoba 2027.<img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5983\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0145-1-696x464-1-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0145-1-696x464-1-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261012-WA0145-1-696x464-1.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Har ila yau taron ya samu halartar tsoffin gwamnonin jihohin Plateau wato Cif Joshua Dariye da Sanata Simon Lalong; Taraba Rev. Jolly Nyame; Kogi Alhaji Yahaya Bello; Katsina Barr. Ibrahim Shema; Bauchi Mallam Isa Yuguda; da kuma Babbar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-tsare da Daidaita Ayyuka Hajiya Hadiza Bala Usman. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), da wasu manyan jami&#8217;an gwamnati, tare da sauran mambobin kwamitin amintattu (BOT) da sakatariyar kungiyar A4A.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya yi kira ga mutanen Arewa da su goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027 inda ya ba su tabbacin cewa babu abin da ya kamata su ji tsoro game da wa&#8217;adin mulki na biyu na Shugaban. Ya bukaci shugabanni da al&#8217;ummar Arewa da su hada kai &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5967,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-5964","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5964","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5964"}],"version-history":[{"count":5,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5964\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5989,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5964\/revisions\/5989"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5967"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5964"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5964"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5964"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}