{"id":5921,"date":"2026-10-13T10:40:05","date_gmt":"2026-10-13T10:40:05","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5921"},"modified":"2026-10-13T10:40:05","modified_gmt":"2026-10-13T10:40:05","slug":"yan-majalisar-dokokin-greenland-sun-goyi-bayan-yarjejeniyar-tsaro-da-amurka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/13\/yan-majalisar-dokokin-greenland-sun-goyi-bayan-yarjejeniyar-tsaro-da-amurka\/","title":{"rendered":"&#8216;Yan majalisar Dokokin Greenland Sun Goyi Bayan Yarjejeniyar Tsaro Da Amurka."},"content":{"rendered":"<p><strong>Yawancin &#8216;yan majalisar dokokin Greenland sun nuna goyon bayansu ga yarjejeniyar tsaro da aka kulla kwanan nan tsakanin wannan tsibiri na yankin Arctic da Shugaban Amurka Donald Trump yayin wata muhawara a majalisar.<\/strong><\/p>\n<p>Amurka Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan da ya gabata domin rage tashin hankali bayan barazanar da Shugaba Trump ya rika yi akai-akai na son mallakar tsibirin, wanda ke da muhimmancin dabarun soja da kuma arzikin ma&#8217;adanai.<\/p>\n<p>Yarjejeniyar na bukatar a sake duba ta a karo na biyu a majalisa kafin a kada kuri&#8217;a a kanta\u00a0 inda ake sa ran &#8216;yan majalisar za su amince da dokar.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Shugaba Trump na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar soja ta Greenland<\/p>\n<p>Yarjejeniyar na fadada rawar da sojojin Amurka ke takawa a Greenland, inda za ta ba da damar kafa sabbin sansanonin soja guda biyu da kuma tsarin kare kai daga makamai masu linzami na Shugaba Trump mai suna <em><strong>&#8220;Golden Dome,&#8221;<\/strong> <\/em>tare da tabbatar da ikon mallakar kasar Denmark da kuma &#8216;yancin al&#8217;ummar Greenland na yanke hukunci kan makomarsu.<\/p>\n<p>Sai dai shugaban jam&#8217;iyyar adawa ta Naleraq, Pele Broberg ya bayyana cewa akwai cikakkun bayanai da dama da ba su da tabbas game da yadda yarjejeniyar za ta yi aiki a zahiri.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;An bai wa Amurka manyan hakkoki a kasarmu. Ba a bai wa al&#8217;ummar Greenland garantin samun takamaiman biyan kudi ba don wadannan hakkoki,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Broberg yayin muhawarar majalisar a birnin Nuuk, babban birnin Greenland.<\/p>\n<p>Jam&#8217;iyyun da ke mulki wadanda ke da rinjayen kujeru a majalisa sun kare yarjejeniyar.<\/p>\n<p>Tsohuwar Ministar Harkokin Waje Vivian Motzfeldt daga jam&#8217;iyyar Demokraatit da ke cikin kawancen masu mulki\u00a0 ta jaddada cewa Greenland ta samu kariya mai karfi ba tare da ta biya komai ba, tare da samun karbuwa a matsayin kasa mai cin gashin kanta.<\/p>\n<p>Ministan Harkokin Waje Mute Egede ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba wanda ba za a iya auna shi da kudi ba.<\/p>\n<p>Shugaban jam&#8217;iyyar Siumut Erik Jensen shi ma ya tabbatar da goyon bayan jam&#8217;iyyarsa ga yarjejeniyar.<\/p>\n<p><strong>&#8220;Tsawon shekaru da dama Siumut ta yi ta yakin neman ganin cewa ba a sake kulla yarjejeniyoyi game da Greenland ba tare da sa hannun Greenland ba&#8230; Shi ya sa<\/strong> muke<strong> gamsuwa,&#8221;<\/strong> in ji Jensen.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Reuters\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yawancin &#8216;yan majalisar dokokin Greenland sun nuna goyon bayansu ga yarjejeniyar tsaro da aka kulla kwanan nan tsakanin wannan tsibiri na yankin Arctic da Shugaban Amurka Donald Trump yayin wata muhawara a majalisar. Amurka Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan da ya gabata domin rage tashin hankali bayan barazanar da Shugaba &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5924,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40,39],"tags":[],"class_list":["post-5921","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5921","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5921"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5921\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5925,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5921\/revisions\/5925"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5924"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5921"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5921"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5921"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}