{"id":5910,"date":"2026-10-12T10:23:48","date_gmt":"2026-10-12T10:23:48","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5910"},"modified":"2026-10-12T10:23:48","modified_gmt":"2026-10-12T10:23:48","slug":"mutane-139-masu-kaura-sun-mutu-bayan-jirgin-ruwansu-ya-kife-a-kusa-da-djibouti","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/12\/mutane-139-masu-kaura-sun-mutu-bayan-jirgin-ruwansu-ya-kife-a-kusa-da-djibouti\/","title":{"rendered":"Mutane 139 Masu Kaura Sun Mutu Bayan Jirgin Ruwansu Ya Kife  A Kusa Da Djibouti."},"content":{"rendered":"<p><strong>Mutane akalla 139 ciki har da yara 15 sun mutu bayan wani jirgin ruwa na masu hijira ya kife a daren da Ta gabata a gabar tekun Djibouti yayin da suke kan hanyar zuwa Yemen.<\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa mutane 82 wadanda dukkaninsu &#8216;yan kasar Habasha ne sun tsira yayin da wasu mutane 84 kuma har yanzu ba a san inda suke ba.<\/p>\n<p>Safiya Ibrahim mai kula da ayyukan agaji a hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce jirgin ya kife ne a kusa da garin tashar jiragen ruwa na Obock.<\/p>\n<p><em>&#8220;<strong>A cikin jirgin akwai mata da maza, har ma da yara. Adadin wadanda suka mutu ya yi yawa sosai,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji ta.<\/p>\n<p>&#8220;<em><strong>Wadanda suka tsira sun gaya min cewa jirgin ya fara nutsewa ta baya ne da zarar sun shiga cikinsa,&#8221;<\/strong><\/em> in ji shugaban ayyukan IOM a Djibouti Alexandre Coissac.<\/p>\n<p>Coissac ya ce: <em><strong>&#8220;Muna tare da wadanda suka tsira da kuma iyalan da suka rasa masoyansu ko kuma wadanda har yanzu ba su samu labarin &#8216;yan uwansu ba.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>An ga wasu kayayyaki na sirri wadanda ake kyautata zaton na mutanen da ke cikin jirgin ne a bakin teku yayin da ake ci gaba da ayyukan neman wadanda suka bata da kuma ceto.<\/p>\n<p>IOM ta ce tana ba da tallafi ga wadanda suka tsira ciki har da kula da lafiyarsu da kuma taimaka musu wajen tuntu\u0253ar iyalansu.<\/p>\n<p>Coissac ya ce wannan bala&#8217;i <em><strong>&#8220;jan hankali ne mai karfi&#8221;<\/strong> <\/em>game da hadarin da masu hijira ke fuskanta yayin neman sabuwar rayuwa a wasu wurare.<\/p>\n<p>Ya ce daya daga cikin wadanda suka tsira ya gaya masa cewa sun fito ne daga yankin Tigray na arewacin Habasha inda &#8216;yan tawaye ke gwabzawa da gwamnatin tarayya sakamakon sake barkewar rikici a baya-bayan nan.<\/p>\n<p>Har yanzu kasar Yemen na fama da mummunan yakin basasa, amma duk da wannan rikici da kuma karuwar rashin kwanciyar hankali a yankin baki daya, masu hijira na ci gaba da ketare mashigin ruwa na Bab el-Mandeb.<\/p>\n<p>Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban masu hijira daga yankin Kahon Afirka (Horn of Africa) ne ke yin wannan tafiya mai hadari a kowace shekara, da fatan isa kasashen Gulf domin samun tsaro da kuma aiki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Labaran Afirka\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mutane akalla 139 ciki har da yara 15 sun mutu bayan wani jirgin ruwa na masu hijira ya kife a daren da Ta gabata a gabar tekun Djibouti yayin da suke kan hanyar zuwa Yemen. Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa mutane 82 wadanda dukkaninsu &#8216;yan kasar Habasha ne sun &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5913,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-5910","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5910","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5910"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5910\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5915,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5910\/revisions\/5915"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5913"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5910"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5910"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5910"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}