{"id":5877,"date":"2026-10-12T07:19:42","date_gmt":"2026-10-12T07:19:42","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5877"},"modified":"2026-10-12T07:19:42","modified_gmt":"2026-10-12T07:19:42","slug":"inec-ta-sanya-sunan-adamu-a-matsayin-dan-takarar-gwamna-na-jamiyyar-sdp-a-jihar-nasarawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/12\/inec-ta-sanya-sunan-adamu-a-matsayin-dan-takarar-gwamna-na-jamiyyar-sdp-a-jihar-nasarawa\/","title":{"rendered":"INEC Ta Sanya Sunan Adamu A Matsayin Dan Takarar Gwamna Na Jam&#8217;iyyar SDP A Jihar Nasarawa."},"content":{"rendered":"<p><strong>Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya sunan tsohon Sufeto-Janar na &#8216;Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, a matsayin dan takarar gwamna na jam&#8217;iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Nasarawa.<\/strong><\/p>\n<p>Kungiyar yakin neman zaben Adamu ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na zamani da sadarwa na kungiyar Otaru Douglas, ya sanya wa hannu a Lafia babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Kungiyar ta bayyana sanya sunan a matsayin tabbacin takarar Adamu, inda ta ce hakan ya kawo karshen rade-radi da ce-ce-ku-ce game da wanda zai wakilci jam&#8217;iyyar a zaben gwamna mai zuwa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: APC ta lashe zaben cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa<\/p>\n<p>Ta ce wannan ci gaba ba zai hana kungiyar ci gaba da tuntubar masu kada kuri&#8217;a a kan shirye-shiryen da ta tsara ba a kananan hukumomi 13 na jihar.<\/p>\n<p>A cewar sanarwar, muhimman abubuwan da kungiyar ta sa a gaba sun hada da inganta tsaro samar da ayyukan yi karfafa gwiwar matasa da mata da kuma inganta shugabanci mai mayar da hankali kan bukatun al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Kungiyar ta taya Adamu shugabancin jam&#8217;iyyar SDP na kasa da na jiha da kuma magoya bayan jam&#8217;iyyar murna kan wannan ci gaba tare da yaba wa jajircewarsu wajen yakin neman zaben.<\/p>\n<p>Haka kuma ta yi kira ga mazauna jihar da sauran magoya baya da su shiga wannan tafiya, inda ta bayyana kwarin gwiwarta kan shirye-shiryen da jam&#8217;iyyar ta yi domin zaben mai zuwa.<\/p>\n<p>Sai dai sanarwar ba ta bayar da karin bayani game da sanarwar ta INEC ko kuma takamaiman tsarin da hukumar ta bi wajen sanya sunan Adamu a matsayin dan takarar jam&#8217;iyyar ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya sunan tsohon Sufeto-Janar na &#8216;Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, a matsayin dan takarar gwamna na jam&#8217;iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Nasarawa. Kungiyar yakin neman zaben Adamu ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na zamani da sadarwa na &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5880,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-5877","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5877","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5877"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5877\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5882,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5877\/revisions\/5882"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5880"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5877"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5877"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5877"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}