{"id":5849,"date":"2026-10-12T06:25:05","date_gmt":"2026-10-12T06:25:05","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5849"},"modified":"2026-10-12T06:25:05","modified_gmt":"2026-10-12T06:25:05","slug":"shugaban-masar-ya-kammala-ziyarar-da-ya-kai-malaysia-inda-suka-tattauna-kan-rikicin-gabas-ta-tsakiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/12\/shugaban-masar-ya-kammala-ziyarar-da-ya-kai-malaysia-inda-suka-tattauna-kan-rikicin-gabas-ta-tsakiya\/","title":{"rendered":"Shugaban Masar Ya Kammala Ziyarar Da Ya Kai Malaysia Inda Suka Tattauna Kan Rikicin Gabas Ta Tsakiya."},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi ya kammala ziyarar aiki ta kwana biyu a kasar Malaysia ziyarar farko da wani shugaban kasar Masar ya kai kasar cikin kusan shekaru talatin.<\/strong><\/p>\n<p>Shi da Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim sun tattauna kan bukatar cimma matsaya ta siyasa domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.<\/p>\n<p>Dukkansu sun yi Allah-wadai da ayyukan sojin Isra&#8217;ila a Gaza tare da tattauna batutuwan da suka shafi yankin baki daya ciki har da tashin hankalin da ke faruwa a yankin Mashigar Ruwa ta Hormuz.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Na kuma tattauna da Firayim Minista game da halin da ake ciki a yankin Kahon Afirka da kuma Tekun Jan Ruwa (Red Sea). Na jaddada muhimmancin cimma matsaya ta siyasa mai dorewa da ta shafi dukkan bangarori, a matsayin hanyar da za ta kawo karshen dukkan rikice-rikicen yankin,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji Al-Sisi.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Jamus za ta dakatar da samar da makamai ga Isra&#8217;ila yayin da ake fama da yunwa a Gaza<\/p>\n<p>Shugabannin biyu sun sake jaddada goyon bayansu ga tsarin samar da kasashe biyu domin warware rikicin Isra&#8217;ila da Falasdinu bisa iyakokin shekarar 1967 tare da sanya Gabashin Kudus a matsayin babban birni.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Mun dauki matsayi mai karfi dangane da munanan ayyukan da ake tafkawa kan al&#8217;ummar Falasdinu da Gaza sakamakon taurin kai da tashin hankalin da Isra&#8217;ila ke haifarwa,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Ibrahim.<\/p>\n<p>Sun kuma tattauna batun karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma fadada hadin gwiwar tattalin arziki a tsakaninsu.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Hakika, Masar kasa ce mai matukar muhimmanci a duniyar Larabawa da kuma nahiyar Afirka.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Saboda haka, hadin gwiwa da Masar zai bai wa Malaysia babbar dama da rawar da za ta taka wajen fadada kasuwanci da zuba jari, da harkokin yawon bude ido, da sauran fannoni daban-daban,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Ibrahim.<\/p>\n<p>Sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda hudu da suka shafi karfafa gwiwar mata, ilimin gaba da sakandare, yawon bude ido, da kuma zuba jari.<\/p>\n<p>Masar ce kasa ta bakwai mafi girma wajen hada-hadar kasuwanci da Malaysia a nahiyar Afirka a shekarar 2025, inda darajar kasuwancin tsakanin kasashen biyu ta kai dalar Amurka miliyan 720.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar Harkokin Wajen Malaysia ta bayyana cewa, kasuwancin ya karu da kashi 74.7 cikin dari zuwa dalar Amurka miliyan 870 a tsakanin watan Janairu da Agusta na shekarar 2026.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Africanews\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi ya kammala ziyarar aiki ta kwana biyu a kasar Malaysia ziyarar farko da wani shugaban kasar Masar ya kai kasar cikin kusan shekaru talatin. Shi da Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim sun tattauna kan bukatar cimma matsaya ta siyasa domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya. Dukkansu sun yi Allah-wadai da ayyukan &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5852,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-5849","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5849","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5849"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5849\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5853,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5849\/revisions\/5853"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5852"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5849"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5849"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5849"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}