{"id":5762,"date":"2026-10-11T09:56:53","date_gmt":"2026-10-11T09:56:53","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5762"},"modified":"2026-10-11T09:56:53","modified_gmt":"2026-10-11T09:56:53","slug":"uwargidan-shugaban-kasa-ta-tabbatar-wa-yan-najeriya-game-da-alkawarin-shugaba-tinubu-na-kawo-sauyi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/11\/uwargidan-shugaban-kasa-ta-tabbatar-wa-yan-najeriya-game-da-alkawarin-shugaba-tinubu-na-kawo-sauyi\/","title":{"rendered":"Uwargidan Shugaban Kasa Ta Tabbatar Wa &#8216;Yan Najeriya Game Da Alkawarin Shugaba Tinubu Na Kawo Sauyi."},"content":{"rendered":"<p><strong>Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta bai wa &#8216;yan Najeriya tabbacin cewa Shugaba Bola Tinubu zai cika alkawarin da ya yi a sakonsa na Ranar &#8216;Yancin Kai na sauya fasalin kasar idan aka sake zabensa domin wa&#8217;adi na biyu a shekara mai zuwa<\/strong>.<\/p>\n<p>Ta bayyana hakan ne a birnin Lafia na jihar Nasarawa yayin babban taron kungiyar &#8216;North-Central Grassroots Mobilisation Network&#8217; na yakin neman sake zaben Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5769 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-2-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"333\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-2-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-2-1024x682.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-2-768x511.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-2.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>Taron gangamin wanda ya samu halartar dimbin magoya bayan jam&#8217;iyyar daga sassan yankin Arewa ta Tsakiya ya kuma samu halartar manyan shugabannin jam&#8217;iyyar ciki har da Shugaban Jam&#8217;iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda da Sanata Hope Uzidinma (Gwamnan Jihar Imo) da sauran gwamnonin yankin.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5768 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-3-300x197.jpg\" alt=\"\" width=\"499\" height=\"328\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-3-300x197.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-3-1024x673.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-3-768x505.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-3.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 499px) 100vw, 499px\" \/><\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaban Najeriya Ta Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zaben Mata Na Tinubu<\/p>\n<p>Uwargidan Shugaban kasar ta ce: \u201c<em>Shugaba Tinubu mutum ne mai imani da hadin kai tsaro da kuma ci gaban kasarmu.<\/em><\/p>\n<p>\u201c<em>Taken sakon Shugaban kasa na Ranar \u2018Yancin Kai shi ne \u2018Daga Gyare-gyare zuwa Wadata\u2019 saboda haka Shugaban kasa yana nuna cewa za su yi gyare-gyare a bangarori daban-daban amma yanzu lokacin samun wadata ne kuma muna ganin yadda tattalin arzikinmu ke samun kwanciyar hankali.<\/em><\/p>\n<p><em>\u201cFarashin musayar kudaden kasashen waje yana raguwa, kuma masu zuba jari suna dawowa Najeriya. Game da manomanmu ma kuma za ku iya ganin dukkan Gwamnoninmu a nan suna gudanar da ayyukan raya ababen more rayuwa irin wanda ba a taba gani a baya ba<\/em>.\u201d<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5767 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-4-300x173.jpg\" alt=\"\" width=\"499\" height=\"288\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-4-300x173.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-4-1024x590.jpg 1024w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-4-768x442.jpg 768w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-4.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 499px) 100vw, 499px\" \/><\/p>\n<p><strong>Abinci<\/strong><br \/>\nMadam Tinubu ta kara da cewa gwamnatin mai ci tana kuma daukar matakai masu karfi wajen magance matsalar karancin abinci mai gina jiki.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Kamar yadda kuke gani yanzu, mun kammala shirin samar da abinci inda muke tallafawa kowane yaro da kuma mata masu juna biyu da masu shayarwa.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Wannan na da nufin tabbatar da cewa sun samu abinci mai gina jiki sosai tare da bai wa yaran da ke fama da rashin isasshen abinci mai gina jiki damar samun kulawa da abincin da zai sa su girma cikin koshin lafiya. Ba ma wannan kadai ba matasanmu da ke makaranta suna samun tallafin da ya dace.<\/em><\/p>\n<p>&#8220;<em>Abu daya da nake son fada shi ne yayin da muke komawa jihohinmu daban-daban ku gaya wa kowa cewa Shugaban kasa jagora ne mai matukar jajirtattun dabi&#8217;u. Kamar yadda muke gani ba ya shakkar daukar matakai masu wahala kuma shi jagora ne da za a iya dogara da shi wajen kai mu ga ci gaba da wadata<\/em>&#8221; cewar Uwargidan Shugaban kasa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5766 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-5-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"333\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-5-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-5.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>Ta bukaci al&#8217;ummar yankin Arewa ta Tsakiya da su tabbatar sun sanar da mutane cewa al&#8217;amura za su inganta matuka idan aka sake zabar Tinubu da Shettima.<\/p>\n<p><strong>Gina Tattalin Arziki Mai Manufa<\/strong><br \/>\nTa bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta gina tattalin arziki mai karfi da al&#8217;ummomi masu tsaro da kuma Najeriya mai ci gaba da daukaka.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5765 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-6-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"333\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-6-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/mata-6.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>&#8220;<em>Saboda haka ku zabi ci gaba ku zabi kwarewa ku zabi wadata ku kuma zabi sake zabar Shugaban Kasa da dukkan &#8216;yan takarar jam&#8217;iyyar APC daga sama har kasa<\/em>&#8221; in ji ta.<\/p>\n<p>Sauran masu jawabi a wurin taron sun kuma bayyana cewa zabar Shugaba Bola Tinubu da jam&#8217;iyyar APC a babban zaben shekarar 2027 zai haifar da babbar nasara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta bai wa &#8216;yan Najeriya tabbacin cewa Shugaba Bola Tinubu zai cika alkawarin da ya yi a sakonsa na Ranar &#8216;Yancin Kai na sauya fasalin kasar idan aka sake zabensa domin wa&#8217;adi na biyu a shekara mai zuwa. Ta bayyana hakan ne a birnin Lafia na jihar Nasarawa yayin babban &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":5770,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-5762","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5762","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5762"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5762\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5771,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5762\/revisions\/5771"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5770"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5762"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5762"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5762"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}