{"id":5738,"date":"2026-10-10T15:35:07","date_gmt":"2026-10-10T15:35:07","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5738"},"modified":"2026-10-10T15:35:07","modified_gmt":"2026-10-10T15:35:07","slug":"gwamnonin-yankin-arewa-ta-tsakiya-sun-goyi-bayan-shirin-shugaba-tinubu-na-sake-tsayawa-takara-a-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/10\/gwamnonin-yankin-arewa-ta-tsakiya-sun-goyi-bayan-shirin-shugaba-tinubu-na-sake-tsayawa-takara-a-2027\/","title":{"rendered":"Gwamnonin Yankin Arewa Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Shirin Shugaba Tinubu Na Sake Tsayawa Takara A 2027"},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamnonin yankin Arewa ta Tsakiya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake samun wa&#8217;adin mulki na biyu yayin babban taron jam&#8217;iyyar APC da aka gudanar a filin Lafia Square da ke jihar Nasarawa.<\/strong><\/p>\n<p>A jawabinsa na maraba Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa jihar za ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam&#8217;iyyar APC da sauran &#8216;yan takarar jam&#8217;iyyar a babban zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Sule ya nuna kwarin gwiwa kan nasarar da jam&#8217;iyyar za ta iya samu a zabe tare da sake jaddada aniyar jihar Nasarawa na ci gaba da goyon bayan APC da &#8216;yan takararta.<\/p>\n<p>Gwamnonin jihohin Benue Plateau Kwara Kogi Niger da Nasarawa suma sun bayyana goyon bayansu ga yunkurin Tinubu na sake tsayawa takara inda suka yi nuni da sauye-sauyen da aka samu a fannin tattalin arziki da sauran bangarori a karkashin gwamnatinsa.<\/p>\n<p>Da take jawabi a wajen taron Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kwarin gwiwar cewa matsalolin tattalin arziki da &#8216;yan Najeriya ke fuskanta za su ragu tare da fatan samun ingantacciyar rayuwa idan Shugaban ya samu wa&#8217;adin mulki na biyu.<\/p>\n<p>Ta yi karin haske kan wasu shirye-shiryen gwamnatin a fannonin kiwon lafiya gina hanyoyi da ilimi ciki har da shirin bayar da rancen kudi ga dalibai da aka tsara domin bai wa karin dalibai damar samun ilimi mai zurfi.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5741 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/re-e-2-300x169.jpeg\" alt=\"\" width=\"499\" height=\"281\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/re-e-2-300x169.jpeg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/re-e-2-390x220.jpeg 390w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/re-e-2.jpeg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 499px) 100vw, 499px\" \/><\/p>\n<p>Uwargidan Shugaban Kasa ta bayyana cewa samun wa&#8217;adi na biyu ga Tinubu zai ba da damar ci gaba da aiwatar da shirin gwamnati na\u00a0 &#8221;<em>Sabon Fatan Rayuwa&#8217;<\/em>&#8216; tare da magance wasu daga cikin kalubalen da &#8216;yan Najeriya ke fuskanta.<\/p>\n<p>Wannan jawabi nata na cikin kokarin jam&#8217;iyyar APC na tara goyon baya ga Shugaban Kasa da sauran &#8216;yan takarar jam&#8217;iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar shugabannin jam&#8217;iyya masu ruwa da tsaki, magoya baya, da kuma abokan huldar siyasa daga sassan yankin Arewa ta Tsakiya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnonin yankin Arewa ta Tsakiya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake samun wa&#8217;adin mulki na biyu yayin babban taron jam&#8217;iyyar APC da aka gudanar a filin Lafia Square da ke jihar Nasarawa. A jawabinsa na maraba Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa jihar za ta goyi bayan dan &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":5742,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-5738","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5738","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5738"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5738\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5744,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5738\/revisions\/5744"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5742"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5738"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5738"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5738"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}