{"id":5338,"date":"2026-10-06T10:03:28","date_gmt":"2026-10-06T10:03:28","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5338"},"modified":"2026-10-06T10:03:28","modified_gmt":"2026-10-06T10:03:28","slug":"shugaba-tinubu-ya-ayyana-zaman-makokin-kasa-saboda-jamian-rundunar-sojin-sama","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/06\/shugaba-tinubu-ya-ayyana-zaman-makokin-kasa-saboda-jamian-rundunar-sojin-sama\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Ayyana Zaman Makokin Kasa Saboda Jami&#8217;an Rundunar Sojin Sama"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana zaman makokin kasa na kwana uku domin juyayin rasuwar jami&#8217;an Rundunar Sojin Sama da suka mutu a hatsarin jirgin saman soja da ya faru a ranar Litinin<\/strong>.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a rage tutoci zuwa rabin sanda a fadin kasar nan domin nuna girmamawa ga wadannan jami&#8217;ai.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa game da hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya kirar ATR-42.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan hatsarin jirgin NAF a Ondo<\/p>\n<p>Hatsarin ya faru ne kusa da sansanin sojin ruwa a yankin Igbokoda na Jihar Ondo. Jirgin wanda ke dauke da fasinjoji 25 da ma&#8217;aikatan jirgi bakwai yana kan aikin yau da kullum daga Benin zuwa Legas ne lokacin da hatsarin ya faru.<\/p>\n<p><em>&#8220;Wannan lokaci ne mai cike da radadi ga Rundunar Sojinmu da kuma kasa baki daya. Jami&#8217;an Rundunar Sojin Samanmu suna sadaukar da rayuwarsu a kowace rana domin kare Najeriya. Ba za a taba mantawa da irin sadaukarwar da suka yi ba&#8221;<\/em> in ji Shugaba Tinubu a cikin sakon ta&#8217;aziyya ga Babban Hafsan Sojin Sama Air Marshal Sunday Aneke da dukkan jami&#8217;ai da sauran ma&#8217;aikatan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.<\/p>\n<p>Ya ce<em>: \u201cKwamandan Rundunar Sojin Sama ya yi min bayani kuma na umurci Rundunar Sojin Saman Najeriya da ta fara gudanar da cikakken bincike nan take kan musabbabin hatsarin domin hana sake faruwar hakan a nan gaba.<\/em><\/p>\n<p><em>\u201cIna yaba wa Rundunar Sojin Saman Najeriya bisa daukar matakin fara aikin neman wadanda hatsarin ya shafa da ceto su nan take bayan faruwar lamarin.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Rundunar Sojin Saman za ta bayyana sunayen jami\u2019an bayan ta tuntubi iyalansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>LADAN NASIDI.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana zaman makokin kasa na kwana uku domin juyayin rasuwar jami&#8217;an Rundunar Sojin Sama da suka mutu a hatsarin jirgin saman soja da ya faru a ranar Litinin. A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5341,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[49,39],"tags":[],"class_list":["post-5338","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5338","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5338"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5338\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5343,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5338\/revisions\/5343"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5341"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5338"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5338"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5338"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}