{"id":5254,"date":"2026-10-05T06:30:42","date_gmt":"2026-10-05T06:30:42","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5254"},"modified":"2026-10-05T06:30:42","modified_gmt":"2026-10-05T06:30:42","slug":"gwamnatin-najeriya-za-ta-kaddamar-da-shirin-kayayyakin-lantarki-a-arewa-maso-gabas-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/05\/gwamnatin-najeriya-za-ta-kaddamar-da-shirin-kayayyakin-lantarki-a-arewa-maso-gabas-2\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Najeriya Za Ta Kaddamar Da Shirin Kayayyakin Lantarki A Arewa Maso Gabas"},"content":{"rendered":"<p><strong>Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ce Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da wani shirin samar da kekunan lantarki a Arewa maso Gabas a cikin makonni masu zuwa tare da tura kekuna 10,600 na lantarki tare da motocin bas 300 da taksi na lantarki don rage radadin tattalin arziki a yankin.<\/strong><\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasa Shettima wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar da tagaba yayin da yake magana da manema labarai bayan ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Ikoyi a Legas, ya ce gwamnati na aiwatar da shirye-shirye da ayyuka da nufin inganta yanayin rayuwar &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Gwamnati na aiwatar da shirye-shirye da ayyuka don rage radadin mutanenmu. A cikin makonni biyu masu zuwa, za mu kaddamar da kekunan lantarki a Arewa maso Gabas, za mu gudanar da kekunan lantarki 10,600 don rage radadin mutanen Arewa maso Gabas, da kuma motocin bas da taksi 300, taksi na lantarki. Duk wadannan an yi su ne don rage radadin da mutanenmu ke ciki.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>\u201cMuna sane da wahalhalun da \u2018yan Najeriya ke ciki, amma lokutan wahala ba sa dawwama har abada. Mutane masu juriya ne kawai ke dawwama,\u201d<\/strong> <\/em>in ji Mataimakin Shugaban Kasa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5258\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261003-WA0223-768x409-1-300x160.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"160\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261003-WA0223-768x409-1-300x160.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261003-WA0223-768x409-1.jpg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasa ya yaba da dawowar Shugaba Tinubu gida Najeriya, inda ya bayyana cewa ya ci gaba da tattaunawa akai-akai da shugaban kasar a duk tsawon lokacin da ya yi a kasashen waje tare da musayar bayanai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Gwamnan Gombe ya bukaci shugabannin Arewa maso Gabas su samar da sakamako mai kyau<\/p>\n<p>Shettima ya ce ci gaban kimiyya da fasaha ya bai wa Shugaban damar ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yayin da yake waje, inda ya kara da cewa dawowarsa za ta kara ba da muhimmanci ga matakai da shirye-shiryen da ke da nufin inganta rayuwar &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p>Ya kuma kare matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatin ta dauka, inda ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya gaji matsanancin yanayi na tattalin arziki kuma ya dauki matakai masu wuyar gaske\u2014ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kudaden waje daban-daban\u2014domin magance lamarin.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Matakan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kudaden waje matakai ne masu matukar muhimmanci da tasiri. A zahiri, tattalin arzikin kasar na gab da rugujewa, amma ya ceto shi. Ina so &#8216;yan Najeriya su fahimci wannan muhimmiyar gaskiya. Muna kan hanyar da za ta kai mu ga halin da Caracas (Venezuela) ta tsinci kanta a ciki. Ya ceto tattalin arzikinmu. Ya ceto kasar daga rugujewa,&#8221;<\/strong><\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bayyana cewa Shugaban yana sane da kalubalen da talakawan Najeriya ke fuskanta kuma zai ci gaba da samar da matakan tallafi domin rage radadin da gyare-gyaren tattalin arzikin ke haifarwa.<\/p>\n<p>Ya ambaci Asusun Ba da Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) a matsayin daya daga cikin matakan tallafi da gwamnatin ta samar domin bai wa daliban da ba su da karfin kudi damar samun ilimi.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Shugaban yana da matukar tausayi da damuwa game da rayuwar talaka. Shirin NELFUND babban mataki ne da aka dauka domin taimaka wa daliban da ba su da karfin kudi su samu damar samun ilimi mai inganci. Don haka, ku kwantar da hankalinku, za mu ci gaba da samar da shirye-shirye da ayyukan da za su rage radadin da jama&#8217;a ke ciki. Ko da yake ana ta maganar siyasa a yanzu, za mu ci gaba da tafiyar da siyasa tare da gudanar da ayyukan gwamnati,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Mataimakin Shugaban Kasar.<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Kasar ya ce duk da cewa harkokin siyasa na kara karfi a kasar, gwamnatin za ta ci gaba da hada siyasa da gudanar da ayyukan gwamnati tare da mayar da hankali kan shirye-shiryen da suka shafi rayuwar &#8216;yan Najeriya kai tsaye. Shugaba Tinubu ya kuma kar\u0253i bakuncin Ministan Raya Ma&#8217;adanai, Dele Alake, da Shugaban Kwamitin Edita na jaridar The Nation, Sam Omatseye, a gidansa da ke Ikoyi a birnin Lagos, gabanin \u0199addamar da littafin Omatseye mai taken From AD to APC: The Evolution of Political Parties and the Exploits of One Man.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ce Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da wani shirin samar da kekunan lantarki a Arewa maso Gabas a cikin makonni masu zuwa tare da tura kekuna 10,600 na lantarki tare da motocin bas 300 da taksi na lantarki don rage radadin tattalin arziki a yankin. Mataimakin Shugaban Kasa Shettima &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":5257,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-5254","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5254"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5261,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions\/5261"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5257"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5254"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5254"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5254"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}