{"id":5114,"date":"2026-10-03T12:10:20","date_gmt":"2026-10-03T12:10:20","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5114"},"modified":"2026-10-03T12:10:20","modified_gmt":"2026-10-03T12:10:20","slug":"tsohon-mataimakin-saraki-ya-kai-ziyara-ga-gwamna-abdulrazaq-a-tsakiyar-canjin-siyasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/03\/tsohon-mataimakin-saraki-ya-kai-ziyara-ga-gwamna-abdulrazaq-a-tsakiyar-canjin-siyasa\/","title":{"rendered":"Tsohon Mataimakin Saraki Ya Kai Ziyara Ga Gwamna AbdulRazaq A Tsakiyar Canjin Siyasa"},"content":{"rendered":"<p><strong>Tsohon Darakta-Janar na Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki Dr. Audu Musa Idowu ya ziyarci Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq a ranar Juma&#8217;a a gidan Ahmadu Bello da ke Ilorin bayan da ya yi murabus daga jam&#8217;iyyar\u00a0 PDP kwanan nan.<\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan ya karbi bakuncin Idowu a yayin wannan ziyara ta girmamawa inda wasu masu ruwa da tsaki a fagen siyasa suka raka shi.<\/p>\n<p>An gudanar da taron ne tare da halartar Shugaban jam&#8217;iyyar\u00a0 APC na Jihar Kwara Prince Sunday Adeniran Fagbemi dan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazabar Ekiti Abolarin Ganiyu Gabriel da sauran mambobin jam&#8217;iyya da masu ruwa da tsaki a siyasa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5119 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-2-300x164.jpg\" alt=\"\" width=\"499\" height=\"273\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-2-300x164.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-2.jpg 696w\" sizes=\"auto, (max-width: 499px) 100vw, 499px\" \/><\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Kwamitin Sulhu Na APC Na Jihar Kwara Ya Mika Rahotonsa<\/p>\n<p>Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanai game da tattaunawar ba ganawar ta ba wa Idowu da gwamnan damar musayar ra&#8217;ayoyi kan batutuwan da suka shafi moriyar juna.<\/p>\n<p>Wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a fagen siyasar Jihar Kwara inda &#8216;yan siyasa da kungiyoyi ke ci gaba da tattaunawa da sake tsara dabarunsu gabanin babban zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Huldar Idowu da Gwamna AbdulRazaq ta ja hankalin mutane saboda alakar da ya taba yi a baya da tsohon Gwamnan Jihar Kwara kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki.<\/p>\n<p>A baya ya rike mukamin Darakta-Janar na Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki kafin ya yi murabus daga jam&#8217;iyyar PDP kwanan nan.<\/p>\n<p>Saboda haka ganawarsa da Gwamna AbdulRazaq ta haifar da sha&#8217;awa a tsakanin masu sharhi kan harkokin siyasa musamman ganin yadda ake samun sauye-sauyen kawance da tsarin siyasa a jihar.<\/p>\n<p>Sai dai babu wata sanarwa ta hukuma daga ko dai Idowu ko gwamnan da ke nuna cewa ziyarar tana nufin sauya sheka zuwa wata jam&#8217;iyya kulla kawance ko kuma canza akidar siyasa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5118 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-3-300x205.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"342\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-3-300x205.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-3-220x150.jpg 220w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-3.jpg 614w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>Kasancewar shugaban jam&#8217;iyyar APC na jiha da sauran manyan jiga-jigan jam&#8217;iyyar a taron ya bayyana yanayin siyasa na wannan taro duk da cewa ba a sanar da wani takamaiman sakamako ba.<\/p>\n<p>Haka kuma taron ya zo ne a daidai lokacin da jam&#8217;iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar Kwara ke kara kaimi wajen gudanar da shawarwari tattara magoya baya da kuma shirye-shirye gabanin zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Matakin da Idowu ya dauka na ficewa daga jam&#8217;iyyar PDP kwanan nan ya kara sanya sauye-sauye a yanayin siyasar jihar inda ake sa ido sosai kan ayyukan manyan &#8216;yan siyasa yayin da lokacin zabe ke karatowa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-5117 alignnone\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-4-300x243.jpg\" alt=\"\" width=\"501\" height=\"406\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-4-300x243.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/KWARA-4.jpg 519w\" sizes=\"auto, (max-width: 501px) 100vw, 501px\" \/><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tsohon Darakta-Janar na Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki Dr. Audu Musa Idowu ya ziyarci Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq a ranar Juma&#8217;a a gidan Ahmadu Bello da ke Ilorin bayan da ya yi murabus daga jam&#8217;iyyar\u00a0 PDP kwanan nan. Gwamnan ya karbi bakuncin Idowu a yayin wannan ziyara ta girmamawa inda wasu masu ruwa da tsaki &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":5120,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-5114","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5114","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5114"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5114\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5122,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5114\/revisions\/5122"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5120"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5114"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5114"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5114"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}