{"id":5011,"date":"2026-10-02T09:32:12","date_gmt":"2026-10-02T09:32:12","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=5011"},"modified":"2026-10-02T09:54:27","modified_gmt":"2026-10-02T09:54:27","slug":"gwamnan-jihar-kwara-ya-yi-kira-ga-zaman-lafiya-da-hadin-kai-yayin-bikin-samun-yancin-kai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/02\/gwamnan-jihar-kwara-ya-yi-kira-ga-zaman-lafiya-da-hadin-kai-yayin-bikin-samun-yancin-kai\/","title":{"rendered":"Gwamnan Jihar Kwara Ya Yi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Yayin Bikin Samun &#8216;Yancin Kai"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira ga dukkan &#8216;yan Najeriya da su dauki Ranar Samun &#8216;Yancin Kai a matsayin lokacin yin nazari kan juriyarmu bambance-bambancen al&#8217;adu da kuma hadin kanmu a matsayin kasa daya tare da sabunta alkawarin gina kasar da muke burin samu.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Yayin jawabi a Ilorin a wajen bikin cika shekaru 66 da Najeriya ta samu &#8216;yancin kai Gwamnan ya yaba wa &#8216;yan kasa bisa jaruntaka kwazon kasuwanci kirkire-kirkire da kuma kudurin da suka nuna duk da kalubalen da ake fuskanta. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Yayin da yake taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan &#8216;yan kasa murnar wannan rana Gwamnan ya yi kira ga jama&#8217;a da su guji tashin hankali aikata laifuka da kalaman kiyayya tare da rungumar zaman lafiya da tsaron bai-daya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> KARANTA KUMA: Bikin Cika Shekaru 66: Malamin Addini Ya Yi Kira ga Hadin Kai da Gina Kasa<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\"> &#8220;A yau yayin da muke bikin cika shekaru 66 da samun &#8216;yancin kan Najeriya ina taya al&#8217;ummar Jihar Kwara da &#8216;yan Najeriya murna ko suna gida ko a kasashen waje&#8221; in ji shi.<\/span><\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> &#8220;<em>Ranar Samun &#8216;Yancin Kai lokaci ne na bikin nuna juriya bambance-bambancen al&#8217;adu da hadin kanmu tare da sabunta alkawarin gina Najeriya irin wacce muke burin samu.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> &#8220;<em>Duk da kalubalen da muke fuskanta &#8216;yan Najeriya na ci gaba da nuna jaruntaka kwazon kasuwanci kirkire-kirkire da kuduri wadanda su ne manyan dukiyoyin kasarmu.&#8221;<\/em><br \/>\n<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">AbdulRazaq ya yi amfani da damar wajen bayyana wasu daga cikin nasarorin gwamnatinsa da suka shafi rayuwar Jama\u2019a<span class=\"Apple-converted-space\">\u00a0 <\/span>musamman a fannonin ilimi noma kiwon lafiya da kuma gyaran birane. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da karfafa harkokin noma da inganta rayuwar manoma ta hanyar shirye-shirye irin su Kwara SAPZ L-PRES da sauran matakan tallafi wadanda suka samar da karin damammaki ga manoma sama da 100,000 tare da samar da cibiyoyin harkokin noma hanyoyin karkara da tallafin amfani da na&#8217;urorin zamani a harkar noma.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"><em> &#8220;A Kwara gwamnatinmu ta mayar da hankali kan inganta rayuwar jama&#8217;a. A fannin ilimi shirin KwaraLEARN ya horar da malamai dubbai ya samar da littattafan karatu da kayan aiki sama da miliyan 1.2 tare da gabatar da na&#8217;urorin zamani na dijital a makarantun firamare sama da 1,500<\/em>&#8221; in ji Gwamnan.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> &#8220;<em>Mun gina azuzuwa sama da 2,000, mun dauki malamai kusan 9,000 aiki mun kafa Jami&#8217;ar Ilimi ta Jihar Kwara (Kwara State University of Education) mun soke biyan kudaden gudummawar PTA a makarantun firamare na gwamnati, tare da dawo da damar samun tallafin hukumar UBEC.&#8221; <\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">\u201cA fannin kiwon lafiya a yanzu jihar Kwara ce ke da mafi karancin yawan mace-macen yara &#8216;yan kasa da shekaru biyar a Najeriya inda ake samun kimanin mace-mace 14 a cikin kowane haihuwa 1,000 na yara masu rai.<\/span>An gyara an samar da kayan aiki tare da sanya tsarin amfani da hasken rana a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 200 yayin da aka inganta Babban Asibitin Ilorin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami&#8217;ar Jihar Kwara.\u201d<\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kafin ya gabatar da jawabinsa Gwamnan ya duba jerin gwano na jami&#8217;an tsaro da kuma daliban makaranta da suka gudanar da jerin gwano na musamman.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai Mataimakin Gwamna Mista Kayode Alabi Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara kuma dan takarar gwamna na jam&#8217;iyyar APC Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi abokin takararsa Hon. Seun Oguniyi ADATO sauran &#8216;yan majalisar dokokin jihar mambobin majalisar zartarwa da kuma dalibai daga wasu zababbun makarantu.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Babban abin da ya dauki hankali a wajen taron shi ne yadda Gwamna ya yanka kek din bikin samun &#8216;yancin kai tare da rakiyar Mataimakin Gwamna Kakakin Majalisa da sauran manyan mutane.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira ga dukkan &#8216;yan Najeriya da su dauki Ranar Samun &#8216;Yancin Kai a matsayin lokacin yin nazari kan juriyarmu bambance-bambancen al&#8217;adu da kuma hadin kanmu a matsayin kasa daya tare da sabunta alkawarin gina kasar da muke burin samu. Yayin jawabi a Ilorin a wajen bikin cika shekaru &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5014,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-5011","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5011","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5011"}],"version-history":[{"count":5,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5011\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5018,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5011\/revisions\/5018"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5014"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5011"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5011"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5011"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}