{"id":4878,"date":"2026-10-01T09:20:20","date_gmt":"2026-10-01T09:20:20","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4878"},"modified":"2026-10-01T09:20:20","modified_gmt":"2026-10-01T09:20:20","slug":"uwargidan-shugaban-kasa-ta-yi-murnar-cikar-najeriya-shekaru-66","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/10\/01\/uwargidan-shugaban-kasa-ta-yi-murnar-cikar-najeriya-shekaru-66\/","title":{"rendered":"Uwargidan Shugaban Kasa Ta Yi Murnar Cikar Najeriya Shekaru 66"},"content":{"rendered":"<p><strong>Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta bayyana cewa kasar ta nuna karfin gwiwa da juriya tun bayan samun &#8216;yancin kai a ranar 1 ga Oktoba 1960.<\/strong><\/p>\n<p>Ta bayyana hakan ne a cikin sakon da ta aika wa &#8216;yan kasa domin taya murnar cika shekaru 66 da kasar ta samu &#8216;yancin kai.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Yayin da Najeriya ke cika shekaru 66 da samun &#8216;yancin kai muna bikin tafiya mai ban sha&#8217;awa ta kasa mai juriya tare da girmama sadaukarwar wadanda suka shimfida harsashin &#8216;yancinmu.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Tun bayan samun &#8216;yancin kai a shekarar 1960 mun shawo kan kalubale daban-daban mun rungumi sauyi kuma mun ci gaba da gina kasa mai karfi da wadata&#8221;<\/em> cewar mai dakin shugaban Kasa.<\/p>\n<p>Uwargidan Shugaban kasar ta yi kira ga &#8216;yan kasa da su ci gaba da zama lafiya da juna tare da guje wa tashin hankali ko duk wani abu da zai raba kan kasar.<\/p>\n<p><em>&#8220;Banbancin al&#8217;adunmu na daya daga cikin manyan dukiyoyinmu; dole ne mu ci gaba da bunkasa shi ta hanyar zaman lafiya hakuri tattaunawa, hadin kai da kaunar kasa. Kamar yadda Martin Luther King Jr. ya taba tunatar da mu &#8216;Kauna ita ce karfi mafi dorewa a duniya.&#8217;<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Allah ya sa mu ci gaba da zabar kauna maimakon rarrabuwa, zaman lafiya maimakon rikici da fata maimakon yanke kauna yayin da muke hada karfi da karfe wajen cimma burinmu na ganin Najeriya ta yadda muke fata.<\/em><\/p>\n<p>&#8220;<em>Ina addu&#8217;ar Allah Madaukakin Sarki Ya albarkaci Najeriya, Ya kare al&#8217;ummarmu Ya karfafa hadin kanmu Ya shiryar da shugabanninmu tare da bai wa kasarmu zaman lafiya mai dorewa, wadata da ci gaba.<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Barka da cika shekaru 66 da samun &#8216;yancin kai Najeriya&#8221;<\/em> cewar ta.<\/p>\n<p>Hakazalika Uwargidan Shugaban kasar ta taya tsofaffin kasar murna yayin da duniya ke bikin ranar tsofaffi ta duniya a ranar 1 ga Oktoba a kowace shekara.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Yayin da duniya ke bikin cika shekaru 36 da fara ranar tsofaffi ta duniya mai taken &#8216;Zamanin Tsawon Rai: Sake Duba Tsare-tsare don Rayuwa Mai Tsayi ana tunatar da mu nauyin da ke kanmu na tabbatar da cewa tsofaffi suna cikin koshin lafiya suna ba da gudummawa kuma ana girmama su<\/em>&#8221; in ji Uwargidan shugaban Kasa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Ministan FCT Ya Taya Uwargidan Shugaban Kasa Murnar Cika Shekaru 66<\/p>\n<p><em>&#8220;Tsofaffi su ne masu rike da hikima da gogewa masu matukar muhimmanci. Bai kamata a taba watsar da su yin watsi da su ko ware su ba &#8220;Maimakon haka ya kamata a ba su goyon baya da kuma damammaki masu ma&#8217;ana don su ci gaba da taka rawa a harkokin iyali da na al&#8217;umma&#8221;<\/em> in ji ta.<\/p>\n<p>Saboda haka Uwargidan Shugaban Kasa ta yi kira ga iyalai da kada su yi watsi da tsofaffi a cikinsu sai dai su daraja su tare da ci gaba da kula da su.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Ina kira ga iyalai da al&#8217;ummomi a fadin Najeriya da su ci gaba da daraja shawarwarinsu su koyi darussa daga abubuwan da suka fuskanta a rayuwa tare da karfafa tsare-tsaren da za su ba su damar tsufa cikin mutunci da kuma ci gaba da kasancewa masu amfani ga al&#8217;umma tare da samar da ingantattun matakan tallafin jin dadin jama&#8217;a&#8221;<\/em> cewar ta.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta bayyana cewa kasar ta nuna karfin gwiwa da juriya tun bayan samun &#8216;yancin kai a ranar 1 ga Oktoba 1960. Ta bayyana hakan ne a cikin sakon da ta aika wa &#8216;yan kasa domin taya murnar cika shekaru 66 da kasar ta samu &#8216;yancin kai. &#8220;Yayin da Najeriya ke &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4881,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-4878","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4878","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4878"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4878\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4883,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4878\/revisions\/4883"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4881"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4878"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4878"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4878"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}