{"id":4653,"date":"2026-09-27T14:59:03","date_gmt":"2026-09-27T14:59:03","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4653"},"modified":"2026-09-27T14:59:03","modified_gmt":"2026-09-27T14:59:03","slug":"kano-ta-zama-jiha-ta-daya-a-sakamakon-jarabawar-neco-na-shekarar-2026","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/27\/kano-ta-zama-jiha-ta-daya-a-sakamakon-jarabawar-neco-na-shekarar-2026\/","title":{"rendered":"Kano Ta Zama Jiha Ta Daya  A Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekarar 2026"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Jihar Kano ta zama jiha ta daya a Najeriya wajen samun nasara a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026 (SSCE) da Hukumar Kula da Jarabawa ta Kasa (NECO) ta gudanar.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jihar ta samu adadin dalibai 74,413 da suka samu maki mai kyau (credit) a darussa akalla biyar ciki har da Turanci da Lissafi hakan ya sa ta zarce Jihar Lagos wadda ta samu dalibai 72,496 yayin da Jihar Oyo ta zo ta uku da dalibai 55,543.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wannan nasara ita ce ta biyu a jere da Jihar Kano ta zama ta daya a jerin jihohin da suka fi nuna kwazo a jarabawar NECO bayan irin wannan nasarar da ta samu a jarabawar shekarar 2025.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake tsokaci kan wannan ci gaba ta cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa dalibai malamai iyaye da sauran masu ruwa da tsaki bisa abin da ya kira kwazo na musamman.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSCE ta shekarar 2026<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wadannan nasarori da aka samu a jere sun nuna cewa ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi da gwamnatin jihar ke yi yana haifar da sakamako mai kyau da ake iya gani.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bai wa al&#8217;ummar Kano tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga fannin ilimi ta hanyar kara yawan kudade inganta kayan aikin makaranta daukar malamai da horar da su bayar da tallafin karatu da kuma taimaka wa daliban da ba su da karfin biyan kudin makaranta.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A matsayin wani bangare na wadannan matakan tallafi, gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan 4.4 a shekarar 2026 wajen biyan kudin jarabawar kammala sakandare (SSCE) ga dalibai musamman wadanda ba su da karfin biya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cewar gwamnan an tsara wannan tallafin ne domin kawar da cikas na kudi da kuma bai wa dalibai damar shiga jarabawar cikin sauki.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce sakamakon jarabawar NECO na baya-bayan nan ya kara tabbatar da ci gaban da daliban Kano ke samu a karkashin wannan gwamnati.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A karkashin jagorancin Gwamna Yusuf fannin ilimi ya kasance yana samun daya daga cikin manyan kaso na kudade a kasafin kudin shekara-shekara na jihar Kano.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A shekarar 2024 ilimi ya dauki kusan kashi 29.95 na kasafin kudin jihar yayin da a kasafin kudin 2025 kudaden da aka ware suka karu zuwa Naira biliyan 168.35 wanda ya kai kashi 31 na jimillar kasafin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Don shekarar 2026 jihar ta ware Naira biliyan 405.35 ga fannin ilimi wanda ya kai kusan kashi 30 na jimillar kasafin kudin jihar na Naira tiriliyan 1.478.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamna Yusuf ya bayyana cewa, saka hannun jarin ya wuce batun biyan kudin jarabawa kawai ya kuma hada da gyaran azuzuwa, daukar malamai samar da kayan karatu da kayan sanya na makaranta (uniforms) tallafin karatu da sauran matakan da nufinsu shi ne inganta ilimi a fadin jihar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Manufofin gwamnatin kan fannin ilimi sun kuma jawo yabo da karbuwa a matakin kasa da na duniya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamna Yusuf ya sadaukar da wannan nasarar ta NECO ga dalibai malamai iyaye da al&#8217;ummar jihar Kano tare da tabbatar musu cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya ce manufar ita ce samar da tsarin ilimi mai karfin bai wa matasan Kano ilimi da kwarewar da ake bukata domin ci gaba da karatu a manyan makarantu samun aikin yi kirkire-kirkire da kuma jagoranci.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamnan ya yi nuni da cewa a halin yanzu tsarin ilimin jihar Kano yana kula da dalibai sama da miliyan biyar bisa alkaluman kididdigar makarantu ta shekara-shekara da gwamnatin ta ambata.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jihar Kano ta zama jiha ta daya a Najeriya wajen samun nasara a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026 (SSCE) da Hukumar Kula da Jarabawa ta Kasa (NECO) ta gudanar. Jihar ta samu adadin dalibai 74,413 da suka samu maki mai kyau (credit) a darussa akalla biyar ciki har da Turanci da Lissafi hakan ya &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4655,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[113,114],"class_list":["post-4653","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","tag-kano-state","tag-neco-2026"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4653","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4653"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4653\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4656,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4653\/revisions\/4656"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4655"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4653"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4653"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4653"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}