{"id":4649,"date":"2026-09-27T14:26:25","date_gmt":"2026-09-27T14:26:25","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4649"},"modified":"2026-09-27T14:26:25","modified_gmt":"2026-09-27T14:26:25","slug":"shugaba-trump-ya-yi-hasashen-yarjejeniyar-amurka-da-cuba-ba-tare-da-matakin-soja-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/27\/shugaba-trump-ya-yi-hasashen-yarjejeniyar-amurka-da-cuba-ba-tare-da-matakin-soja-ba\/","title":{"rendered":"Shugaba Trump Ya Yi Hasashen Yarjejeniyar Amurka Da Cuba Ba Tare Da Matakin Soja Ba"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana sa ran Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya inda ya jaddada cewa ba za a bukaci daukar matakin soja a kan kasar ba.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Ina ganin cewa Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya.<\/em> Ba na tunanin za mu bukaci amfani da sojoji&#8221; in ji Shugaba Trump yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar White House ranar Asabar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bayyana hakan ne kafin ya tafi jihar Tennessee, yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin Cuba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamnatin Amurka ta bayyana a fili cewa manufarta ita ce sauya gwamnatin Cuba. Matakin hana shigo da man fetur da Washington ta dauka a farkon wannan shekarar ya kara jefa kasar cikin mawuyacin hali yayin da take fuskantar karancin man fetur da katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar kayayyakin more rayuwa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaba Trump ya ce: &#8220;Muna son taimaka wa Cuba&#8230; Muna son bude kofar Cuba ga mutanenmu.&#8221;<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Amurka ta sanya takunkumi kan hukumomi ko kamfanoni 11 na Cuba<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cikin jawabin da ya yi a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata Shugaba Trump ya kwatanta Cuba a matsayin kasa da ta gaza inda ya ce &#8220;<em>yanci zai zo<\/em>&#8221; ga kasar. Tawagar wakilan Cuba ta fice daga zauren taron yayin da yake jawabi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga baya ranar Asabar Ministan Harkokin Wajen Cuba Bruno Rodriguez ya bayyana cewa Cuba a shirye take ta tattauna da Amurka ba tare da ya yi tsokaci kai tsaye kan kalaman Shugaba Trump ba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>A shirye muke mu gudanar da harkokin kasuwanci da kamfanonin Amurka kamar yadda muke yi da sauran kasashe&#8221;<\/em> in ji Rodriguez yayin da yake kakkausar suka kan takunkumin kasuwanci da Amurka ta dade tana kakaba wa Cuba.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Amurka ta ci gaba da aiwatar da wannan takunkumi na tsawon sama da shekaru 60 yayin da gwamnatin Shugaba Trump ta kara matsa lamba kan Havana a &#8216;yan watannin nan.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana sa ran Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya inda ya jaddada cewa ba za a bukaci daukar matakin soja a kan kasar ba. &#8220;Ina ganin cewa Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya. Ba na tunanin za mu bukaci amfani da sojoji&#8221; in ji Shugaba Trump &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4651,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-4649","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4649","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4649"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4649\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4652,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4649\/revisions\/4652"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4651"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4649"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4649"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4649"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}