{"id":4639,"date":"2026-09-27T13:30:52","date_gmt":"2026-09-27T13:30:52","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4639"},"modified":"2026-09-27T13:30:52","modified_gmt":"2026-09-27T13:30:52","slug":"tsohon-firayim-ministan-guinea-toure-ya-rasu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/27\/tsohon-firayim-ministan-guinea-toure-ya-rasu\/","title":{"rendered":"Tsohon Firayim Ministan Guinea Tour\u00e9 Ya Rasu"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Tsohon Firayim Minista kuma babban jigon &#8216;yan adawa a kasar Guinea Sidya Tour\u00e9 ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tour\u00e9 ya kasance yana jagorantar daya daga cikin manyan jam&#8217;iyyun adawa na kasar, wato Union of Republican Forces (UFR) yayin da yake gudun hijira a kasar Ivory Coast.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jam&#8217;iyyar UFR na daya daga cikin jam&#8217;iyyun siyasa 40 da aka soke a watan Maris a cikin wani mataki mai tsauri na takaita &#8216;yancin jama&#8217;a karkashin jagorancin shugaba mai karfin iko na kasar Mamady Doumbouya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wata majiya mai kusanci da iyalin marigayin ta bayyana cewa Tour\u00e9 ya rasu ne a ranar Juma&#8217;a a birnin Paris bayan shafe shekaru da dama yana taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da rayuwar jama&#8217;ar Guinea.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Majiyoyin wadanda suka bukaci a boye sunayensu saboda dalilai na tsaro sun ce an kwantar da shi a Asibitin Amurka da ke Paris (American Hospital of Paris) na tsawon makonni biyu bayan ya yi rashin lafiya a birnin Abidjan.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tour\u00e9 ya zauna a Abidjan tun bayan barin kasar Guinea sakamakon juyin mulkin soji na watan Satumbar 2021 wanda ya kawo Doumbouya kan karagar mulki.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga baya, an zabi Doumbouya a matsayin shugaban kasar ta Yammacin Afirka a watan Disambar bara a zaben da aka ware manyan jam&#8217;iyyun adawa ciki har da UFR da sauran manyan jam&#8217;iyyun adawa biyu na kasar wato UFDG da RPG.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban jam&#8217;iyyar UFDG Cellou Dalein Diallo wanda shi ma ke zaune a gudun hijira ya bayyana bakin cikinsa game da rashin &#8220;<em>aboki kuma abokin gwagwarmaya&#8221;<\/em> domin kasar Guinea, a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tour\u00e9 ya yi tarayya wajen burin ganin an canza fasalin &#8220;<em>kasarmu tare da dukkan dumbin damammakin da take da su zuwa kasa mai bunkasar tattalin arziki da ke tafiya bisa ka&#8217;idojin dimokuradiyya da bin doka da oda.&#8221;<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban kasar Guinea Lansana Conte wanda ya yi mulki tsakanin shekarun 1984 da 2008 ya nada Tour\u00e9 a matsayin Firayim Minista a watan Yulin 1996 mukamin da ya rike har zuwa watan Maris na 1999.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Lokacin da ya rike mukamin Firayim Minista ya kasance mai cike da sauye-sauye a fannin gudanarwa da tattalin arziki tare da kokarin karfafa dangantakar Guinea da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Bayan ya bar gwamnati Tour\u00e9 ya zama shugaban jam&#8217;iyyar UFR a shekarar 2000. A hankali ya zama babban jigo wajen nuna adawa ga Conte da kuma gwamnatocin da suka biyo bayansa.<br \/>\n<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tour\u00e9 ya tsaya takarar shugaban kasa a matsayin dan takarar jam&#8217;iyyar UFR a shekarun 2010 da 2015 inda ya sha kashi a dukkan lokutan biyu.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">An haife shi a shekarar 1945 a kasar Ivory Coast inda kuma ya yi wani bangare na aikinsa musamman a fannin gudanar da harkokin tattalin arziki da kudi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tsohon shugaban kasa Alpha Conde\u2014wanda Tour\u00e9 ya yi aiki a karkashinsa duk da cewa sun taba samun sabani a wasu lokuta\u2014ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, abin takaici ne matuka yadda mutumin da ya ba kasarsa gudunmawa mai yawa ya tsinci kansa cikin halin wahalar rayuwa a gudun hijira a karshen rayuwarsa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Firayim Ministan Guinea na yanzu Amadou Oury Bah ya bayyana Tour\u00e9 a wani sako da ya wallafa a shafin X a matsayin &#8220;<em>mai kawo sauyi mai duba gaskiyar al&#8217;amura&#8221; da kuma &#8220;fitaccen mutum a fagen siyasar Guinea na tsawon shekaru talatin.<\/em>&#8220;<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tsohon Firayim Minista kuma babban jigon &#8216;yan adawa a kasar Guinea Sidya Tour\u00e9 ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Tour\u00e9 ya kasance yana jagorantar daya daga cikin manyan jam&#8217;iyyun adawa na kasar, wato Union of Republican Forces (UFR) yayin da yake gudun hijira a kasar Ivory Coast. Jam&#8217;iyyar UFR na daya daga cikin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4641,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-4639","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4639","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4639"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4639\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4644,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4639\/revisions\/4644"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4641"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4639"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4639"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4639"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}