{"id":4517,"date":"2026-09-25T11:44:10","date_gmt":"2026-09-25T11:44:10","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4517"},"modified":"2026-09-25T11:44:10","modified_gmt":"2026-09-25T11:44:10","slug":"cote-divoire-za-ta-karbi-bakuncin-taron-kasuwanci-na-amurka-da-afirka-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/25\/cote-divoire-za-ta-karbi-bakuncin-taron-kasuwanci-na-amurka-da-afirka-2027\/","title":{"rendered":"C\u00f4te d&#8217;Ivoire Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kasuwanci Na Amurka Da Afirka 2027"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Kaba Niale Babban Minista kuma Ministan Harkokin Waje ta sanar cewa kasar C\u00f4te d\u2019Ivoire ce za ta karbi bakuncin taron kasuwanci na Amurka da Afirka (U.S.-Africa Business Summit) a shekarar 2027.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ta yi wannan sanarwar ne a gefen taron tattaunawa kan kasuwanci da zuba jari da kungiyar Corporate Council on Africa (CCA) ta shirya a Amurka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ta bayyana zabin birnin Abidjan a matsayin &#8220;<em>alama ta nuna amincewa da kuma nauyi&#8221;<\/em> ga kasar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ana sa ran wannan babban taro zai mayar da C\u00f4te d\u2019Ivoire cibiyar kasuwanci da ke hada Amurka da nahiyar Afirka tare da zama ginshikin bunkasa zuba jari kasuwanci da hadin gwiwa mai muhimmanci tsakanin Washington da Afirka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: C\u00f4te d\u2019Ivoire za ta karbi bakuncin taron yankin Afirka na farko kan harkokin ruwa<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A cewar gwamnati wannan zabi yana nuna kyakkyawar alakar abota da hadin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin C\u00f4te d\u2019Ivoire da Amurka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A jawabinta Niale ta ambaci muhimman mutane ciki har da Franck Garcia Mataimakin Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka da kuma Florizelle Liser Shugaba kuma Babban Jami&#8217;in Gudanarwa na kungiyar Corporate Council on Africa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ta ce &#8220;<em>Zuba jarin Amurka a C\u00f4te d\u2019Ivoire ya fara haifar da sakamako mai kyau&#8221; inda ta ambaci kamfanin Cybastion a fannin sauye-sauyen fasahar zamani (digitaltransformation) Starlink a fannin samar da intanet da kuma Zipline a fannin jigilar kayan kiwon lafiya.\u201d<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ministar ta bayyana cewa C\u00f4te d\u2019Ivoire na da burin mayar da alkawuran zuba jari zuwa zahirin ayyuka tare da karfafa gwiwar shugabannin kasuwanci a taron su shiga tattaunawa kai tsaye da kuma kulla kawance mai dorewa wanda zai biya bukatun al&#8217;umma.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kasancewar za ta karbi bakuncin taron na 2027 ya tabbatar da matsayin Abidjan a matsayin muhimmiyar cibiyar tattalin arziki a Yammacin Afirka wanda ke nuna ci gaban hadin gwiwa mai karfi tsakanin C\u00f4te d\u2019Ivoire da Amurka.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kaba Niale Babban Minista kuma Ministan Harkokin Waje ta sanar cewa kasar C\u00f4te d\u2019Ivoire ce za ta karbi bakuncin taron kasuwanci na Amurka da Afirka (U.S.-Africa Business Summit) a shekarar 2027. Ta yi wannan sanarwar ne a gefen taron tattaunawa kan kasuwanci da zuba jari da kungiyar Corporate Council on Africa (CCA) ta shirya a &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4519,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-4517","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4517","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4517"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4517\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4521,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4517\/revisions\/4521"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4519"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4517"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4517"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4517"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}