{"id":4513,"date":"2026-09-25T11:24:56","date_gmt":"2026-09-25T11:24:56","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4513"},"modified":"2026-09-25T11:24:56","modified_gmt":"2026-09-25T11:24:56","slug":"dr-congo-likita-ya-rasu-yayin-da-cutar-ebola-ke-karuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/25\/dr-congo-likita-ya-rasu-yayin-da-cutar-ebola-ke-karuwa\/","title":{"rendered":"DR Congo: Likita Ya Rasu Yayin Da Cutar Ebola Ke Karuwa"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Wani matashin likita ya rasu sakamakon cutar Ebola a birnin Kisangani yayin da ake samun karuwar masu dauke da cutar a wajen yankin da annobar ta fi kamari a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Dr. Victor Kingombe likitan cututtukan cikin jiki ya rasu sakamakon cutar a cibiyar kula da masu dauke da Ebola da ke Kisangani babban birnin lardin Tshopo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Abokan aikinsa da &#8216;yan uwansa sun taru domin jana&#8217;izarsa suna kallon yadda ma&#8217;aikatan lafiya sanye da kayan kariya suka dauki gawar tasa zuwa cikin akwatin gawa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Likitanmu na cututtukan cikin jiki ya tafi. Dr. Victor me ya sa Me ya sa Likita Likitanmu na cututtukan cikin jik<\/em>i&#8221; in ji takwararsa likita Agnes Kalokola cikin kuka.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Ebola a DRC: WHO ta yi gargadi game da karancin ma&#8217;aikatan lafiya<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">An fara samun rahoton masu dauke da Ebola a Kisangani a karshen watan Yuni kuma an kaddamar da cibiyar kula da masu cutar da Kingombe ya rasu a cikinta ne kasa da makonni biyu da suka gabata.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Duk da cewa an samu raguwar masu dauke da cutar a wannan watan a lardin Ituri\u2014yankin da annobar ta fi kamari\u2014lardunan da ke makwabtaka da shi sun yi rajistar karuwa mai yawa, inda aka ga karuwar kashi 73 cikin dari a lardin North Kivu cikin makonni uku da suka gabata.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa annobar na kan hanyar zarce wacce ta faru a Yammacin Afirka tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 wacce ita ce mafi muni a tarihi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Cutar na yaduwa ne a cikin mawuyacin hali sakamakon rashin tsaro gudun hijira yajin aikin ma&#8217;aikatan lafiya da kuma yawan zirga-zirgar jama&#8217;a.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ma&#8217;aikatan lafiya na fuskantar rashin amincewa daga al&#8217;umma inda aka kai hare-hare kan cibiyoyin kula da masu cutar da kuma kungiyoyin da ke gudanar da jana&#8217;iza a lokuta daban-daban yayin da ake yada jita-jitar cewa cutar Ebola ba gaskiya ba ce.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Mataimakin gwamnan lardin Tshopo Didier Lomoyo Iteku wanda ya halarci jana&#8217;izar Kingombe ya ce bayan ya kalli gawar ta cikin taga ta filasti &#8220;<em>Wannan cuta gaskiya ce. Ga likita nan wanda ya zo nan domin kokarin ceto rayuka amma shi kansa ya zama wanda cutar ta shafa.<\/em>&#8220;<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Congo ta fara yi wa ma&#8217;aikatan lafiya allurar rigakafin Ebola a Kisangani a watan Agusta ta hanyar amfani da allurar Ervebo\u2014wacce aka fara kirkira domin nau&#8217;in cutar na Zaire amma aka gano tana bayar da kariya daga nau&#8217;in cutar na Bundibugyo da ake fama da shi a yanzu. Ana ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen hanyoyin magance cutar a fadin kasar.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wani matashin likita ya rasu sakamakon cutar Ebola a birnin Kisangani yayin da ake samun karuwar masu dauke da cutar a wajen yankin da annobar ta fi kamari a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Dr. Victor Kingombe likitan cututtukan cikin jiki ya rasu sakamakon cutar a cibiyar kula da masu dauke da Ebola da ke Kisangani babban &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4515,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[101,102],"class_list":["post-4513","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","tag-congo","tag-ebol"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4513","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4513"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4513\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4516,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4513\/revisions\/4516"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4515"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4513"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4513"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4513"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}