{"id":4458,"date":"2026-09-24T11:06:53","date_gmt":"2026-09-24T11:06:53","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4458"},"modified":"2026-09-24T11:06:53","modified_gmt":"2026-09-24T11:06:53","slug":"najeriya-da-zambiya-sun-dauki-matakin-zurfafa-hadin-gwiwa-tsakaninsu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/24\/najeriya-da-zambiya-sun-dauki-matakin-zurfafa-hadin-gwiwa-tsakaninsu\/","title":{"rendered":"Najeriya Da Zambiya Sun Dauki Matakin Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakaninsu."},"content":{"rendered":"<p><strong>Ana sa ran Najeriya da Zambiya za su zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a muhimman fannoni bayan da Babban Kwamishinan Najeriya a Zambia Jakada Efe A. Clark-Omeru ya mika takardun shaidar aikinsa ga Shugaba Hakainde Hichilema<\/strong>.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar Harkokin Waje ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinta Mista Oluwafemi Adeniyi ya sanya wa hannu a Abuja.<\/p>\n<p>An gudanar da bikin ne a birnin Lusaka inda Jakada Clark-Omeru ya isar da sakon gaisuwa da fatan alheri daga Shugaba Bola Tinubu zuwa ga Shugaba Hichilema da kuma al&#8217;ummar kasar Zambia.<\/p>\n<p>Ana sa ran wannan mataki zai karfafa dangantakar diflomasiyya tare da inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Zambiya a fannonin da suka shafi moriyar kasashen biyu.<\/p>\n<p>Mika takardun shaidar aikin da Babban Kwamishinan ya yi na nuni ne da fara aikin diflomasiyyarsa a hukumance a kasar Zambia.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-4462 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-2-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"333\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-2-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-2.jpg 631w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>Babban Kwamishinan ya kuma taya Shugaba Hichilema murnar sake zabensa a karo na biyu a babban zaben kasar Zambiya na watan Agusta na shekarar 2026.<\/p>\n<p>A cewar sanarwar Jakada Clark-Omeru ta jaddada dadaddiyar alaka tsakanin Najeriya da Zambiya wacce ta ginu kan muradun juna girmama juna hadin kan kasashen Afirka, da kuma tarihin hadin gwiwa wajen yaki da mulkin mallaka da tsarin wariyar launin fata a Kudancin Afirka.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Babban Kwamishinan ya bayyana shirye-shiryen Najeriya na kara karfafa alakar kasashen biyu ta hanyar yarjejeniyoyin da ake da su da kuma sabbin hadin gwiwa a muhimman fannoni ciki har da noma hakar ma&#8217;adanai kasuwanci da zuba jari ilimi yawon bude ido masana&#8217;antar kirkire-kirkire kimiyya da fasaha, da kuma tura masu aikin sa kai karkashin shirin &#8216;Technical Aid Corps Scheme<\/em>&#8221; cewar Adeniyi.<\/p>\n<p>A jawabinsa Shugaba Hichilema ya bayyana muhimmancin da Zambiya ke baiwa diflomasiyyar tattalin arziki karkashin shirin &#8216;Grow Zambia Agenda&#8217; tare da yin kira ga jami&#8217;an diflomasiyya da su goyi bayan karuwar zuba jari kasuwanci yawon bude ido da hadin gwiwar tattalin arziki a matakin kasa da kasa.<\/p>\n<p>Ya jaddada bukatar mayar da alakar diflomasiyya zuwa ayyuka na zahiri da kuma sakamako mai amfani.<\/p>\n<p>Shugaba Hichilema ya yi kira da a samar da karin hadin gwiwa tsakanin &#8216;yan kasuwa al&#8217;ummomi da gwamnatoci tare da ba da fifiko na musamman ga fannin fasaha da kuma kara darajar kayayyaki a cikin gida.<\/p>\n<p>Shugaban Zambia ya ce &#8220;<em>zaman lafiya tsaro da kwanciyar hankali<\/em>&#8221; su ne abubuwan da ake bukata don ci gaba mai dorewa.<\/p>\n<p>Ya kuma yi kira da a samar da isasshen jari ga masu zuba jari sannan ya nuna damar da ake da ita ta yawon bude ido a Zambiya yana mai sanar da cewa ana shirin inganta filayen jiragen sama guda hudu na larduna zuwa matsayin kasa da kasa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Najeriya Za Ta Karbi Bakuncin Taron Duniya Na Masu Harkar Hulda Da Jama&#8217;a (Public Relations) Na Shekarar 2026.<\/p>\n<p>Shugaba Hichilema ya sake jaddada kudirin Zambia na goyon bayan Yarjejeniyar Yankin Ciniki Cikin &#8216;Yanci na Afirka (AfCFTA) da kuma karfafa ciniki tsakanin kasashen Afirka.<\/p>\n<p>A yayin ganawa ta musamman da Shugaba Hichilema Jakada Clark-Omeru ta bayyana gudummawar da kamfanoni da kwararrun &#8216;yan Najeriya ke bayarwa ga tattalin arzikin Zambiya ciki har da Dangote Cement Access Bank Zambiya UBA Zambia Sahara Group Harvest Group Atlas Group Naija Chops da Tasty Bite.<\/p>\n<p>Ta kuma bayyana sha&#8217;awar Najeriya ta duba yiwuwar kulla Yarjejeniyar Ayyukan Sufurin Jiragen Sama tsakanin kasashen biyu (BASA) domin samar da hanyar zirga-zirgar jiragen sama kai-tsaye tsakanin Najeriya da Zambiya.<\/p>\n<p>Adeniyi ya ce Shugaba Hichilema ya amince da muhimmiyar gudummawar da kamfanonin Najeriya ke bayarwa a Zambiya tare da lura da cewa an dauki matakai don samar da yanayin kasuwanci mai inganci da sauki.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba Hichilema da Jakada Clark-Omeru &#8220;<em>ta bayyana damammakin karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Zambia ta hanyar inganta hadin gwiwa a bangaren kamfanoni masu zaman kansu da kuma mu&#8217;amala tsakanin al&#8217;ummar kasashen biyu.&#8221;<\/em><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-4461 aligncenter\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-3-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"500\" height=\"333\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-3-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/NIG-3.jpg 631w\" sizes=\"auto, (max-width: 500px) 100vw, 500px\" \/><\/p>\n<p>Bikin ya biyo bayan liyafa a Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Lusaka inda ya tattaro shugabannin al&#8217;ummar Najeriya da wakilan &#8216;yan kasuwan Najeriya.<\/p>\n<p>Wannan liyafar ta bai wa Ambasada Clark-Omeru damar sake jaddada kudirin tawagar na inganta walwalar &#8216;yan Najeriya yayin da take aiki tare da al&#8217;ummar Najeriya da &#8216;yan kasuwan Zambia.<\/p>\n<p>A cewar Ma&#8217;aikatar Harkokin Waje, tawagar za ta ci gaba da aiki tare da &#8216;yan Najeriya da &#8216;yan kasuwan Zambia don ciyar da &#8220;<em>muhimmancin tattalin arziki dabi&#8217;u da kuma hoton Najeriya&#8221;<\/em> gaba.<\/p>\n<p>Gwamnatin Najeriya ta ce tana fatan yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Zambiya don karfafa dadadden zumunci tsakanin kasashen biyu da kuma bunkasa kawancen da ke ciyar da muradun su gaba da kuma wadata juna.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ana sa ran Najeriya da Zambiya za su zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a muhimman fannoni bayan da Babban Kwamishinan Najeriya a Zambia Jakada Efe A. Clark-Omeru ya mika takardun shaidar aikinsa ga Shugaba Hakainde Hichilema. Ma&#8217;aikatar Harkokin Waje ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinta Mista Oluwafemi Adeniyi ya sanya wa hannu a &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4463,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[95,96],"class_list":["post-4458","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","tag-nigeria","tag-zambia"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4458","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4458"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4458\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4464,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4458\/revisions\/4464"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4463"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4458"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4458"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4458"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}