{"id":4452,"date":"2026-09-24T10:39:42","date_gmt":"2026-09-24T10:39:42","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4452"},"modified":"2026-09-24T10:39:42","modified_gmt":"2026-09-24T10:39:42","slug":"ebola-a-drc-hukumar-lafiya-ta-duniya-who-ta-yi-gargadi-game-da-karancin-maaikatan-lafiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/24\/ebola-a-drc-hukumar-lafiya-ta-duniya-who-ta-yi-gargadi-game-da-karancin-maaikatan-lafiya\/","title":{"rendered":"Ebola A DRC: Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Yi Gargadi Game Da Karancin Ma&#8217;aikatan Lafiya."},"content":{"rendered":"<p><strong>Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na fuskantar karancin ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da za su yi aiki a cibiyoyin kula da masu cutar Ebola yayin da kasar ke fama da barkewar cutar cikin sauri inda aka samu karuwar masu dauke da cutar da kashi 73 cikin dari a cikin makonni uku a lardin North Kivu.<\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi game da lamarin inda ta bayyana cewa har yanzu ba a iya shawo kan cutar ba duk da raguwar adadin masu dauke da ita a wasu lardunan.<\/p>\n<p>Bisa alkaluman gwamnati na baya-bayan nan, cutar ta bazu zuwa larduna bakwai inda aka samu mutane 7,773 da aka tabbatar suna dauke da cutar tare da mutuwar mutane 3,759.<\/p>\n<p>Daraktar WHO mai kula da ayyukan gaggawa a yankin Afirka Marie Roseline Belizaire ta ce an samu raguwar masu dauke da cutar da kashi 26 cikin dari a lardin Ituri da kuma kashi 15 cikin dari a lardin Haut-Uele tsakanin ranar 31 ga watan Agusta da 20 ga watan Satumba.<\/p>\n<p>Sai dai Belizaire ta ce yanayin yadda cutar ke yaduwa ya ci gaba da bambanta sosai a yankunan da abin ya shafa.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Yayin da ake samun raguwar masu dauke da cutar da mace-mace a wasu lardunan a wasu kuma ana ci gaba da samun karuwa. Har yanzu ba a shawo kan cutar ba kuma tana ci gaba da yaduwa a fadin yankuna masu fadi&#8221;<\/em> in ji ta.<\/p>\n<p>WHO ta ce rashin tsaro gudun hijirar jama&#8217;a yajin aikin ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da kuma karuwar zirga-zirgar jama&#8217;a na kara dagula lamarin cutar.<\/p>\n<p>Hukumar ta ce cutar na kan hanyar zarce annobar Ebola ta shekarun 2014-2016 a Yammacin Afirka wadda ita ce mafi muni a tarihi inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 11,000 musamman a kasashen Guinea Liberia da Sierra Leone.<\/p>\n<p>Catherine Smallwood jami&#8217;ar WHO mai kula da harkokin cutar Ebola ta ce an fara samun raguwar masu dauke da cutar da mace-mace a lardin North Kivu bayan makonni da dama ana samun karuwa.<\/p>\n<p>Ta ce duk da cewa ana kara yawan gadajen kula da marasa lafiya a kowace rana cibiyoyin kiwon lafiya na ci gaba da fuskantar karancin ma&#8217;aikata da abokan aiki da ake bukata wajen gudanar da ayyukansu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na fuskantar karancin ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da za su yi aiki a cibiyoyin kula da masu cutar Ebola yayin da kasar ke fama da barkewar cutar cikin sauri inda aka samu karuwar masu dauke da cutar da kashi 73 cikin dari a cikin makonni uku a lardin North Kivu. Hukumar Lafiya ta &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4455,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[82,83],"class_list":["post-4452","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","tag-drc","tag-ebola"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4452","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4452"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4452\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4457,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4452\/revisions\/4457"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4455"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4452"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4452"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4452"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}