{"id":4385,"date":"2026-09-23T10:34:04","date_gmt":"2026-09-23T10:34:04","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4385"},"modified":"2026-09-23T10:34:04","modified_gmt":"2026-09-23T10:34:04","slug":"shugaban-kasar-sudan-ta-kudu-ya-rusa-gwamnatinsa-saboda-takaddama","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/23\/shugaban-kasar-sudan-ta-kudu-ya-rusa-gwamnatinsa-saboda-takaddama\/","title":{"rendered":"Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Ya Rusa Gwamnatinsa Saboda Takaddama"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya rusa gwamnatin ri\u0199on \u0199warya a ranar Talata sa&#8217;o&#8217;i bayan ya sanya hannu kan gyare-gyare ga dokokin za\u0253e wa\u0257anda suka cire bu\u0199atun kammala kundin tsarin mulki na dindindin da kuma \u0199idayar jama&#8217;a na \u0199asa kafin a ka\u0257a \u0199uri&#8217;a.<\/strong><\/p>\n<p>An tura manyan jami&#8217;an tsaro a Sudan ta Kudu ranar Talata yayin da shugaban ke shirin rusa gwamnatin don za\u0253en farko inda masu sharhi suka yi garga\u0257in cewa sauye-sauyen doka na \u0257an lokaci ka\u0257an za su ba shi cikakken iko kan sauyin.<\/p>\n<p>Sudan ta Kudu ta sami &#8216;yancin kai a shekarar 2011 amma jim ka\u0257an bayan haka ta fa\u0257a cikin yakin basasa na shekaru biyar kuma ta kasance \u0257aya daga cikin \u0199asashe mafi talauci da cin hanci da rashawa a duniya.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Sudan Ta Kudu Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokar Zabe Gabanin Zaben Watan Disamba.<\/p>\n<p>Ana sa ran gudanar da zabe a ranar 22 ga watan Disamba bayan an dage shi sau biyu amma gwamnati ta gaza aiwatar da kusan dukkan sharuddan da aka gindaya a yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018.<\/p>\n<p>Bisa rahotanni ba a yi rajistar masu kada kuri&#8217;a ba ba a hada rundunonin sojoji masu adawa da juna waje guda ba kuma kundin tsarin mulkin da aka dade ana jira bai samu tabbatuwa ba.<\/p>\n<p>Shugaba Salva Kiir ya rusa gwamnati da tsakiyar dare (karfe 10 na dare agogon GMT) daidai da jadawalin zaben da aka amince da shi sannan ya nada sabuwar gwamnatin rikon kwarya da za ta kula da gudanar da zaben.<\/p>\n<p>Sai dai wannan mataki ya zo ne kwana guda bayan da aka yi gyare-gyare a Dokar Zabe ta Kasa wadanda suka bai wa Kiir damar ci gaba da rike iko tare da cire dukkan mataimakan shugaban kasa da aka nada bisa yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 a lokacin gudanar da zaben.<\/p>\n<p>Gyare-gyaren sun kuma ba da damar ci gaba da zaben duk da rashin kundin tsarin mulki ko kuma kididdigar al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Masana sun yi gargadi yayin da suke zantawa da ofishin kamfanin dillancin labarai na AFP da ke Nairobi cewa gyare-gyaren sun bai wa Kiir cikakken iko ba tare da wani shamaki ba.<\/p>\n<p>A cewar lauya kuma tsohon memba a kwamitin tsara kundin tsarin mulki Michael Wani &#8220;<em>Kiir zai kasance shi kadai ne mai iko ba tare da mataimakan shugaban kasa ba ba tare da bangaren zartarwa ba kuma ba tare da majalisar dokoki ba.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Mai sharhi mai zaman kansa Machot Amuom ya bayyana cewa akwai &#8220;<em>rudani<\/em>&#8221; sosai game da sauye-sauyen da aka yi a doka.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Sabuwar dokar tana bai wa shugaban kasa cikakken iko. Yana iya yanke shawarar kin gudanar da zabe har na tsawon shekara guda ko ma shekaru biyu masu zuwa&#8221;<\/em> in ji Amuom.<\/p>\n<p>Rahotanni sun nuna cewa an ga karuwar sojoji a babban birnin kasar, Juba a ranar Talata.<\/p>\n<p>Har yanzu akwai tsananin takun-saka tsakanin bangarorin siyasa masu adawa da juna yayin da ake tsare da shugaban &#8216;yan adawa Riek Machar bisa zargin cin amanar kasa.<\/p>\n<p>A wannan yanayi masu sa ido na kasa da kasa na fargabar cewa zaben na iya jefa kasar cikin rikici mai tsanani.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya rusa gwamnatin ri\u0199on \u0199warya a ranar Talata sa&#8217;o&#8217;i bayan ya sanya hannu kan gyare-gyare ga dokokin za\u0253e wa\u0257anda suka cire bu\u0199atun kammala kundin tsarin mulki na dindindin da kuma \u0199idayar jama&#8217;a na \u0199asa kafin a ka\u0257a \u0199uri&#8217;a. An tura manyan jami&#8217;an tsaro a Sudan ta Kudu ranar Talata &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4388,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-4385","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4385","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4385"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4385\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4389,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4385\/revisions\/4389"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4388"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4385"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4385"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4385"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}