{"id":4257,"date":"2026-09-20T11:40:59","date_gmt":"2026-09-20T11:40:59","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4257"},"modified":"2026-09-20T11:40:59","modified_gmt":"2026-09-20T11:40:59","slug":"congo-ta-fara-allurar-rigakafin-ebola-ga-maaikatan-lafiya-na-frontline","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/20\/congo-ta-fara-allurar-rigakafin-ebola-ga-maaikatan-lafiya-na-frontline\/","title":{"rendered":"Congo Ta Fara Allurar Rigakafin Ebola Ga Ma&#8217;aikatan Lafiya Na Frontline"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta fara yi wa ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da ke kan gaba wajen yaki da cutar Ebola allurar rigakafi a Bunia a lardin Ituri wanda shi ne cibiyar yankin da cutar ke yaduwa cikin sauri a kasar.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shirin bayar da rigakafin wanda ya fara ranar Asabar yana mai da hankali ne kan ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da sauran ma&#8217;aikatan da ke aiki a sahun gaba kuma ke cikin babban hadarin kamuwa da kwayar cutar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jami&#8217;an kiwon lafiya na amfani da allurar rigakafi ta Ervebo wacce ta tabbatar da inganci wajen yaki da bullar cutar a baya da ta samo asali daga nau&#8217;in kwayar cutar Ebola ta Zaire.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sai dai jami&#8217;ai sun ce ana bayar da allurar ne a karkashin shirin bayar da magani na musamman (compassionate-use programme) saboda har yanzu ana ci gaba da bincike kan ingancinta wajen yaki da nau&#8217;in kwayar cutar Bundibugyo wacce ke haifar da bullar cutar a yanzu.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Nikole Landu wata ma&#8217;aikaciyar kiwon lafiya ta ce ta karbi allurar ne saboda yadda take yawan mu&#8217;amala da marasa lafiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Na so a yi min allurar rigakafin ne saboda ina yawan mu&#8217;amala da mutane masu rashin lafiya kuma ina cikin babban hadarin kamuwa da cutar&#8221;<\/em> in ji ta.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Landu ta kara da cewa duk da cewa allurar ba za ta iya bayar da cikakkiyar kariya ba za ta iya rage hadarin kamuwa da mummunar rashin lafiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jami&#8217;an kiwon lafiya sun ce allurar Ervebo na iya bayar da wani mataki na kariya daga kwayar cutar Bundibugyo saboda kwayoyin cututtukan biyu suna da alaka da juna amma ana bukatar karin bincike don tantance ko za ta iya hana kamuwa da rashin lafiya ga mutanen da suka kamu da kwayar cutar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ana gudanar da shirin bayar da rigakafin ne a yankunan kiwon lafiya na Bunia da Mongbwalu a lardin Ituri wadanda dukkansu ke cikin yankunan da cutar ta fi shafa sosai.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya zuwa ranar Asabar kasar Congo ta tabbatar da bullar cutar Ebola ga mutane 7,541 ciki har da wadanda suka mutu su 3,639 bisa ga alkaluman gwamnati.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Annobar ta fi kamari a lardin Ituri kuma an bayyana ta a matsayin mafi muni a cikin bullar cutar Ebola guda 17 da aka taba samu a kasar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kokarin shawo kan lamarin ya fuskanci kalubale saboda rashin tsaro gudun hijirar jama&#8217;a yajin aikin ma&#8217;aikatan lafiya da kuma karuwar zirga-zirgar mutane.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa har yanzu yana da wuyar shawo kan annobar kuma tana iya zarce annobar Ebola ta shekarun 2014\u20132016 a Yammacin Afirka wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 11,000 musamman a kasashen Guinea Liberia da Sierra Leone.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamnan soja na lardin Ituri Manjo Janar Gaby Kasongo Mulumba ya ce daukar matakin ba ma&#8217;aikatan da ke sahun gaba fifiko wajen rigakafin ya zama dole saboda yadda suke fuskantar hadarin kamuwa da kwayar cutar da kuma muhimmiyar rawar da suke takawa wajen yaki da ita.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"><em>&#8220;Tare za mu iya kawar da cutar kwayar cutar Bundibugyo tare da kare al&#8217;ummarmu&#8221;<\/em> in ji Mulumba bayan ya karbi rigakafin a birnin Bunia ranar Asabar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">A watan da ya gabata kasar Congo ta fara bayar da rigakafin Ervebo a birnin Kisangani na lardin Tshopo inda ake sa ran shirin zai shafi yankuna 14 na kiwon lafiya a fadin lardunan Tshopo Bas-Uele da Haut-Uele.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hukumar WHO ta bayyana a watan da ya gabata cewa an amince da amfani da alluran rigakafin Ervebo guda 70,000 a Congo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ta ce za a ware allurai kimanin 50,000 domin ma&#8217;aikatan da ke sahun gaba da ma&#8217;aikatan lafiya yayin da za a yi amfani da allurai 20,000 wajen gudanar da gwajin likitanci domin tantance ko rigakafin yana ba da kariya daga kwayar cutar Bundibugyo.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kwayar cutar Bundibugyo wadda ita ce ke haifar da wannan annoba ta yanzu ba ta da rigakafi ko takamaiman magani da aka amince da su a hukumance.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta fara yi wa ma&#8217;aikatan kiwon lafiya da ke kan gaba wajen yaki da cutar Ebola allurar rigakafi a Bunia a lardin Ituri wanda shi ne cibiyar yankin da cutar ke yaduwa cikin sauri a kasar. Shirin bayar da rigakafin wanda ya fara ranar Asabar yana mai da hankali ne kan ma&#8217;aikatan &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4259,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42,45],"tags":[],"class_list":["post-4257","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","category-health"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4257","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4257"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4257\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4260,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4257\/revisions\/4260"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4259"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4257"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4257"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4257"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}