{"id":4237,"date":"2026-09-20T09:49:38","date_gmt":"2026-09-20T09:49:38","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4237"},"modified":"2026-09-20T09:49:38","modified_gmt":"2026-09-20T09:49:38","slug":"shugabannin-tsaro-na-nato-sun-zabi-carsten-breuer-a-matsayin-shugaba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/20\/shugabannin-tsaro-na-nato-sun-zabi-carsten-breuer-a-matsayin-shugaba\/","title":{"rendered":"Shugabannin Tsaro Na NATO Sun Zabi Carsten Breuer A Matsayin Shugaba"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>An zabi Janar Carsten Breuer babban hafsan sojin kasar Jamus a matsayin shugaban Kwamitin Soji na kungiyar NATO wanda shi ne babban matsayin jagorancin soji a kungiyar.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Kasashe 32 mambobin NATO ne suka zabi Breuer a matsayin shugaba mai zuwa yayin wani taro a Copenhagen kamar yadda shugaban kwamitin mai ci yanzu Admiral Giuseppe Cavo Dragone na Italiya ya bayyana a shafinsa na X.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> Breuer zai karbi mukamin a lokacin bazara mai zuwa inda zai maye gurbin Dragone. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">&#8220;Kwarewarka wajen yanke hukunci kan ayyukan soji da zurfin sanin da kake da shi game da wannan kungiya da kuma yadda ka jagoranci rundunar sojin Jamus za su amfani NATO sosai&#8221; in ji Dragone. <\/span><\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">&#8220;Shugabannin soji sun dora maka amana a wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga tsaron yankin Turai da Atlantic&#8221; <\/span><\/em><span class=\"s1\">ya kara da cewa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"> Kwamitin Soji yana ba wa shugabannin siyasa na NATO shawara kan batutuwan da suka shafi soji inda shugaban kwamitin ke zama babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Babban Sakatare Mark Rutte.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Jirgin Yakin NATO Ya Harbo Jirgin Mara Matuki a Sararin Saman Romania <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Breuer zai karbi mukamin ne a daidai lokacin da NATO ke sake duba yadda ake raba nauyin ayyukan tsaro tsakanin Amurka da kawayenta na Turai. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen Turai mambobin kungiyar da su dauki karin nauyi wajen tabbatar da tsaron nahiyar.<br \/>\n<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Gwamnatocin kasashen Turai sun kara kashe kudade a fannin tsaro sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a shekarar 2022 da kuma rashin tabbas game da irin gudummawar da Amurka za ta ci gaba da bayarwa ga NATO a nan gaba. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Jamus na daya daga cikin kasashen da suka fi kashe kudade a wannan fanni inda Berlin ke shirin ninka kudaden da take kashewa a fannin tsaro zuwa sama da Yuro biliyan 200 (dalar Amurka biliyan 230) nan da shekarar 2030.<br \/>\n<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Breuer mai shekaru 61 ya shiga rundunar sojin Jamus (Bundeswehr) a shekarar 1984 a matsayin jami&#8217;in tsaron sararin sama. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga baya ya halarci Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soji ta Amurka (US Army Command and General Staff College) da ke Fort Leavenworth Kansas da kuma horon manyan hafsoshin soji na Jamus a Hamburg. Ya yi aiki tare da Rundunar NATO ta Kasa da Kasa mai kula da Tsaro da Samar da Zaman Lafiya (ISAF) a Kabul a shekarar 2014. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Breuer ya samu lakabin &#8220;<em>janar din shugaban gwamnati&#8221;<\/em> (chancellor\u2019s general) bayan da Olaf Scholz wanda shi ne shugaban gwamnati a lokacin ya nada shi shugaban kwamitin da ke kula da matakan da Jamus ta dauka wajen tunkarar annobar COVID-19 a shekarun 2021 da 2022. <\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ana sa ran Lieutenant General Christian Freuding wanda shi ne babban hafsan sojin kasa na Jamus a yanzu zai maye gurbin Breuer a matsayin babban hafsan soji kafin karshen wannan shekara.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An zabi Janar Carsten Breuer babban hafsan sojin kasar Jamus a matsayin shugaban Kwamitin Soji na kungiyar NATO wanda shi ne babban matsayin jagorancin soji a kungiyar. Kasashe 32 mambobin NATO ne suka zabi Breuer a matsayin shugaba mai zuwa yayin wani taro a Copenhagen kamar yadda shugaban kwamitin mai ci yanzu Admiral Giuseppe Cavo &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4240,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-4237","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4237","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4237"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4237\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4239,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4237\/revisions\/4239"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4240"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4237"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4237"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4237"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}