{"id":4193,"date":"2026-09-19T12:37:52","date_gmt":"2026-09-19T12:37:52","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4193"},"modified":"2026-09-19T12:37:52","modified_gmt":"2026-09-19T12:37:52","slug":"yan-sandan-gombe-sun-%c6%99arfafa-tsaro-gabanin-za%c9%93en-cike-gurbi-na-mazabar-tarayya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/19\/yan-sandan-gombe-sun-%c6%99arfafa-tsaro-gabanin-za%c9%93en-cike-gurbi-na-mazabar-tarayya\/","title":{"rendered":"Yan sandan Gombe sun \u0199arfafa tsaro gabanin za\u0253en cike gurbi na mazabar tarayya."},"content":{"rendered":"<p><strong>Rundunar &#8216;Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da daukar cikakkun matakan tsaro gabanin zaben cike-gurbi na mazabar Tarayya ta Gombe Kwami Funakaye wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 19 ga watan Satumbar 2026.<\/strong><\/p>\n<p>Rundunar ta bayyana cewa ta tura isassun jami&#8217;ai da kayan aiki zuwa ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cibiyoyin tattara sakamakon zabe rumfunan zabe da sauran muhimman wurare a kananan hukumomi ukun da abin ya shafa.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa Kwamishinan &#8216;Yan Sanda na Jihar Gombe CP Umar Ahmed Chuso ya bayyana cewa ana gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwar mambobin Kwamitin Tuntu\u0253a na Hukumomi daban-daban kan Tsaron Zabe (ICCES) domin tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana kafin yayin da kuma bayan kammala kada kuri&#8217;a.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: INEC ta Kara Kaimi Wajen Shirye-Shiryen Karshe Na Za\u0253en Cike Gurbi A Gombe.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa za a takaita zirga-zirga da harkokin kasuwanci a kananan hukumomin Gombe Kwami da Funakaye daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma a ranar Asabar ban da ayyukan da suka zama dole a matsayin wani bangare na matakan tsaro.<\/p>\n<p>Kwamishinan &#8216;yan sandan ya ce ba za a bai wa ma&#8217;aikatan da ke gudanar da ayyukan da suka zama dole damar amfani da kararrawar gaggawa (siren) motocin da ba su da rajista ko motocin da aka rufe lambobin rajistarsu ba.<\/p>\n<p>Hukumar ta kuma fayyace cewa hukumomin tsaro na gwamnati da ke aiki karkashin tsarin ICCES ne kawai za su samu izinin samar da tsaro yayin zaben.<\/p>\n<p>Ta kuma bayyana cewa an cire kungiyoyin tsaro na jiha kungiyoyin da ke taimakawa wajen tsaro masu gadin kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin sa kai (vigilante) daga ayyukan tsaron zaben.<\/p>\n<p>&#8216;Yan sandan sun yi gargadi game da yada labaran karya ayyukan &#8216;yan daba na siyasa da sauran ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama&#8217;a yayin zaben.<\/p>\n<p>Sun kuma yi gargadin cewa ba za a amince da nuna makamai ko mallakar abubuwan da za su iya haifar da tuhuma a wuraren kada kuri&#8217;a ba.<\/p>\n<p>Rundunar &#8216;Yan sandan Jihar Gombe ta bukaci iyaye da masu kula da yara da su yi taka-tsantsan ga &#8216;yan uwansu da ke barin a dauke su aiki ko kuma a yi amfani da su a matsayin &#8216;yan daba na siyasa.<\/p>\n<p>A cewar rundunar duk wanda aka samu yana aikata ayyukan da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.<\/p>\n<p>&#8216;Yan sandan sun kuma bukaci mazauna yankin da su hada kai da hukumomin tsaro tare da kai rahoton ayyukan da ake zargi ga ofishin &#8216;yan sanda mafi kusa ko ta hanyar lambobin gaggawa na rundunar: 0815 056 7771 da 0903 643 5359.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar &#8216;Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da daukar cikakkun matakan tsaro gabanin zaben cike-gurbi na mazabar Tarayya ta Gombe Kwami Funakaye wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 19 ga watan Satumbar 2026. Rundunar ta bayyana cewa ta tura isassun jami&#8217;ai da kayan aiki zuwa ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4196,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[79,61,78],"class_list":["post-4193","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics","tag-gombe-state","tag-inec","tag-npf"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4193","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4193"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4193\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4199,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4193\/revisions\/4199"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4196"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4193"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4193"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4193"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}