{"id":4183,"date":"2026-09-19T11:57:54","date_gmt":"2026-09-19T11:57:54","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4183"},"modified":"2026-09-19T11:57:54","modified_gmt":"2026-09-19T11:57:54","slug":"amurka-da-denmark-sun-cimma-yarjejeniya-kan-kasancewar-sojojin-amurka-a-greenland","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/19\/amurka-da-denmark-sun-cimma-yarjejeniya-kan-kasancewar-sojojin-amurka-a-greenland\/","title":{"rendered":"Amurka Da Denmark Sun Cimma Yarjejeniya Kan Kasancewar Sojojin Amurka A Greenland."},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka Denmark da Greenland sun cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Washington damar fadada kasancewar sojojinta a tsibirin, tare da hana abokan g\u0101ban Amurka kafa sansanonin soji a wurin.<\/strong><\/p>\n<p>Ya bayyana hakan ne a ranar Juma&#8217;a ta hanyar wani sako a shafinsa na Truth Social inda ya ce yarjejeniyar tana bai wa Amurka damar samun damar shiga kafa sansani da kuma ha\u0199\u0199in tashi a sararin samaniyar Greenland har abada.<\/p>\n<p>Trump ya ce yarjejeniyar ba ta da wa&#8217;adin karewa inda ya kwatanta ta a matsayin &#8220;<em>cikar burin Amurka.<\/em>&#8221;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta kafa babban karfin soji a tsibirin wanda tuni yake dauke da sansanin Rundunar Sojin Sama da Sararin Samaniya ta Amurka (US Space Force) a arewa maso yammacin Greenland.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Babu Ja Da Baya Kan Batun Greenland \u2013 Shugaba Trump<\/p>\n<p>Wannan yarjejeniya ta sha bamban da kiran da Trump ya yi a baya na cewa Amurka ta mallaki Greenland wadda yanki ce mai cin gashin kanta ta kasar Denmark.<\/p>\n<p>Tuni Amurka ta samu damar tashi a sararin samaniyar Greenland da kuma kafa sansanonin soja a can bisa wata yarjejeniyar tsaro da aka kulla da Denmark a shekarar 1951.<\/p>\n<p>Ofishin Firayim Ministan Denmark ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta karfafa tsaro a yankunan Arewacin Tekun Atlantika da kuma yankin Arctic.<\/p>\n<p>Firayim Ministan Greenland Jens-Frederik Nielsen ya ce yarjejeniyar ta yi la&#8217;akari da muradun Greenland da kuma matsayinta a fannin hadin gwiwar kasa da kasa.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Wannan yana amfanar mu duka&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Sai dai ba a bayyana cikakkun bayanai game da yarjejeniyar ba ciki har da ko za a gina sabbin sansanonin sojan Amurka a tsibirin.<\/p>\n<p>Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce yarjejeniyar ta magance damuwar tsaron Amurka game da Greenland &#8220;<em>gaba daya kuma har abada.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Rubio ya kara da cewa Greenland za ta ci gaba da kasancewa cikin yankin tsaro mai muhimmanci na Arewacin Amurka kuma za a hana abokan gaba shiga yankin da ke kewaye da tsibirin.<\/p>\n<p>Wani jami&#8217;in Ma&#8217;aikatar Harkokin Wajen Amurka ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta haramta wa kasashen da ba sa cikin kungiyar NATO gina sansanonin soja a Greenland lamarin da ke bai wa Amurka da kawayenta damar gudanar da wasu muhimman ayyukan zuba jari na musamman wadanda ba a bayyana cikakkun bayanansu ba.<\/p>\n<p>Jami&#8217;in ya kara da cewa yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki ko da Greenland ta samu &#8216;yancin kai.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka Denmark da Greenland sun cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Washington damar fadada kasancewar sojojinta a tsibirin, tare da hana abokan g\u0101ban Amurka kafa sansanonin soji a wurin. Ya bayyana hakan ne a ranar Juma&#8217;a ta hanyar wani sako a shafinsa na Truth Social inda ya &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4186,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-4183","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4183","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4183"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4183\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4187,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4183\/revisions\/4187"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4186"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4183"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4183"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4183"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}