{"id":4169,"date":"2026-09-19T10:34:53","date_gmt":"2026-09-19T10:34:53","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4169"},"modified":"2026-09-19T10:34:53","modified_gmt":"2026-09-19T10:34:53","slug":"gwamnatin-najeriya-na-gudanar-da-bincike-kan-mutuwar-mutane-37-a-hannun-hukumar-nscdc","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/19\/gwamnatin-najeriya-na-gudanar-da-bincike-kan-mutuwar-mutane-37-a-hannun-hukumar-nscdc\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Najeriya Na gudanar Da Bincike Kan Mutuwar Mutane 37 A Hannun Hukumar NSCDC."},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa mai mutane 10 domin gudanar da bincike kan rahoton mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Neja wadanda ake zargi da hannu cikin hakar ma&#8217;adinai ba bisa ka&#8217;ida ba.<\/strong><\/p>\n<p>An dora wa kwamitin alhakin gano\u00a0 wadanda suka mutu din da kuma bincikar yanayin da ya shafi kama su tsare su da kuma mutuwar tasu tare da tantance ko akwai wani da ke da alhaki hannu ko kuma ya nuna sakaci ko rashin da&#8217;a dangane da wannan lamari.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Asabar Ministan Harkokin Cikin Gida Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da kafa kwamitin biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na gudanar da cikakken bincike mai zurfi wanda ke nuna gaskiya da kuma rashin cikas kan lamarin mutuwar mutanen.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya Ta Goyi Bayan Jami&#8217;an Hako Ma&#8217;adinai Ta Yi Garga\u0257i Ga Masu Hako Ma&#8217;adinai Ba Bisa Ka&#8217;ida Ba<\/p>\n<p>Tunji-Ojo ya kuma bayar da umarnin dakatar da dukkan jami&#8217;an da ke da hannu a cikin lamarin har sai an kammala bincike ciki har da Kwamandan hukumar NSCDC na Jihar Neja da wasu jami&#8217;ai 20 da ma&#8217;aikatar ta fitar da sunayensu da mukamansu.<\/p>\n<p>Yayin da yake bayyana mutuwar mutanen a matsayin abin takaici da damuwa matuka ministan ya ce gwamnatin Najeriya na da nauyin bayar da cikakken bayani mai gamsarwa da kuma nuna gaskiya game da lamarin ga iyalan wadanda suka rasu da kuma sauran &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p>Jonathan Kure tsohon Mataimakin Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) shi ne zai jagoranci kwamitin yayin da tsohon Darakta-Janar na Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya (Nigerian Law School) Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN) zai yi aiki a matsayin sakatare.<\/p>\n<p>Sauran mambobin sun hada da tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na &#8216;Yan Sanda Hosea Hassan Karma Farfesa a fannin Histopathology kuma tsohon Babban Daraktan Lafiya na Asibitin Koyarwa na Jami&#8217;ar Ilorin Olayinka Buhari wakilan Majalisar Masarautar Minna da Gwamnatin Jihar Neja Sakataren Kungiyar Masu Hakar Ma&#8217;adinai ta Kasa Liman Sulaiman lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam Deji Adeyanju Hajiya Zainab Suleiman Okino daga jaridar Blueprint da kuma mai sharhi kan al&#8217;amuran yau da kullum Dr. George Agbakahi.<\/p>\n<p>An kuma umurci kwamitin da ya ba da shawarar daukar matakin da ya dace a kan duk wanda aka samu da laifi ya tantance yiwuwar diyya idan ya dace sannan ya gabatar da matakan da za a dauka don hana sake afkuwar lamarin.<\/p>\n<p>A cewar ministan kwamitin zai iya hada kwararrun da suka dace ya sami damar shiga wuraren da suka dace da takardu ya ziyarci wuraren da abin ya shafa sannan ya karbi takardun shaida daga jama&#8217;a.<\/p>\n<p>Tunji-Ojo ya umurci shugabannin NSCDC da dukkan jami&#8217;an da abin ya shafa da su hada kai sosai wajen binciken sannan su tabbatar da cewa an adana bayanai da shaidun da suka shafi lamarin kuma an bai wa masu bincike damar yin hakan.<\/p>\n<p>Ya yi gargadin cewa duk wani yunkurin lalata ko boye shaida tsoratar da shaidu ko kawo cikas ga binciken za a dauki shi a matsayin babban laifi.<\/p>\n<p>Kwamitin yana da makonni biyu don kammala bincikensa da kuma mika rahotonsa ga ministan.<\/p>\n<p>Tunji-Ojo ya kuma mika ta&#8217;aziyya ga iyalan mamatan sannan ya yi kira da a kwantar da hankali yayin da ake ci gaba da binciken.<\/p>\n<p>A ranar Juma&#8217;a ne Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan kama mutanen yanayin tsare su kulawar lafiya da aka bayar da kuma abubuwan da suka haifar da mutuwar.<\/p>\n<p>Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 17 ga Satumba wanda ya shafi mutanen da rundunar NSCDC ta jihar Neja ta tsare bisa zargin hakar ma&#8217;adinai ba bisa ka&#8217;ida ba.<\/p>\n<p>Daga baya Ministan Harkokin Cikin Gida ya jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya zuwa jihar Neja kan mutuwar wanda aka ruwaito cewa ya shafi ma&#8217;aikatan hakar ma&#8217;adinai 37.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa mai mutane 10 domin gudanar da bincike kan rahoton mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Neja wadanda ake zargi da hannu cikin hakar ma&#8217;adinai ba bisa ka&#8217;ida ba. An dora wa kwamitin alhakin gano\u00a0 wadanda suka mutu din &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4172,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[72,73],"class_list":["post-4169","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","tag-niger-state","tag-nigerian-government"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4169","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4169"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4169\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4173,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4169\/revisions\/4173"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4172"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4169"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4169"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4169"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}