{"id":4139,"date":"2026-09-18T15:52:10","date_gmt":"2026-09-18T15:52:10","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4139"},"modified":"2026-09-18T15:52:10","modified_gmt":"2026-09-18T15:52:10","slug":"shugabannin-apc-adc-ndc-sun-ziyarci-zamfara-domin-taaziyyar-yari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/18\/shugabannin-apc-adc-ndc-sun-ziyarci-zamfara-domin-taaziyyar-yari\/","title":{"rendered":"Shugabannin APC ADC NDC Sun Ziyarci Zamfara Domin Ta&#8217;aziyyar Yari"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong>Manyan &#8216;yan siyasa daga jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran jam&#8217;iyyun adawa sun hallara a Talata Mafara Jihar Zamfara domin yin\u00a0 ta&#8217;aziyya ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam&#8217;iyyar APC Sanata Abdulaziz Abubakar Yari bisa rasuwar kanwar mahaifiyarsa Hajiya Rukiya Jibril.<\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wannan ziyarar ta&#8217;aziyya ta hada manyan jami&#8217;an gwamnatin tarayya shugabannin jam&#8217;iyyar APC da fitattun &#8216;yan siyasar adawa lamarin da ya nuna yadda aka samu wakilcin bangarorin siyasa daban-daban a wurin zaman makokin iyalin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Sanata George Akume wanda ya isar da sakon ta&#8217;aziyyar Shugaba Bola Tinubu ga Yari da iyalansa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Akume ya tabbatar wa iyalin mamaciyar cewa ba su kadai ba ne a wannan lokaci na bakin ciki inda ya bayyana mutuwa a matsayin wani mataki na sauyi da komawa ga Allah bisa ga nufinsa da hikimarsa.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya bukaci iyalin su samu karfin gwiwa daga imaninsu da kuma sanin cewa mamaciyar ta kammala tafiyarta a duniya tare da komawa ga Mahaliccinta.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA:<a href=\"http:\/\/Zamfara na Neman Asusun Tallafawa Wadanda Rikici ya Shafa Domin Gina Zaman Lafiya\">http:\/\/Zamfara na Neman Asusun Tallafawa Wadanda Rikici ya Shafa Domin Gina Zaman Lafiya<\/a><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sakataren Gwamnatin Tarayya ya yi addu&#8217;ar Allah ya gafarta wa Hajiya Rukiya tare da yi mata rahama ya karbi ayyukanta na kwarai ya kuma sanya ta cikin bayin Allah na kwarai.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Yayin karbar tawagar Yari ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa nuna damuwa da goyon baya ga iyalin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya kuma gode wa Akume da sauran mambobin tawagar bisa tafiyar da suka yi zuwa Talata Mafara domin girmama mamaciyar da kuma taya iyalin zaman makokin.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Samun Nutsuwa da Karfin Gwiwa<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\">Yari ya bayyana cewa ziyarar ta ba shi da iyalinsa nutsuwa karfin gwiwa da kuma juriya yayin da yake yi wa Shugaban kasa SGF da mambobin tawagar addu&#8217;ar ci gaba da samun shiriyar Allah da albarkarsa.<\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya su rika tunawa da goggonsa a cikin addu&#8217;o&#8217;insu tare da neman Allah ya gafarta mata ya yi mata rahama ya kuma sanya ruhinta ya huta cikin kwanciyar hankali.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga cikin wadanda suka raka Akume akwai Gwamnan Jihar Neja Umar Bago Sakataren Jam&#8217;iyyar APC na kasa Sanata Ajibola Bashiru tsohon Gwamnan Jihar Imo Sanata Rochas Okorocha da tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Taron ya kuma samu halartar fitattun mutane daga jam&#8217;iyyun siyasa na adawa. Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal tare da rakiyar Sanata Abdul Ningi sun wakilci jam&#8217;iyyar African Democratic Congress (ADC) yayin da Sanata Tony Nwoye ya jagoranci tawagar jam&#8217;iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Hajiya Rukiya Jibril ita ce \u0199anwar mahaifiyar Sanata Yari ta jini.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Manyan &#8216;yan siyasa daga jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran jam&#8217;iyyun adawa sun hallara a Talata Mafara Jihar Zamfara domin yin\u00a0 ta&#8217;aziyya ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam&#8217;iyyar APC Sanata Abdulaziz Abubakar Yari bisa rasuwar kanwar mahaifiyarsa Hajiya Rukiya Jibril. Wannan ziyarar ta&#8217;aziyya ta &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4147,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-4139","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4139","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4139"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4139\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4148,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4139\/revisions\/4148"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4147"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4139"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4139"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4139"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}