{"id":4098,"date":"2026-09-17T13:51:04","date_gmt":"2026-09-17T13:51:04","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4098"},"modified":"2026-09-17T13:51:04","modified_gmt":"2026-09-17T13:51:04","slug":"maaikatar-ilimi-da-kungiyoyin-kwadago-za-su-sasanta-takaddamar-kwalejin-kings","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/17\/maaikatar-ilimi-da-kungiyoyin-kwadago-za-su-sasanta-takaddamar-kwalejin-kings\/","title":{"rendered":"Ma&#8217;aikatar Ilimi Da Kungiyoyin Kwadago Za Su Sasanta Takaddamar Kwalejin Kings"},"content":{"rendered":"<p><strong>Ma&#8217;aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya da kungiyoyin kwadago na ma&#8217;aikatar sun cimma yarjejeniya mai maki biyar domin warware takaddamar da ke tattare da shirin da ya shafi makarantar Kwalejin King\u2019s\u00a0 Legas.<\/strong><\/p>\n<p>An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro da aka gudanar a daren Laraba a Abuja tsakanin Ministocin Ilimi Dr. Tunji Alausa da Farfesa Suwaiba Ahmad da wakilan kungiyar hadin gwiwar ma&#8217;aikata (Kugiyar\u00a0 Ma&#8217;aikata Ta Hadin Gwuiwa) da kuma kungiyar manyan ma&#8217;aikatan gwamnati ta Najeriya (ASCSN) na ma&#8217;aikatar.<\/p>\n<p>A karkashin yarjejeniyar ana sa ran kungiyoyin kwadagon za su dakatar nan take da yajin aikin da suke gudanarwa sakamakon damuwa game da shirin da ya shafi makarantar Kwalejin King\u2019s.<\/p>\n<p>Bangarorin sun kuma amince cewa ba za a hukunta ko daukar wani mataki na ramuwar gayya kan wani ma&#8217;aikaci ba saboda shiga yajin aikin.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar ta kuma amince da &#8220;<em>dakatar da aiwatar da shirin tsoffin daliban makarantar na karbar ragamar tafiyar da Kwaiejin King\u2019s na tsawon makonni biyu.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Wani mataki da aka cimma a taron shi ne janye &#8216;yan sandan da ke harabar makarantar King\u2019s Kwalej domin samar da yanayi mai kyau na ci gaba da tattaunawa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Ministan Ilimi Ya Garga\u0257i Cibiyoyin Ilimi Kan Zamba Cikin Amincewa<\/p>\n<p>Har ila yau taron ya amince da kafa kwamiti mai mambobi bakwai domin tattaunawa da kuma nazarin yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta kulla da Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar King\u2019s Kwalej (KCOBA).<\/p>\n<p>Ana sa ran kwamitin zai yi nazarin yarjejeniyar ya kuma duba damuwar da kungiyoyin kwadago suka bayyana tare da tunkarar batutuwan da suka taso dangane da tsarin da aka gabatar game da makarantar.<\/p>\n<p>Manufar wadannan matakai ita ce samar da damar ci gaba da tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago domin warware takaddamar da ke tattare da makarantar King\u2019s Kwalej.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ma&#8217;aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya da kungiyoyin kwadago na ma&#8217;aikatar sun cimma yarjejeniya mai maki biyar domin warware takaddamar da ke tattare da shirin da ya shafi makarantar Kwalejin King\u2019s\u00a0 Legas. An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro da aka gudanar a daren Laraba a Abuja tsakanin Ministocin Ilimi Dr. Tunji Alausa da Farfesa &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4101,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[71],"class_list":["post-4098","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","tag-ilimi"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4098","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4098"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4098\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4103,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4098\/revisions\/4103"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4101"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4098"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4098"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4098"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}