{"id":4093,"date":"2026-09-17T13:11:10","date_gmt":"2026-09-17T13:11:10","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=4093"},"modified":"2026-09-17T13:11:10","modified_gmt":"2026-09-17T13:11:10","slug":"jibrin-ya-yi-kira-ga-gwamnonin-apc-su-tattauna-da-wike","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/17\/jibrin-ya-yi-kira-ga-gwamnonin-apc-su-tattauna-da-wike\/","title":{"rendered":"Jibrin Ya Yi Kira Ga Gwamnonin APC Su Tattauna Da Wike."},"content":{"rendered":"<p><strong>Wani jigo a jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) kuma dan majalisar tarayya Abdulmumin Jibrin ya yi kira ga shugabannin jam&#8217;iyyar da gwamnoni da su tattauna da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike game da ayyukansa na siyasa yayin da ake shirin zaben shekarar 2027<\/strong>.<\/p>\n<p>Jibrin ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Abuja dangane da sukar da wasu gwamnonin APC suka yi wa shirin Wike na kafa kawancen siyasa mai suna &#8216;Rainbow Coalition&#8217;.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa Wike ya bayar da gudunmawa wajen samun goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu duk da cewa har yanzu yana cikin jam&#8217;iyyar Peoples Democratic Party (PDP).<\/p>\n<p>&#8220;<em>Babu wani dan jam&#8217;iyyar APC a Najeriya a yau da bai ci gajiyar kokarin Wike ba kai tsaye ko a kaikaice muddin dai yana taimakawa wajen samun nasarar Shugaban kasa yana gudanar da harkokin gwamnati tare da sauke nauyin ayyukansa<\/em>&#8221; in ji Jibrin.<\/p>\n<p>Ya bayyana Wike a matsayin mutum mai matukar muhimmanci ga jam&#8217;iyya mai mulki tare da ba da shawarar cewa kada a rika sukar sa a bainar jama&#8217;a.<\/p>\n<p><em>&#8220;Wike babban karfi ne ga jam&#8217;iyyar APC. Ba na ganin ya kamata a kunyata Wike a wannan lokaci ta hanyar bayyana kalamai a bainar jama&#8217;a<\/em>&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Jibrin ya bayyana cewa matakin da ya dauka na shiga cikin lamarin ba ya samo asali ne daga kusancin sirri da ke tsakaninsa da Wike ba sai dai saboda damuwarsa kan ci gaba da samun goyon baya ga Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Sau biyu kawai na taba haduwa da shi ba tare da shiri ba don haka ba wai ina kare Wike ba ne. Amma duk lokacin da aka samu wani abu da zai shafi kwanciyar hankalin tafiyar tabbatar da nasarar Shugaban kasa ina son shiga cikin lamarin domin bayar da tawa gudummawar<\/em>&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Dan majalisar ya kuma yi ikirarin cewa Wike ya yi wasu sadaukarwa na siyasa domin goyon bayan jam&#8217;iyyar APC ciki har da a Jihar Ribas da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).<\/p>\n<p>\u201c<em>Na yi imani cewa Wike ya yi sadaukarwa. Ya mika jihar Ribas ga jam&#8217;iyyar APC. Wike yana da &#8216;yan takara a zaben FCT amma ya bukace su da su janye domin bai wa APC damar nasara. Wike ya shiga wannan gwamnati ne a matsayin gwamnatin hadin kan kasa. A zahiri ya kamata mu yi masa adalci ya yi abubuwa da yawa fiye da haka<\/em>\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Jibrin ya bayyana cewa &#8216;yan siyasa na wasu jam&#8217;iyyu na iya goyon bayan dan takarar shugaban kasa ba tare da sun shiga jam&#8217;iyyar dan takarar a hukumance ba.<\/p>\n<p>\u201c<em>Akwai mutanen da ke wasu jam&#8217;iyyu wadanda ke aiki tare da mu a NDC da ADC. Wasu daga cikinsu sun kira ni jiya suna cewa Ka ga abin da ake cewa game da Wike<\/em>\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Ya bukaci gwamnonin APC masu damuwa game da ayyukan Wike da su tattauna da shi kai tsaye maimakon yin maganganu a bainar jama&#8217;a.<\/p>\n<p>\u201c<em>Idan akwai matsala a matakin jiha ya kamata a tuna cewa dukkan wannan hadin gwiwa da yake yi domin Shugaban kasa ne. Idan wani a matakin jiha ya ga hakan na iya zama barazana a gare shi ko ga muradunsa, ya kamata ya tattauna da Wike<\/em>\u201d cewar Jibrin.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa a ganinsa ci gaban kasancewar Wike a jam&#8217;iyyar PDP tare da goyon bayan sake zaben Tinubu bai kamata ya zama cikas ga hadin gwiwar siyasa ba.<\/p>\n<p>Kalaman na Jibrin sun biyo bayan sukar da wasu gwamnonin APC suka yi kwanan nan kan ayyukan hadin gwiwar siyasa da Wike ke jagoranta ciki har da gwamnan jihar Kwara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wani jigo a jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) kuma dan majalisar tarayya Abdulmumin Jibrin ya yi kira ga shugabannin jam&#8217;iyyar da gwamnoni da su tattauna da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike game da ayyukansa na siyasa yayin da ake shirin zaben shekarar 2027. Jibrin ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4096,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[70],"class_list":["post-4093","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics","tag-apc"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4093","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4093"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4093\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4097,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4093\/revisions\/4097"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4096"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4093"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4093"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4093"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}