{"id":3933,"date":"2026-09-14T12:03:00","date_gmt":"2026-09-14T12:03:00","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3933"},"modified":"2026-09-14T12:03:00","modified_gmt":"2026-09-14T12:03:00","slug":"fiye-da-mutane-2000-daga-yemen-da-suka-rasa-muhallansu-sun-isa-djibouti","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/14\/fiye-da-mutane-2000-daga-yemen-da-suka-rasa-muhallansu-sun-isa-djibouti\/","title":{"rendered":"Fiye Da Mutane 2,000 Daga Yemen Da Suka Rasa Muhallansu Sun Isa Djibouti."},"content":{"rendered":"<p><strong>Mutane sama da 2,000 da ke tserewa daga sabon rikici a Yemen sun isa Djibouti a cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM).<\/strong><\/p>\n<p>Zuwan wadannan mutane ya biyo bayan kwace wani muhimmin birni mai tashar jiragen ruwa a gabar tekun yammacin Yemen da kuma wani tsibiri a mashigar ruwa ta Bab el-Mandeb da &#8216;yan tawayen Houthi wadanda Iran ke goyon baya suka yi a makon da ya gabata.<\/p>\n<p>Wannan karuwar rikici ta haifar da fargabar komawa ga cikakken yakin basasa, lamarin da ya tilastawa dubban mazauna yankin barin gidajensu.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin wadanda suka rasa muhallansu sun tsallaka mashigar ruwa ta Bab el-Mandeb zuwa Djibouti wadda ke da nisan kilomita 30 daga Yemen.<\/p>\n<p>Jami&#8217;an Djibouti sun bayyana cewa rundunar sojin ruwa, da masu tsaron gabar teku, da sauran hukumomi suna gudanar da ayyukan ceto a mashigar ruwan tare da samar da tallafin gaggawa ga wadanda suka isa kasar.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA:\u00a0<a href=\"http:\/\/Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na neman dala biliyan 1 domin tunkarar gaggawa ta fannin lafiya a duniya\">http:\/\/Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na neman dala biliyan 1 domin tunkarar gaggawa ta fannin lafiya a duniya<\/a><\/p>\n<p>Daya daga cikin wadanda suka rasa muhallansu, Hussein Haydara, wanda ya tsere daga birnin Hodeidah ya ce wannan shi ne karo na biyu da aka tilasta masa barin gidansa.<\/p>\n<p>Haydara ya ce wannan gudun hijira na baya-bayan nan ya zo ba-zata inda ya bar iyalai da dan lokaci kadan na tattara kayansu yayin da suke tserewa daga harin bama-bamai da harbin bindiga daga maharba.<\/p>\n<p>Hukumar IOM ta bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon sabon rikicin Yemen ya kai kusan 86,000 inda sama da mutane 82,000 suka rasa muhallansu tun farkon watan Satumba.<\/p>\n<p>Wannan karuwar rikici ta kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka dade ana kiyayewa tun shekarar 2022 bayan shekaru da dama na yakin basasa a kasar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mutane sama da 2,000 da ke tserewa daga sabon rikici a Yemen sun isa Djibouti a cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM). Zuwan wadannan mutane ya biyo bayan kwace wani muhimmin birni mai tashar jiragen ruwa a gabar tekun yammacin Yemen da kuma wani tsibiri a mashigar ruwa ta Bab el-Mandeb da &#8216;yan &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":3936,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[59],"class_list":["post-3933","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news","tag-djibouti"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3933","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3933"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3933\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3937,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3933\/revisions\/3937"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3936"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3933"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3933"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3933"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}