{"id":3713,"date":"2026-09-08T11:31:46","date_gmt":"2026-09-08T11:31:46","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3713"},"modified":"2026-09-08T11:31:46","modified_gmt":"2026-09-08T11:31:46","slug":"burundi-ta-yi-allah-wadai-da-tashin-hankali-yayin-da-yan-kasarta-ke-barin-kenya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/09\/08\/burundi-ta-yi-allah-wadai-da-tashin-hankali-yayin-da-yan-kasarta-ke-barin-kenya\/","title":{"rendered":"Burundi Ta Yi Allah-Wadai Da Tashin Hankali Yayin Da &#8216;Yan Kasarta Ke Barin Kenya"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daruruwan &#8216;yan Burundi da ke zaune a Kenya sun yi layi a ofishin jakadancinsu da ke Nairobi don samun takardun tafiya bayan Shugaba William Ruto ya umarci a rufe \u0199ananan kasuwancin da ke mallakar \u0199asashen waje.<\/strong><\/p>\n<p>Wannan matakin ya haifar da fargaba a tsakanin &#8216;yan kasuwa na \u0199asashen waje, musamman &#8216;yan Burundi wa\u0257anda ke samun abin rayuwa ta hanyar sayar da kayayyaki a titi a Nairobi wanda hakan ya sa wasu suka shirya komawa gida.<\/p>\n<p>Kenya ta da\u0257e tana jan hankalin &#8216;yan cirani daga ko&#8217;ina cikin \u0198ungiyar Gabashin Afirka (EAC) wa\u0257anda membobinsu ke jin da\u0257in &#8216;yancin yin tafiya a cikin \u0199ungiyar yankin.<\/p>\n<p>A makon da ya gabata, Ruto ya bai wa \u0199ananan kasuwancin da ke mallakar \u0199asashen waje har zuwa ranar Litinin da su rufe, yana mai cewa Kenya <em>&#8220;ba ta gina kwarin gwiwar masu zuba jari ga masu talla ba.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Tana ri\u0199e manyan ambulan launin ruwan kasa jama&#8217;a sun yi layi na tsawon sa&#8217;o&#8217;i a wajen ofishin jakadancin Burundi yayin da jakunkuna da jakunkunan filastik suka taru a harabar.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Burundi Ta Sake Tabbatar da Al\u0199awarin \u0198arfafa Ha\u0257in gwiwa da Najeriya<\/p>\n<p><em>&#8220;Sun kore mu kamar dabbobi&#8221;<\/em> in ji Fasto Jean-Baptiste Ndayizeye.Ndayizeye ya bayyana cewa an kai wa biyu daga cikin makwabtansa hari tare da yi musu fashi inda ya kwatanta lamarin da tashe-tashen hankulan nuna kyama ga baki da ke faruwa a Afirka ta Kudu.<\/p>\n<p><em>&#8220;Abin da &#8216;yan Afirka ta Kudu suka yi wa baki da kuma abin da &#8216;yan Kenya ke yi, abu daya ne&#8221;<\/em> in ji shi tare da kara da cewa rashin ba su wani gargadi kafin hakan ya faru, rashin adalci ne.<\/p>\n<p>Wani dan kasar Burundi, Eric Bizimana, wanda ya isa Kenya a shekarar 2022 bayan ya shafe shekaru ba tare da aiki a kasarsa ba ya ce bai taba neman izinin aiki ba saboda tsadar kudin da ake bukata.<\/p>\n<p><em>&#8220;Suna cikin matukar bakin ciki&#8221;<\/em> na barin Kenya in ji Philemon Jaika Adamba, direban babur mai safarar fasinjoji (boda) dan kasar Kenya wanda ya kai wasu &#8216;yan kasar Burundi biyu zuwa ofishin jakadancin kasarsu. <em>&#8220;Ba adalci ba ne.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>&#8216;An yi rashin fahimta&#8217;<\/p>\n<p>Burundi kasa mai yawan jama&#8217;a kimanin miliyan 15 mamba ce a kungiyar EAC tare da Kenya wadda ita ce babbar kasa ta fuskar tattalin arziki a yankin.<\/p>\n<p>Ministan Harkokin Wajen Burundi Edouard Bizimana ya yi Allah-wadai da rahotannin tashe-tashen hankula da ake kai wa baki hari musamman &#8216;yan kasar Burundi.<\/p>\n<p><em>&#8220;Gwamnatin Kenya ce ke da alhakin kare rayuwar &#8216;yan kasar Burundi da ke zaune a Kenya.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em>&#8220;Barin fararen hula a Kenya su rika gudanar da ayyukan &#8216;yan sanda na ba da hoton kasa da ta gaza domin hakan na bude kofa ga tashe-tashen hankula fashi da garkuwa da dukiya da kuma nuna kyama ga baki&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Karamin Ministan Harkokin Wajen Kenya Korir Sing\u2019Oei ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Burundi a ranar Litinin inda ya nemi afuwar &#8216;yan kasar Burundi tare da ba su tabbacin cewa &#8216;yan sanda za su kare yankunan da aka samu rahoton tashe-tashen hankali.<\/p>\n<p>Sing\u2019Oei ya bayyana cewa an <em>&#8220;fahimci kalaman shugaban kasar ba daidai ba.&#8221;<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Sakamakon rashin fahimtar juna mutane da yawa sun fuskanci hare-hare daga makwabtansu da kuma abokansu&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p><em>&#8220;Babban burinmu shi ne mu san halin da kuke ciki da inda kuke zaune da kuma tabbatar da cewa kuna da takardun shaida tare da yin rajistar ayyukanku&#8221;<\/em> ya kara da cewa.<\/p>\n<p>Kakakin gwamnati Charles Owino ya bayyana cewa hukumomi sun bude shirin <em>&#8220;yin rajista da kuma tantance takardu a hukumance&#8221;<\/em> tare da yin kira ga &#8216;yan kasar Burundi da su gabatar da takardunsu a ofishin jakadancinsu.<\/p>\n<p><em>&#8220;Gwamnati ta fahimci cewa, saboda yanayin tarihi da kuma al&#8217;amuran da suka shafi yankin, akwai &#8216;yan kasashen Gabashin Afirka da dama ciki har da &#8216;yan kasar Burundi da yawa da ke zama da kuma gudanar da harkokinsu a Kenya ba tare da cikakkun takardu ba&#8221;<\/em> in ji Owino.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>AFP\/Africanews\/Ladan Nasidi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daruruwan &#8216;yan Burundi da ke zaune a Kenya sun yi layi a ofishin jakadancinsu da ke Nairobi don samun takardun tafiya bayan Shugaba William Ruto ya umarci a rufe \u0199ananan kasuwancin da ke mallakar \u0199asashen waje. Wannan matakin ya haifar da fargaba a tsakanin &#8216;yan kasuwa na \u0199asashen waje, musamman &#8216;yan Burundi wa\u0257anda ke samun &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3716,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-3713","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3713","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3713"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3713\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3717,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3713\/revisions\/3717"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3716"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3713"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3713"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3713"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}