{"id":3431,"date":"2026-08-31T14:14:05","date_gmt":"2026-08-31T14:14:05","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3431"},"modified":"2026-08-31T14:14:05","modified_gmt":"2026-08-31T14:14:05","slug":"shugaban-yan-adawar-zambia-na-fuskantar-zargin-cin-amanar-kasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/31\/shugaban-yan-adawar-zambia-na-fuskantar-zargin-cin-amanar-kasa\/","title":{"rendered":"Shugaban &#8216;Yan Adawar Zambia Na Fuskantar Zargin Cin Amanar Kasa"},"content":{"rendered":"<p><strong>An gurfanar da shugaban &#8216;yan adawar Zambia Brian Mundubile da tuhumar cin amanar kasa kuma yana ci gaba da zama a hannun &#8216;yan sanda tare da abokin takararsa a yayin da ake fama da tsananin tashin-tashinar siyasa a kasar.<\/strong><\/p>\n<p>An kama Mundubile ne a ranar Alhamis, bayan wani samame mai cike da tashin hankali da hukumomi suka kai wanda ya tilasta wa dan siyasar adawar boyewa.<\/p>\n<p>Ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan a kasar wanda ya bai wa shugaba mai ci Hakainde Hichilema damar lashe wa&#8217;adi na biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: An Rufe Kotunan Zambia a Ranar Karshe ta Kalubalantar Sakamakon Zabe<\/p>\n<p>Daga nan ne hukumomi suka zargi jam&#8217;iyyar Mundubile ta NRPUP da shirin tayar da kayar baya ta hanyar amfani da makamai zargin da jam&#8217;iyyar ta musanta.<\/p>\n<p>A daren Asabar lauyan Mundubile Milner Katolo ya sanar da cewa an tuhumi wanda yake karewa da laifin cin amanar kasa.<\/p>\n<p>Katolo ya shaida wa kafofin yada labarai na cikin gida cewa shugaban &#8216;yan adawar yana fatan amsa wannan tuhuma a gaban kotu.<\/p>\n<p>Lauyan ya ce an kuma tuhumi wasu mutane 17 da laifin cin amanar kasa ciki har da abokin takarar Mundubile Makebi Zulu.<\/p>\n<p>A cewar sakamakon hukuma Mundubile ya samu kashi 38 cikin 100 na kuri&#8217;u a zaben da aka gudanar a ranar 13 ga watan Agusta yayin da Hichilema ya samu kashi 60 cikin 100.<\/p>\n<p>Washegarin zaben jami&#8217;an tsaro sun kai samame a wani gida da ke da alaka da Mundubile a babban birnin kasar Lusaka inda suka kashe wani tsohon minista tare da kama wasu &#8216;yan siyasa da dama.<\/p>\n<p>Bayan samamen Mundubile da Zulu sun nemi mafaka a wani ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin. An tsare su ne bayan shugaban kasar ya matsa wa Majalisar Dinkin Duniya lamba kan ta mika su ga hukumomi.<\/p>\n<p>Jam&#8217;iyyar adawar ba ta samu damar kalubalantar sakamakon zaben a kotu ba kasancewar hukumomi sun rufe kotunan a ranar Litinin wadda ita ce ranar karshe ta shigar da kara.<\/p>\n<p>Ana sa ran za a rantsar da Hichilema domin fara wa&#8217;adinsa na biyu a ranar 1 ga watan Satumba.<\/p>\n<p>Masu sa ido na yankin da na kasa da kasa sun bayyana ranar zaben a matsayin mai cike da zaman lafiya amma Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Zambia ta yi kira da a dauki matakin gaskiya da bayyana halin da mutanen da ba a san inda suke ba bayan kama su da kuma ayyukan tsaro a lokacin zaben suke ciki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>BBC\/Safina Umar Farouk.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An gurfanar da shugaban &#8216;yan adawar Zambia Brian Mundubile da tuhumar cin amanar kasa kuma yana ci gaba da zama a hannun &#8216;yan sanda tare da abokin takararsa a yayin da ake fama da tsananin tashin-tashinar siyasa a kasar. An kama Mundubile ne a ranar Alhamis, bayan wani samame mai cike da tashin hankali da &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3434,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-3431","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3431","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3431"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3431\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3435,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3431\/revisions\/3435"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3434"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3431"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3431"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3431"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}